@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SHIN, ZA KU KARBETA DA HANNAYE BIYU?
A koda yaushe Allah na tare da bayinsa muminai, kuma a kullum buqatarsa ita ce ya faranta musu rai.
Ko da kaga muminai cikin bala'i da masifa, to, jarrabawa ce kawai don Allah ya tantancesu ya kuma daukaka darajarsu.
To, yanzu anzo gurin, domin 'yan shi'ah sun himmatu kan cewa sai sun dawo da martabar addinin Allah ya kasance shi ke jagorantar rayuwar al'umma.
A gefe guda kuma azzalumai sun tashi haiqan kan lalle sai sun shafe su tare da danne wannan yunquri (gwagwarmaya) da zai kawo qarshensu da zaluncinsu.
Saboda hakane suka fito da dukkan qarfinsu suna karkashe 'yan shi'ah. Allah kuma na rarrashinsu ta hanyar bushara mai sanya nishadi da qarfafa gwiwa cewa;
" ALLAH YAYI ALQAWARI GA ('yan shi'ah) WADANDA SU KAYI IMANI DAGA GARE KU, KUMA SUKA AIKATA AYYUKAN QWARAI (cewa) LALLE ZAI SHUGABANTAR DASU (don yin adalci) A CIKIN QASA KAMAR YADDA YA SHUGABANTAR DA WADANDA SUKE DAGA GABANINSU, KUMA LALLE ZAI TABBATAR MUSU DA ADDININSU (muslimci) WANDA YA YARDAR MUSU (a matsayin jagora), KUMA LALLE NE YANA MUSANYA MUSU (da) AMINCI BAYAN (wannan) TSORO NASU (da suke ciki na cutarwa), SUNA BAUTA MIN (kamar yadda na umarce su), BA SU HADA KOME DANI (wajen yin hukunci). KUMA WANDA YA KAFIRTA A BAYAN (tabbatar musu da) WANNAN (alqawarin da nake yi musu), TO, WADANCAN (da suka kafirta) SUNE FASIQAI ('yan'uwan Buhari) ."
(Suratul-Nurr, aya ta 55)
Yanzu za ku karbi wannan busharar ce ko kuma za ku juyawa kafirci da zalunci baya Allah ya canza ku da wasu?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com