A Wadanne Kabbarori Annabi (S) Ke 'Daga Hannayensa Cikin Sallah ???




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


SAHABBAI SUN TAKA RAWA WAJEN CANZA SIFFAR SALLAR MANZON ALLAH (S. A. W. W) 


Maluma ba za su taba kubuta daga cikin wadannan zarge-zarge na canza haqiqanin siffar sallar Manzon Allah (S. A. W. W) ba domin ganin gaskiyar da suke yi kuma su rufe idanuwansu wajen yin riqo da ita, sai dai mafiya girman wannan laifi sune wasu daga cikin Sahabban Manzon Allah (S. A. W. W) da suka cancanza abubuwa don bin son zuciyarsu da kuma wata boyayyiyar manufa da su suka fi kowa saninta. 


Tabbas, idan ka kalli yadda al'ummar musulmi ke yin sallarsu sai abin ya daure maka kai sakamakon yadda kowa ke siffanta irin tasa sallar, alhali kuma duk suna cewa da Annabi (S. A. W. W) suke yin koyi. 


Amma bisa gaskiyar magana ba za a sami sallah ta zama an cancanza siffofinta sannan ace wai duk haka Annabi (S. A. W. W) yake yi ba, a'a, dole ya zama akwai haqiqanin siffar yadda ya koyar, sai dai kawai ace mafi yawan mutane na bin son zuciyarsu ce wacce Shaidan ke yi musu jagoranci cikin ayyukansu. 


Za mu kawo wasu riwayoyi ne masu siffanta mana yadda Annabi (S.A.W.W) ke yin sallarsa, sai dai kuma suna cin karo da juna. Anan ne za mu iya fahintar wacce magana ce ta gaskiya a cikinsu. 


     GA SU KAMAR HAKA 


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


(1)


«1127» حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ أَبِي بَكْرٍ الْوَاسِطِيُّ حَدَّثَنَا عُبَيْدُ اللَّهِ بْنُ سَعْدٍ حَدَّثَنِي عَمِّي حَدَّثَنَا ابْنُ أَخِي الزُّهْرِيِّ عَنْ عَمِّهِ أَخْبَرَنِي سَالِمٌ أَنَّ عَبْدَ اللَّهِ قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا قَامَ إِلَى الصَّلاَةِ رَفَعَ يَدَيْهِ حَتَّى إِذَا كَانَتَا حَذْوَ مَنْكِبَيْهِ كَبَّرَ ثُمَّ إِذَا أَرَادَ أَنْ يَرْكَعَ رَفَعَهُمَا حَتَّى يَكُونَا حَذْوَ مَنْكِبَيْهِ وَكَبَّرَ وَهُمَا كَذَلِكَ ثُمَّ رَكَعَ ثُمَّ إِذَا أَرَادَ أَنْ يَرْفَعَ صُلْبَهُ رَفَعَهُمَا حَتَّى تَكُونَا حَذْوَ مَنْكِبَيْهِ ثُمَّ قَالَ سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ ثُمَّ يَسْجُدُ فَلاَ يَرْفَعُ يَدَيْهِ فِي شَيْءٍ مِنَ السُّجُودِ وَيَرْفَعُهُمَا فِي كُلِّ رَكْعَةٍ وَتَكْبِيرَةٍ يُكَبِّرُهَا قَبْلَ الرُّكُوعِ حَتَّى تَنْقَضِيَ صَلاَتُهُ.


Ahmad Bn Muhammad Bn Abiy Bakri Al-Wasiiyyu ya bamu labari, Ubaidullahi Bn Sa'ad ya bamu labari, Baffana ya bani labari, 'Dan 'Dan'uwana Al-Zuhriy ya bamu labari daga Baffansa, Saalim ya bani labari cewa Abdullahi ya ce :


" Manzon Allah (S. A. W. W) ya kasance idan ya miqe zuwa ga sallah yana daga hannayensa har sai sun kai daidai kafadunsa sai yayi Kabbara. Sa'an nan idan yayi nufin yin ruku'u yana daga su har sai sun kai daidai kafadunsa sai yayi Kabbara suna nan a haka, sa'an nan yayi ruku'u.  Sa'an nan idan yayi nufin dago kunkuminsa yada dago su (hannayen nasa) har su kasance daidai kafadunsa sa'an nan yace : " SAMI'ALLAHU LIMAN HAMIDAHU " Sa'an nan yayi Sujadah.  Ba ya daga hannayensa cikin wani abu daga Sujadah, amma yana daga su cikin kowacce raka'a da Kabbara wadanda yake yi musu Kabbara kafin ruku'u, har sai ya qare sallarsa. "


