Abunda Nafi Rikewa Kuma Yayi Matukar Tasiri Acikin Rayuwata, Haduwa ta da Sheikh Ya'aKub Yahya Katsina, _Ammar Ubale Mai Rauni

Ammar Ubale tare da Sheikh Ya'aKub Yahaya katsin

A Satin nan ne Dai Daga Cikin Fitattun Mawakan Manzon da Iyalan gidan sa Tsarkaka,  Ammar Ubale Wanda Aka fi Sani Da ( Mai Rauni ), Ya Saki Wani Rubutu A Shafin Sa Na Facebook inda yake bayyana Wani abu da Ya Shafi Rayuwar sa Bayan Ganawar sa da Sheikh Ya'aKub Yahayya katsina a Shekarun baya.


Gadai Rubutun a yadda ya  Wallafa shi.


"Abinda nafi riƙewa kuma yayi matuƙar tasiri cikin Rayuwata bayan fara waƙar yabo wanda muke wa Manzon Allah (S) da Iyalan gidansa shine ranar da Malam Yakubu Yahya Katsina yamin nasiha lokacin damuka gaisa dashi zuwa na farko garin Katsina.


Bana mantawa lokacin daga Abuja Struggle nake bazato ba tsammani damuka tsaya Kano bayan anyi Birthday na Shahid Sheikh Turi (R) muka wuce nidasu Adam Lawal Katsina  shima ranar ne ranar farkon haɗuwata dashi.

Mun shiga mun taras Sheikh ya ida Sallah yana kan Dardumarsa muka fara gaisuwa, bayan mungaisa ya tambayeni niɗan wani gari ne? Nace Potiskum ta jihar Yobe, yace garinsu Sidi Mustapha kenan? Nace Na'am. Nacemai daga Abuja nake bantaɓa zuwa garinnan ba sai bana sai kuma Abokaina suka ce yakamata mugaisa tunda nazo nace shine mukazo mu gaisa kuma amana nasiha matsayinmu na matasa, kafin Malam yafara magana sai Zahraddeen Sirajo Abbas  yace ai shine yayi waƙar (Mata Nasrullah), Sheikh yace tabbas wani sa'i yakanji idan gidan Tv na AlwilayahTv Hausa  sun saka.


Sheikh yacemin sannunku da ƙoƙari, ayita Gwagwarmaya kar afasa kuma muna fatan Allah Ta'ala ya tabbatar damu daku gabaɗaya duk rintsi duk wuya, mukace Ilahy. Yayi mana nasiha sosai da sosai amma ni wacce tafimin tasiri shine;

Bayan ya gama sai nake cemai Akarmakallah dayake muna ɗan taɓa waƙe jifa jifa haka ko akwai wata Addu'a da za'a bamu domin idan munyi saƙo ya riƙa zuwa cikin al'umma?


Sai Sheikh Yacemin;

Babban abinda zaisa haka a matakin farko shine kayi dan Allah ba dan wani ba ko wani ya yabeka ba. Yace wannan shine sirrin yaɗuwar saƙo kowane iri ne acikin bayin Allah. Kar kayi dan ace tayi daɗi, dama kai saƙo ka isar walau yayiwa masu sauraro daɗi ko kuma akasin haka, nace tabbas hakane.

Sai naƙara tambayar Sheikh ko akwai wata Addu'a Harwayau wacce za'aban kafin nafara rubuta waƙa  domin samun Ilhamomi da Basira?

Sai yacemin kadaina saɓon Allah, saboda Allah Ta'ala baya bawa wanda yake saɓa masa basira ko ilhama, dan ka guji abinda saɓama Allah ne shikuma zai kimsa maka Ilhamomi da basirori. Nayi godiya sosai yamin Addu'ar Allah Ta'ala yatsare hanya muka fita.


Wannan nasihar tanamin tasiri sosan gaske, saboda Wallahil Azeem ko waƙa zan rubuta awannan satin da zanyi to nakanyi iyakar ƙoƙarina wurin ganin cewa ban saɓawa Allah Ta'ala da sanina ba tunda dama ni Mairauni ne ba Ma'asumi ba, kuma Alhamdulillah Allah Ta'ala yana bamu Ilhamar da Basirar daidai gwargwado.

Alhamdulillah.❤️

Allah Ta'ala Yayimuku Hidima Kamar Yadda Kukewa Addininsa Hidima Ba Dare Ba Rana Ya Sheikh.🌹🙏



DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post