Tabbas Akwai Zargi Cikin Ruwayoyin Anas Bn Malik..!!!

 DA BASMALA ANNABI (S. A. W. W)  KE FARA BUDE SALLAH KO KUMA DA KARATUN FATIYA  ???



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


TABBAS AKWAI ZARGI CIKIN RIWAYOYIN ANAS BN MALIK 


Na taba cin karo da rubutun wani inda yake cewa duk wata riwaya da tazo daga Anas Bn Malik ba za a karbeta ba, har nake ce masa in har tazo daidai da Ingantattun riwayoyi mai zai hana a karbe ta  ?


Da gaskene malaman Hadisai sun  kawo cikin rubutunsu wadanda suke nuna hanyoyin da ake bi wajen tace Hadisai da kuma irin mutanen da ba a karbar riwaya daga gare su cewa akwai maqaryaci, mai raunin hadda, mayaudari, wanda riwayarsa ta saba da ingantattun riwayoyi da  dai makamantansu, to, cikin wadannan za a iya sanya Anas Bn Malik ciki,  domin kuwa ana samun riwayoyinsa masu cin karo da juna ko kuma masu qaryawa ingantattun riwayoyi. 


Sai dai kuma wani abin mamaki shine, cikin manyan littafan Hadisai wadanda ake kiransu da suna INGANTATTUN HADISAI akwai riwayoyinsa cif cikinsu. 


Cikin wannan rubutu namu na yau insha Allahu za mu kawo wasu riwayoyi ne da suka zo daga gare shi masu cin karo da juna dangane da batun bayyana karatun Basmala cikin sallah da kuma dame Annabi (S. A. W. W) ke fara karantawa yayin bude sallarsa. 


Ga sunan kamar haka insha Allahu. 


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽



(1)


«1216» حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مُبَشِّرٍ حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ سِنَانٍ حَدَّثَنَا زَيْدُ بْنُ الْحُبَابِ أَخْبَرَنِي شُعْبَةُ بْنُ الْحَجَّاجِ حَدَّثَنَا قَتَادَةُ قَالَ: سَمِعْتُ أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ يَقُولُ صَلَّيْتُ خَلْفَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَبِي بَكْرٍ وَعُمَرَ وَعُثْمَانَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ فَلَمْ يَكُونُوا يَجْهَرُونَ بِـ {بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ}.



Aliyu Bn Abdullahi Bn Mubasshirin ya bamu labari, Ahmad Bn Sinaan ya bamu labari, Zaid Bn Hubban ya bamu labari, Shu'abatu Bn Hajjaj ya bamu labari, Qatadata ya bamu labari yace :


Naji Anas Bn Malik yana cewa :


" NAYI SALLAH A BAYAN MANZON ALLAH (S. A. W. W) DA ABUBAKAR DA UMAR DA USMANA (R. A)  AMMA BASU KASANCE SUNA BAYYANA " BISMILLAHIR-RAHMANUR-RAHEEM  " BA. 


              ABIN LURA 

Abinda wannan riwaya ke karantar mana shine, ana karanta Basmala cikin karatun salloli na farillah sai dai kuma ba a bayyanata kamar yadda Anas yace basa bayyanawa, domin da babu karantata da ba za ayi batun bayyanata ko rashin bayyanawar ba. 


(2)


