A Matsayinka na Almajirin Mlm Zakzaky (h) ka Dauki Dabi'arsa Daya Ka Dabbaka ka sha Mamaki...!!!



... Umar Hassan Gololo...

Hatta azzalumai da karnukansu na daga miyagun Malaman Nigeria da Tantirai 'Yan-iskan gari sai dai su zagi Malam Zakzaky(H) su kuma yi masa sharri amma dai babu Wanda zai jingina masa munanan dabi'u.

Gaskiya da fadar gaskiya ga kowa da kuma tsayuwa akan gaskiya ko me zai faru.

Jarumta da tausayi,kyautata zato ga kowa,fatan alheri da neman tsira ga kowa makiyi da masoyi.

Tausayi da kyautatawa kowa masoyi da makiyi,adalci da kyauta da uwa uba umurni da kyakkyawa da hani ga aikata mummuna da kuma Kira zuwa ga tabbatar addini.

Hakuri da juriya daga zaluncin azzalumai da wautar wawayen gari da mabiya.

Da kyawawan dabi'u Malam Zakzaky(H) ya cimma nasarori masu yawan gaske ba da munanan dabi'u ba.

Saboda bada tarbiyya da Ilmantarwa Malam Zakzaky(H) ya assasa ta'alim da sauran programs na gyaran tarbiyya da gina Shaksiyyar 'Yan-uwa a wannan Harkar tun tale-tale.

Rashin ganin girman Jama'a,zagin mutane,karya,yaudara,rashin cika alkawari,yawo da gulma da tsegunguma,cin amana da cin haram ba dabi'un mutanen kirki bane,shi kuwa Malam Zakzaky(H) so yake mu zama mutanen kirki.

Allahu Ta'ala ya bamu sabati da istikama Alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam..

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post