“Na ga kamar wasu mutane sun dauka addini kasuwanci ne, har ma suke ganin cewa kowa ma in yace a yi addini shima kasuwancin yake yi.
“Amma na san wani abu guda, wanda duk ya dube mu yace muna yin (gwagwarmaya) ne saboda kudi ko saboda ana biyanmu, sai nace masa lallai ya fi sauki kace mana mahaukata akan kace mana ana biyanmu ne. In kace mu mahaukata ne (a wajenka) ya yi daidai. Domin babu yadda za a yi ace wasu mutane ana basu kudi ne, amma suke fuskantar bindiga da rayuwarsu. To meye amfanin kudin?
“Kuma in kai baka ji a jikinka ba, ka samu wanda aka kashe ubansa ko wanda aka kashe dansa, ka tambaye shi nawa za a bashi ya yarda a kashe masa da ko uba?
“Shi ya ji a jikinsa ai. In kace masa mahaukaci ya yi daidai, mahaukaci ka san bai san abin da yake yi ba. Amma kace mutum ana bashi kudi ne, kuma ya fuskanci bindiga, wanda zahiran ba wai an baku labari bane, kun ga yadda ake bude wuta, mutanenmu na nufan inda wutan yake, za a harbi wasu, wani ya je ya kare da kirjinsa ya kare wani shi a harbe shi, kyamarori sun daddauka.
“Wanda duk yace wannan kudi ake basu suke yin wannan. Si mu ce kai nawa za a baka ka fuskanci bindiga? Wannan in dai baka gane cewa imani ne da sadaukarwa ba, sai mu ce ka yi mana shiru kawai. Domin al’amarin addini imani ne da sadaukarwa saboda Allah.”
— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a ganawarsa da yan uwa ranar Laraba 16 ga Rabi'ul Auwal 1444 (12/10/2022) a gidansa da ke Abuja.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com