«1217» حَدَّثَنَا الْحُسَيْنُ بْنُ يَحْيَى بْنِ عَيَّاشٍ الْقَطَّانُ حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ مُسْلِمٍ حَدَّثَنَا عُبَيْدُ اللَّهِ بْنُ مُوسَى حَدَّثَنَا شُعْبَةُ وَهَمَّامُ بْنُ يَحْيَى عَنْ قَتَادَةَ عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَبَا بَكْرٍ وَعُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا لَمْ يَكُونُوا يَجْهَرُونَ بِـ {بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ} وَرَوَاهُ يَزِيدُ بْنُ هَارُونَ وَيَحْيَى بْنُ سَعِيدٍ الْقَطَّانُ وَالْحَسَنُ بْنُ مُوسَى الأَشْيَبُ وَيَحْيَى بْنُ السَّكَنِ وَأَبُو عُمَرَ الْحَوْضِيُّ وَعَمْرُو بْنُ مَرْزُوقٍ وَغَيْرُهُمْ عَنْ شُعْبَةَ عَنْ قَتَادَةَ عَنْ أَنَسٍ بِغَيْرِ هَذَا اللَّفْظِ الَّذِي تَقَدَّمَ فَقَالُوا إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَبَا بَكْرٍ وَعُمَرَ وَعُثْمَانَ كَانُوا يَفْتَتِحُونَ الْقِرَاءَةَ بِـ {الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ} وَكَذَلِكَ رُوِيَ عَنِ الأَعْمَشِ عَنْ شُعْبَةَ عَنْ قَتَادَةَ وَثَابِتٍ عَنْ أَنَسٍ. وَكَذَلِكَ رَوَاهُ عَامَّةُ أَصْحَابِ قَتَادَةَ عَنْ قَتَادَةَ مِنْهُمْ هِشَامٌ الدَّسْتَوَائِيُّ وَسَعِيدُ بْنُ أَبِي عَرُوبَةَ وَأَبَانُ بْنُ يَزِيدَ الْعَطَّارُ وَحَمَّادُ بْنُ سَلَمَةَ وَحُمَيْدٌ الطَّوِيلُ وَأَيُّوبُ السَّخْتِيَانِيُّ وَالأَوْزَاعِيُّ وَسَعِيدُ بْنُ بَشِيرٍ وَغَيْرُهُمْ. وَكَذَلِكَ رَوَاهُ مَعْمَرٌ وَهَمَّامٌ وَاخْتُلِفَ عَنْهُمَا فِي لَفْظِهِ وَهُوَ الْمَحْفُوظُ عَنْ قَتَادَةَ وَغَيْرِهِ عَنْ أَنَسٍ.


Hussaini Bn Yahya Bn Ayyaash Al-Qaddanu ya bamu labari, Aliyu Bn Muslim ya bamu labari,  Ubaidullahi Bn Musa ya bamu labari, Shu'ubatu da Hammaam Bn Yahya ya bamu labari daga Qatadata daga Anas Bn Malik (cewa) :


" LALLE MANZON ALLAH (S. A. W. W) DA ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN BASU KASANCE SUNA BAYYANA (BISMILLAHIR-RAHMANUR-RAHEEM) BA. 


Yazeed Bn Haruna da Yahya Bn Sa'eed Al-Quddaanu da Hassan Bn Musa Al-Ashyabu da Yahya Bn Sakani da Abu Umara Al-Haudheey da Amruu Bn Marzuuqi dama wasunsu sun riwaito daga Shu'ubata daga Qatadata daga Anas da wani lafazi wanda ba wannan lafazin (na sama) da ya gabata ba, suka ce :


LALLE MANZON ALLAH (S. A. W. W) DA ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN SUN KASANCE SUNA BUDE KARATUN (sallah) NE DA " ALHAMDULILLAHIR-RABBIL AALAMEEN "


Kuma kamar haka aka riwaito daga A'amashi daga Shu'ubata daga Qatadata da Thaabit daga Anas.


Kuma kamar haka da yawa daga al'ummar Sahabban Qatadata daga Qatadata.  Daga cikinsu akwai; 


Hishaam Ad-Dastawaa'iyyu,  da 


Sa'eed Bn Abiy Aruubata, da


Abaanu Bn Yazeeda Al-Addaaru, da 


Hammaadu Bn Salamata, da


Humaidud-Daweelu, da 


Ayuba As-Sakhtiyaaniyyu, da


Auzaa'iyyu, da


Sa'eed Bn Bashir dama wasunsu. 


Kuma kamar haka Ma'amaru da Hammaamu sun riwaito shi, suka saba cikin lafazinsa (na biyu), kuma shi din abin kiyayewa ne daga Qatadata da waninsa daga Anas. "


           ABIN LURA 

Cikin wannan riwaya ta biyu an kawo daga Anas inda take tabbatar da riwayar farko ta cewa Manzon Allah (S. A. W. W) da Abubakar da Umar da Usman ba sa bayyanar da karatun Basmala a cikin karatun sallarsu. 


Sannan kuma a cigaban riwayar ya qara tabbatar da cewa lalle Manzon Allah (S. A. W. W) yana fara bude karatun sallah ne da karanta suratul-Fatihatul Kitaab, wanda hakan ke kore batun karanta Basmala a farkon sallah. 


