Babu Wanda Ya Dace da Mata Irin Mijin Yar Shi'a..!!

Wani Bangare na Taron Karawa juna sani na Wakilan Ma'asumah karo na Biyu a kano



Babu matar da take tsantsar kishin mijinta da kuma cika umarnin Ubangiji na sanya kammalellen hijabi kamar matar Dan shi'a. Matar Dan Shi'a ba ta nuna adonta ko kwalliyarta ga namijin da ba mijinta ba. 


Kai kuwa na sani duk ranar da matarka tai kwalliya, ta fesa turare, ka sani badan kai tai ba, watakila zata je unguwane, ko ta haka taja hankalin mazajen kan titi.


Haka al'amarin yake ga mazajen 'yan Shi'a. Idan kana neman kiyaye doka da hana cakuduwar maza da mata leka wajen taron 'yan Shi'a kasha mamaki.


Dan shi'a da zuciya daya yake sayawa matarsa kayan ado, kwalliya da sabbin tufafi, don yasan babu wani mahaluki  kuma hamago da ya isa yaga kwalliyarta.


Kai da ka mayar da matar taka abar tallatawa a titi ta hanyar barinta sasakai a gaban makadi, yayin rawar dije.  Kai ne me bakin sharri, aibatawa da kuma sukar wadanda ko makiyansu sunyi masu shaidar kamun kai.


'Yan shi'a ba a duniyar wata suke rayuwa ba. Suna rayuwa ne tare da jama'a, kuma na tabbata in wadansu basu yi masu adalci ba wasu zasu yi masu.


Bahaushe ma yace "in mafadin magana wawa ne, ai majiyinta ba wawa bane."


Yaran da ake haifa a wannan zamanin sunansu 'ya'yan 'Digital Era', sai sun tantance abu kafin su karbe shi, kuma hanyoyin bincike ya saukaka matuka a garesu. Domin kuwa cikin sakan daya tal zasu iya haduwa da duk wanda suke so su hadu dashi a kowanne lungu na duniya yake, domin gudanar da binkicensu da tantance tantancensu.


Ma'as salam🙏🙏🙏

Na barku lafiya.

Asha shagulgulan Maulidi lafiya.


Tijjanin Dawaki

INTERNET FORUM OF THE ISLAMIC MOVEMENT

19/03/1444 (14/10/2022)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post