Abubuwan da za su Tabbatarwa Al'ummar Musulmi an kashe Yayan Annabi Abisa Zalinci.. !!




Abu na farko


 

   (1) Zubar da jinin 'yayan Annabi (sawa), a watan da ba'a yaki acikinsa wato Al-Muharam, ko lokacin jahiliya suna girmama wannan watan basa yaki a cikinsa. Amman a watan aka karkashe yayan Annabi (sawa). 


  (2) Kashe yara da shari'a bata haukan suba, da kashe jariri. Wannan babu shi a musulinci haramune kashe mata da yara ko a filin yaki. 


 (3) Hana yayan Annabi (sawa) ruwan sha, har da  kananun yara wannnan kwakwata babu shi a misulinci. 


 (4) Daddtsa jikkunan su da yanke kawukan su a addinin musulmci ba inda Allah ya halasta haka, ko da dagawar kafirice.


 (5) Tilatsawa mutum dole sai yayi bai'a ga wani sarki, ko wani shugaba a musulmci. Babu wannan a musulinci. 


   (6) Cirewa mata suturarsu kamar hijabai dasauran da musguna musu, da dukansu, a misilinci babu wannan ko lokacin jahiliya abin kunyane mutum ya tsaya yana fada da mata.


   (7) Biyayya ga shugabannin da suke umarni da haramci, da halasta haramci, da take duk wata dokar Allah haramunne abi su, akuma yi musu da'a babu biyayya ga wanin Allah abisa sabon Allah wannan na daga cikin abin da Hussaini Dan Ali(as) ya ki mikawa a gwamnati wannan lokaci  domin kin yarda da zalinci. Gwamnati wannan lokacin ta takurama sa, sai ya yi caffa a wannan lokacin.

   

(8) Kukan da annabi (sawa) yayi kafin kisan, da za'ayiwa dan sa kuma jikansa sayyidana Hussaini (as), ya na nuna cewar babban kaba'ir ne kashe dan sa, kuma dansa, na kan gaskiya, da ba'a kan gaskiya ya keba da annabi shi zaiyi magana akai. 


(9) Tura rindunar sojoji su kawo Hussaini (as) a raye ko akashe idan har bai mika wuya ba, wanda wannan bashi a musulmci, ka tilastawa mutum sai yabika. 


 (10) Izgilanci, bayan kashe Hussaini (as) da yansa, da yayan yan uwansa al-Hussan (as). A lokacin an kai kawukansu a gaban sarkin wannan lokaci wato yazid dan ma'awuya yayi shewa tare da izgilanci ga yayan annabi a gaban wadanda sukayi saura, ya ce banu hamsin sun dauka mulki wasane yayi musu isgilanci iri daban daban. Wannan babu shi a musulinci. 


  (11)Kora mata su tafi akafa ana zaginsu da aibatasu da jifansu, da akayiwa mata da sauran yayan da suka ragu daga mata da maza yayan annabi wannan ma bashi a musulmci, annabi bai taba yiwa kafirai hakaba ballanta musulmi


12. *CUTARWA GA YAYAN ANNABI WANNAN BABBAN LAIFINE ZAGINSU MA BALLANTANA KASHE SU.*


Idan muka duba iya Wadannan abubun kadai ya nuna cewar gwamnati wannan lokacin karkashin yazidu dan mu'awuya, ba addinin musulmci suke yi ba wani abu suke daban kamar yadda Hussaini (as) ya shaidawa duniya dalilin sa nakin yin bai'ai ga sarakunan wannan lokacin. Wannan kadai ya nuna maka cewar an zalinci yayan annabi. 


*Ko kasan Hussaini yana daga cikin Ahali baiti?*


*Ko kasan Hussaini yana daga cikin wadanda annabi ya ce akula da su zai tambaye al'ummarsa ga me da yadda sukayi da yayan sa ranar gobe alkiyama?*


*Ko kasan Hussaini da dan uwansa Al-Hassan sune samarin gidan Aljanna?*


*Ko kasan Hussaini ya na daga cikin wanda Allah yayi umar ni a lokacin mubahala azo da shi tsakanin christocin najaran da annabin Allah?* 


*Ko kasan Hussaini (as) yana daga cikin ayar da allah ya tsarkake ahalul baiti?*


*Ko kasan Hussaini Annabi  bayaso asasu kuka shi da dan uwansa al-Hassan, To ina ga wanda ya kashesu?* 


*Ko kasan Hussaini yana daga cikin sahabban annabi?*


*Ko kasan Hussaini ya na daga cikin wadanda annabi yayi wasiya dashi?  Da sauran falaloinsa da babu lokacin da ba zaibani damar rubutawa ba.* 

 

   _Hakika duniya a wajan Allah fiffikan sauro yafita daraja, shiyasa ma ya kan bari akashe masa annabawa, sabo da duniya ba komai bace a wajan Allah.

 Allah baya gaggawa yabar sarakunan wannan lokaci sukayi abin da sukayi, akan yayan annabi, tare da duk irin soyayyar da annabi yake nunamusu tun daransa, amman aka karkashesu bayan sa. 


Dan uwana yi kokarin tausayawa yayan annabi irin abin da akayi musu domin annabi ma yayi kuka abisa haka, ta iya kasantuwa sallahar ka, azimin ka, hajjinka, umarar ka, sadarka, yazamo ba karbabbe ba a wajan Allah basu cikaba, amman sakamakon tausaya ga irin abun da akayiwa yayan annabi ko da, da dakika biyune kacal allah darajar wannan tausayawa da ka yi ga yayan annabi Allah, Allah ya karbi aiyuka kanka ya gafartama. Domin akan kare ya gaftawa wata karuwa sakamakon ta tausaya masa, ta shayar da shi ruwa ina kuma ace ga yayan annabi ka tausayamu su? 


Akarshe muna adduar allah ya tausaya mana yajikan mu darajar yayyan annabinsa, halin da muke ciki a wannan kasa allah darajarsu ya kawomana mafita. 


wassalamu.... 


©Habib Nasrallah 

Email habiburabiu81@gmail.com


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post