Allah Daya ne Amma Yana Da Bayi Wakilai Masu Isar Da Sakonsa ..!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MATSALAR WAKILI KAWAI YA ZAMA AYYUKANSA NA CIN KARO DANA JAGORA


Allah shine mahalicci Tilo wanda ba shi da abokin tarayya cikin komai nasa,  kuma yana da ikon kamai nasa ya kasance kamar yadda yake so ko da kuwa bai sanya wata halitta a matsayin mai taimakawa wajen isar da saqon nasa kamar yadda yake so ba. 


" وَإِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ ." (٣٦١)


" KUMA ABIN BAUTARKU ABIN BAUTA NE TILO, BABU ABIN BAUTAWA FACE SHI MAI RAHMA MAI JIN QAI."


            (Baqara:163)


Amma duk da wannan iko nasa bai hukunta cewa shi da kansa ne zai isar da saqonsa ga bayi ba tare da sanya wani wakili/Halifa a doron qasa ba.


Saboda haka yayi nufi kuma ya sanya halifansa a doron qasa kamar yadda yake cewa:


" وَإِذۡ قَالَ رَبُّكَ لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ إِنِّي جَاعِلٞ فِي ٱلۡأَرۡضِ خَلِيفَةٗۖ.........."


" (ka tuna yaa Muhammad) " YAYIN DA UBANGIJINKA KE CEWA MALA'IKU : " LALLE NI MAI SANYA HALIFA NE A CIKIN QASA ."


         (Baqara:30) 


Wannan Halifa nasa na farko shine Annabi Adam (A.S), sai kuma ya cigaba da sanya Manzanni daga cikin tsatson wannan Halifa na farko don su zama masu isar da saqonsa zuwa ga sauran bayinsa.


Wadannan Halifofi nasa sun isar da saqon nasa kamar yadda aka turo su da shi ba tare da canzawa da bin son zuciyarsu ba. Da ace zuwansu sun canza da cewa azo a bi su a matsayin ababen bauta koma bayan Allah, to, da ya zama sun ci amanar kansu da kansu kuma sun tashi daga asalin wakilcin da Allah ya dora su a kansa.


Annabi Muhammad (S.A.W.W) shine Annabin qarshe wanda babu wani a bayansa wanda zai tsaya a matsayin Manzo, sai dai ya tsaya a matsayin Halifansa wanda zai cigaba da isar da saqon da yazo musu dashi daga Ubangijinsu. Yayi iya qoqarinsa ya sauke dukkan haqqin dake kansa na isar da saqo, amma bai zama dukkan saqon ya isa ga al'ummarsa (direct) ta hanyarsa ba, dole sai da ya zama ta hanyar wakilai ne wadanda suka riqa daukar wannan saqo zuwa ga wadanda bai isa gare su ba.


Kafin barinsa duniya sai da halifantar mana da wadanda za su isar da wannan saqon da yazo dashi zuwa gare mu, kuma ta hanyarsu ce muka san haqiqanin koyarwar da yazo da ita.


A daidai lokacin da ya zama babu wadannan Halifofi/wakilai nasa sai ya zama Allah ya tayar da wasu amintattu nasa wadanda suka riqi addinin kuma su kayi Tajdidinsa don ya zama ya rayu cikin zukatan al'ummar Manzonsa kuma ya dabbaqu a aikace kan gabobinsu.


Sayyid Zakzaky (H) shine Jagora Tilo wanda ya zama madubi abin kallo kuma abin koyi tare da fifita shi kan kowa cikin wannan zamani.


Tattare da wannan matsayi nasa bai zama ta hanyarsa ce kadai mabiyansa suka ji kuma suka fahinci kiran da yake yi ba, dole sai ta hanyar wasu wakilai da suka ji daga gare shi kuma suka cigaba da bayyanar da wannan kiran nasa ko da kuwa ba shi ya ayyanasu ba.


Saboda haka a duk lokacin da wani wakili ya bude baki yana magana da yawun wannan harka, to, abu na farko da ya kamata kayi shine ka auna maganar tasa da ayyukansa kaga yana tafiya daidai dana Jagora ne ko kuma yana cin karo da nasa.


Idan ya zama babu karo cikin ayyukan nasa kuma babu karo cikin zantukansu, to, babu wani hurumi na ilimi wanda za ka qalubalenci wannan wakili.


Amma idan ya zama ayyuka da furucinsa na cin karo dana Jagora, to, abinda ya zama wajibi a kanka shine kayi watsi da wannan wakili ko shi wanene ka riqi zantuka da ayyukan dake zuwa daga Jagora.


Wannan dalili yasa mu kayi watsi da ayyuka/zantukan wadanda suka ci amanar Manzon Allah (S.A.W.W) ta hanyar canza karantarwarsa da ayyukansa (S.A.W.W). Sai ya zama wadanda basu canza ayyukansa da zantukansa ba suka zama sune wakilai na gaskiya 'yan amanar da suka isar da saqo kamar yadda aka isar musu.


MATSALAR WAKILI KAWAI YA ZAMA AYYUKANSA NA CIN KARO DANA JAGORA


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da ✍🏽 Ado Isah Guda.


       (08137925034)


5th May, 2022/  5th Shawwal, 1443.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post