            ABIN LURA 


Abinda wannan Hadisi ke karantar damu shine, cikin kowacce raka'a Annabi (S. A. W. W) na daga hannayensa sau biyu ne yayin Kabbarori, sai dai cikin raka'ar farko wacce ake yi mata Kabbarar Hakama. 


(2)


«1129» حَدَّثَنَا أَبُو مُحَمَّدِ بْنُ صَاعِدٍ حَدَّثَنَا بُنْدَارٌ فِيمَا سَأَلْنَاهُ عَنْهُ حَدَّثَنَا عَبْدُ الْوَهَّابِ الثَّقَفِيُّ حَدَّثَنَا حُمَيْدٌ عَنْ أَنَسٍ قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَرْفَعُ يَدَيْهِ إِذَا دَخَلَ فِي الصَّلاَةِ وَإِذَا رَكَعَ وَإِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ مِنَ الرُّكُوعِ وَإِذَا سَجَدَ. لَمْ يَرْوِهِ عَنْ حُمَيْدٍ مَرْفُوعًا غَيْرُ عَبْدِ الْوَهَّابِ وَالصَّوَابُ مِنْ فِعْلِ أَنَسٍ.


Abu Muhammad Bn Saa'idi ya bamu labari, Bundaru ya bamu labari cikin abinda mu kayi masa tambaya game dashi, Abdul-Wahaab As-Saqafiyyu ya bamu labari, Humaid ya bamu labari daga Anas yace :


" Manzon Allah (S. A. W. W) ya kasance yana daga hannayensa yayin da ya shiga sallah (Kabbarar Hakama) da kuma yayin da yayi ruku'u  da kuma lokacin da ya dago kansa daga ruku'u, da kuma in zai yi Sujadah. "


(Mai riwayar yace Abdul-Wahaab As-Saqafiyyu) ba daga wajen Humaid ya riwaito wannan Hadisi ba, Hadisin Marfu'i ne, kuma abinda yake daidai shine daga aikin Anas. 


               ABIN LURA


Wannan riwaya ta biyu (2) kuma tana nuna mana ne cewa Annabi (S. A. W. W) na daga hannayensa cikin kowacce Kabbara da ake yinta kafin ruku'u da wadanda ake yinsu yayin Sujadah. Wato duk Kabbarorin dake cikin sallah ana daga hannaye yayin yinsu.  Sai dai kuma maruwaicin hadisin (reporter) yana qaryata wanda ya bada labarin (narrator). 


(3)


«1131» حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ الْوَكِيلُ حَدَّثَنَا الْحَسَنُ بْنُ عَرَفَةَ حَدَّثَنَا هُشَيْمٌ عَنْ حُصَيْنٍ. وَحَدَّثَنَا الْقَاضِي الْحُسَيْنُ بْنُ إِسْمَاعِيلَ وَعُثْمَانُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ جَعْفَرٍ قَالاَ: حَدَّثَنَا يُوسُفُ بْنُ مُوسَى حَدَّثَنَا جَرِيرٌ عَنْ حُصَيْنِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ قَالَ: دَخَلْنَا عَلَى إِبْرَاهِيمَ فَحَدَّثَهُ عَمْرُو بْنُ مُرَّةَ قَالَ صَلَّيْنَا فِي مَسْجِدِ الْحَضْرَمِيِّينَ فَحَدَّثَنِي عَلْقَمَةُ بْنُ وَائِلٍ عَنْ أَبِيهِ أَنَّهُ رَأَى رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَرْفَعُ يَدَيْهِ حِينَ يَفْتَتِحُ الصَّلاَةَ وَإِذَا رَكَعَ وَإِذَا سَجَدَ. فَقَالَ إِبْرَاهِيمُ مَا أُرَى أَبَاكَ رَأَى رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلاَّ ذَلِكَ الْيَوْمَ الْوَاحِدَ فَحَفِظَ ذَلِكَ وَعَبْدُ اللَّهِ لَمْ يَحْفَظْ ذَلِكَ مِنْهُ ثُمَّ قَالَ إِبْرَاهِيمُ: إِنَّمَا رَفْعُ الْيَدَيْنِ عِنْدَ افْتِتَاحِ الصَّلاَةِ. لَفْظُ جَرِيرٍ.


