'Dai Daga Cikin Yan Uwa Da aka Kona da Wuta a Waki'ar Zariya |
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BA ZA MU TABA MANTAWA DA RANAR 12-12-2015 BA
Dukkan wani abu daka sani na alkhairi ko sharri akwai matsayin da Allah ya tsayar masa. Bayyanar da sharri bai kamata ga mutum ba in ba wanda aka zalunta ba, amma aikin alkhairi abin so ne a bayyanar dashi ko don nuna godiya ga Allah.
Idan kaji wata magana ta sharri ga wani ko wata bai kamata ace kana yadata (broadcasting) ba, domin in a kanka abin ya faru ba za kaso ace ana yadawa ba. Amma in har zaluntarka aka yi ta hanyar cutarwa ko baqantawa kana da dama ka bayyanar dashi ko don neman 'yancinka ko kuma ka nunawa mutane cewa an zalunceka kamar yadda Allah (S.A.W) ke cewa:
لَّا يُحِبُّ ٱللَّهُ ٱلۡجَهۡرَ بِٱلسُّوٓءِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ إِلَّا مَن ظُلِمَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعًا عَلِيمًا (٨٤١)
" ALLAH BA YA SON BAYYANAR DA MUMMUNA GA MAGANA SAI DAI GA WANDA AKA ZALUNTA. KUMA ALLAH YA KASANCE MAI JI NE MASANI."
(Nisa'i, aya ta 147)
Wannan umarni na Allah (T) yasa muke bayyanar da irin zaluncin da Gwamnatin Buhari tayi mana daga ranar 12-12-2015 zuwa ranar 14-12-2015.
A tarihin duniya ba a taba samun zamanin da aka taba zaluntar dan Adam kamar yadda Buhari ya zalunci 'yan shi'ah mabiya Sayyid Zakzaky (H) ba.
Kashe qananan yara da mata na cikin abinda aka haramta yinsa yayin yaqi ko da kuwa kafirai ne ke yinsa. Shi kuwa Buhari ya keta wannan doka wacce kafirai ma suka sanyata, domin shi bayan kisan ma har da qona gawarwaki yayi, wasu kuma da ransu aka cinna musu wuta suka qone qurmus !
An fede cikin mata masu juna biyu an harbe jaririn da aka fitar, kuma an yiwa mata fyade babu adadi. Sannan kuma an toni rami an binne mutanen da basu gaza 346 ba, wasu ma da ransu aka binne don tsantsar rashin imani irin na Muhammadu Buhari.
Bayan irin wannan qazamin ta'addanci da akayi mana sai kuma aka cigaba da daure mutane dauke da muggan raunuka ba tare da anyi musu jinya ba. Mafi muni kuma mafi tsahon dadewa cikin wannan qangi shine jagora Sayyid Zakzaky (H) tare da mai dakinsa malama Zeenat har tsahon shekara shida ba kadan.
Da shike Allah ne mai ikon kashewa da rayawa sai ya zama ya rayar da Sayyid Zakzaky (H) da matarsa cikin wannan mummunan yanayi don su zama aya ga azzaluman wannan lokaci dama wadanda za suzo nan gaba.
Komai lalacewar al'umma ba a rasa na kirki daga cikinsu, saboda haka aka sami wasu mutane wadanda suka nuna rashin adalcin Buhari kan wannan zalunci nasa wanda ko Fir'auna baiyi irinsa ba, domin shi kashewa kawai yayi ba tare da qonawa ba.
Wannan aiki na wasu mutane qalilan da muka bada misali dasu ya zama dole mu bayyanar da ayyukansu na rashin goyon bayan zalunci da kuma tausayawa wadanda aka zalunta. Wannan aiki nasu alkhairi ne wanda ya kamata mu bayyanar dashi kamar yadda Allah (T) ke cewa:
إِن تُبۡدُواْ خَيۡرًا أَوۡ تُخۡفُوهُ أَوۡ تَعۡفُواْ عَن سُوٓءٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَفُوّٗا قَدِيرًا (٩٤١)
" IDAN KUKA BAYYANAR DA ALKHAIRI (na abinda akayi muku) KO KUKA BOYE (shi cikin zukatanku) KO KUMA KUKA KAU DA KAI DAGA MUMMUNAN (abinda akayi muku), TO, LALLE ALLAH YA KASANCE MAI YAFIYA NE MAI IKO."
(SURATUL-NISA'I, AYA TA 148)
To, wannan goyon bayan da wasu su kayi mana alkhairi ne gare mu, shi yasa mu kaga ya dace mu bayyanar dashi don susan lalle munji dadin abinda su kayi mana.
Ba za mu taba yafewa wadannan azzaluman da suka zalunce mu ba matuqar ba su da kansu ne suka nemi yafiyarmu ba, abinda za muyi tayi shine addu'ar Allah ya daukar mana fansar abinda au kayi mana anan duniya ne ko kuma bayan mun koma gare Shi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
20th December, 2021/ 15th Jimada-Ulah, 1443.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com