Yau shekaru goma kenan ana cigaba da tsare wannan bawan Allah mukulisi cikin ma'amala da kowa, mutanen gari sun yi mar wannan sheda, bayan kamu da gwamnatin Nijeriya tayi masa abisa wani dalili na zargi irin Wadda ƴan magana suke ce masa (tuhumar fin ƙarfi) wadda asali babu ita ake samar da ita domin asamu damar mallakar mutum ayi amfani da shi ta wata hanyar domin cinma buri tare da wata manufa wadda alhaƙin tuhumar take koma gareshi
Malam Haruna Abas shi mutumin Zariya ne sannan kuma mazaunin garin, lokacin da Jami'an tsaro na farin kaya DSS suka kamashi suka miƙashi kotu shine kwamanda na masu tsaron Malam Zakzaky wadda akafi sani da (Harisawa)
Tuhumar da ake masa shine wai ana zarginsa da ta'addanci ta hanyar koyawa matasa harbi da dabarun yaƙi wadda wai yasamu damar ƙarɓo kwangilar tasa ne daga ƙasar Lebanon, wai dalilin haka yabashi damar shigowa da makamai Nijeriya makaman da haryau ba a taɓa nuna ko da guda daga cikin su ba tsawan shekaru goma zuwa yau.
Daga cikin manyan zalunci da akayiwa wannan Mazalumin Malam Haruna Abas tare da wasu ƴan uwansa da aka kamasu da shi, bayan kama su da aka yi da kusan shekaru biyu; ba'a san inda suke ba, sai daga baya ya bayyana a hannun jami'an DSS ta hanyar kaisu kurkukun kuje dake Birnin Abuja domin gurfanar da su a wata kotu da aka fara wata Shari'a da su wacce bata da tushe bare makama
Daga fara shari'ar zuwa yau an shafe sama da shekaru bakwai ana yi, amma an gagara kawo karshen shari'ar, kullum in anzo sai dai ace an ɗaga zuwa wani lokaci na gaba, kuma sannan an ƙi bada belinsu. A halin da ake ciki kuma Malam Haruna bai da lafiya saboda tsarewar da ake cigaba da yi musu, hakan har ya sabbaba masa ciwon ido mai tsanani tun shekarar da ta gabata ba tare da wata kulawar kirkiba
Sannan tun a wancan lokacin Shekarar 2012 da aka kamasu kafin a bayyana yadda suke tsare dashi, ashe sun ɓoyeshi cikin azaba a gidan Tsaro na DSS (Yellow House) dake Aso Drive daura da Aso Villa “Under Ground Cell” wato cikin kurkuku mai gidan ƙasa da Sarka a Wuya da Hannu har Tsawon Shekaru uku a wannan yanayin ana gana masa nau'o'in azama iri-iri
Duka manufar wannan shine anaso Malam Haruna Abas ya amsa cewa Malam Zakzaky ne mai gidanshi acikin wannan aikin da ake tuhumar sa dashi na ta'addacci, tsawon lokacin shekarun da aka ɗauka ana tsare dashi Malam Haruna Abas yace; lalle sai dai a kasheshi in dai sai ya amsa wannan laifin da bai ma san shi ba balle ace ma ya aikata shi.
©Abdullahi M Ali
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com