Ahmad Bn Abdullahi Al-Wakeelu ya bamu labari, Hassan Bn Arafata ya bamu labari, Hushaimu ya bamu labari daga Hussaini. Kuma Alqali Hussaini Bn Isma'il da Usmanu Bn Muhammad Bn Ja'afar sun bamu labari suka ce :


" Yusuf Bn Musa ya bamu labari, Jarir ya bamu labari daga Hussaini Bn Abdurrahman yace :


" Mun shiga wajen Ibrahim sai Amruu Bn Murrata ya ba shi labari yace : Munyi sallah a cikin Masallacin Haramai guda biyu (Makkah da Madinah) sai Alqamata Bn Was'ili ya bani labari daga babansa cewa shi (baban nasa) ya ga Manzon Allah (S. A. W. W) yana daga hannayensa yayin da yake bude sallah, da yayin da yake ruku'u da kuma yayin da yake Sujadah." Sai Ibrahim (wanda ake bawa labarin) yace :


" NI BA NA GANIN BABANKA YA GA MANZON ALLAH (S. A. W. W) (yayi irin wannan sallah) FACE WANNAN RANA GUDA 'DAYA, KUMA YA KIYAYE HAKAN. SHI KUWA ABDULLAHI BAI KIYAYE HAKA DAGA GARE SHI BA. "


Sa'an nan Ibrahim yace : " Abin sani dai daga hannaye yayin bude sallah lafazin Jareer ne. "


              ABIN LURA


Abinda kuma za mu lura dashi cikin wannan  riwaya ta uku shine, Amruu Bn Murrata ya tabbatar da cewa lalle Alqamata Bn Was'ili ya ba shi tabbacin cewa lalle shi ya ga Manzon Allah (S. A. W. W) yana daga hannayensa yayin Kabbarori dake cikin sallah, wadanda ake yi kafin ruku'u da wadanda ake yi yayin Sujadah. 


Shi kuma Ibrahim bai qaryata Alqamata Bn Was'ili game da wannan labari da ya bayar ba, sai dai yace shi abinda yake gani shine, shi Waa'ili baban Alqamata sau daya (1) yaga Annabi (S. A. W. W) ya yi irin wannan sallah, kuma ya kiyayeta a haka har yake bada labari. Sai kuma ya qara da cewa shi kuwa Abdullahi bai kiyaye hakan daga gare shi (S. A. W. W) ba. 


(Sunan Darul-Qudniy, KITABUS-SALAH, Babin sabani cikin daga hannaye cikin sallah, hadisai masu lamba 1127, 1129, da kuma mai lamba 1131)


                    NAZARI 


Cikin riwayar farko kwata-kwata abinda take nunawa shine ba a daga hannaye yayin Kabbarorin da ake yinsu yayin Sujadah, wadanda ake yi kafin Sujadah ne kadai ake daga musu hannaye. 


Shi kuwa Hadisi na biyun yana tabbatarwa da cewa ne lalle daga hannaye ana yinsu ne yayin kowacce Kabbara dake cikin sallah. Ko da shike maruwaicin hadisin yayi qoqarin qaryata wani daga cikin Rijaal na hadisin mai suna Abdul-Wahaab As-Saqafiyyu, amma kuma ya gaskata maganar Anas ta cewa Annabi (S. A. W. W) yana daga hannaye cikin dukkan Kabbarorin. 


Sannan kuma riwaya ta uku itama tana goyon bayan riwaya ta biyu ce wacce Alqamata Bn Was'ili ya kawo abinda babansa ya gani daga Manzon Allah (S. A. W. W). 


Saboda haka bisa dogaro da wadannan riwayoyi biyu za mu iya fada da babbar murya cewa tabbas, Annabi (S. A. W. W) yana daga hannayensa yayin kowacce Kabbara dake cikin sallah. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


      (08137925034)


11th July, 2020/  12th Zul-Hijjah, 1443.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post