(3)


«1220» حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ عُثْمَانَ بْنِ ثَابِتٍ الصَّيْدِلاَنِيُّ حَدَّثَنَا عُبَيْدُ بْنُ عَبْدِ الْوَاحِدِ بْنِ شَرِيكٍ حَدَّثَنَا هِشَامُ بْنُ عَمَّارٍ حَدَّثَنَا الْوَلِيدُ حَدَّثَنَا الأَوْزَاعِيُّ عَنْ إِسْحَاقَ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي طَلْحَةَ عَنْ أَنَسٍ قَالَ: كُنَّا نُصَلِّي خَلْفَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَبِي بَكْرٍ وَعُمَرَ وَعُثْمَانَ فَكَانُوا يَسْتَفْتِحُونَ بِأُمِّ الْقُرْآنِ فِيمَا يُجْهَرُ بِهِ.


Muhammad Bn Usmana Bn Thaabit As-Saidilaaniyyu ya bamu labari, Ubaidu Bn Abdulwaaheed Bn Shareeki ya bamu labari, Hishaam Bn Ammar ya bamu labari, Waleedu ya bamu labari, Auzaa'iyyu ya bamu labari daga Ishaq Bn Abdullahi Bn Abiy 'Dalhata daga Anas yace :


" MUN KASANCE MUNA SALLAH A BAYAN MANZON ALLAH (S. A. W. W) DA ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN, SUN KASANCE SUNA SUNA BUDE (karatun sallah ne) DA UMMUL-QUR'ANI (Fatiya) CIKIN INDA SUKE BAYYANA (karatu). "


            ABIN LURA 

Cikin wannan riwaya Anas yana tabbatar mana ne cewa Manzon Allah (S. A. W. W) da Abubakar da Umar da Usman dukkansu suna fara karatun sallarsu ce da karatun fatiya, wanda hakan ke nuna babu karanta Basmala cikin farkon karatun sallah. 


(4)


«1221» حَدَّثَنَا أَبُو بَكْرٍ يَعْقُوبُ بْنُ إِبْرَاهِيمَ الْبَزَّازُ حَدَّثَنَا الْعَبَّاسُ بْنُ يَزِيدَ حَدَّثَنَا غَسَّانُ بْنُ مُضَرَ حَدَّثَنَا أَبُو مَسْلَمَةَ- هُوَ سَعِيدُ بْنُ يَزِيدَ الأَزْدِيُّ- قَالَ: سَأَلْتُ أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ أَكَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَسْتَفْتِحُ بِـ {الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ} أَوْ بِـ {بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ} فَقَالَ: إِنَّكَ لَتَسْأَلُنِي عَنْ شَيْءٍ مَا أَحْفَظُهُ وَمَا سَأَلَنِي عَنْهُ أَحَدٌ قَبْلَكَ. قُلْتُ أَكَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُصَلِّي فِي النَّعْلَيْنِ قَالَ نَعَمْ. هَذَا إِسْنَادٌ صَحِيحٌ.


Baban Bakri Ya'aquba Bn Ibrahim Al-Bazzaazu ya bamu labari,  Abbasu Bn Yazeeda ya bamu labari, Ghassaanu Bn Mudhara ya bamu labari, Abu Maslamata (Sa'eed Bn Yazeeda Al-Azdiyyu) ya bamu labari yace :


" Na tambayi Anas Bn Malik, shin, Manzon Allah (S. A. W. W) ya kasance yana bude (karatun sallah) da " ALHAMDULILLAHIR-RABBIL AALAMEEN " ne ko kuma da " BISMILLAHIR-RAHMANUR-RAHEEM ?" Sai (Anas) yace :


" LALLE KAI KANA TAMBAYATA GAME DA WANI ABU WANDA BAN SAN SHI BA, KUMA WANI GABANINKA BAI YIMIN TAMBAYA GAME DASHI BA. "


Nace, " To, shin, Manzon Allah (S.A.W.W) ya kasance yana yin sallah cikin Takalma ?" Yace :


" EH,  (yana yi). "


Mai riwayar yace wannan isnadi ingantacce ne. 


SUNAN DARUL-QUDNIY, KITABUS-SALAH, BABIN SABANI CIKIN BAYYANA BASMALA, HADISAI MASU WADANNAN LAMBOBI : 1216,  1217,  1220, 1221)


               NAZARI


Idan muka nazarci wadannan riwayoyi guda hudu (4) za muga maganganu ne wadanda sashensu ke warware sashe, kuma a hakan ana tabbatar mana da cewa duk maganganun gaskiya ne. Ga dai abubuwan kamar haka daki-daki. 


(1)- Cikin Hadisi mai lamba 1216 yana nuna mana cewa Annabi (S. A. W. W) da Sahabbansa guda ukun nan duk ba sa bayyanar da karatun Basmala cikin sallolinsu, wanda hakan ke nuna ana karantawa sai dai a boye ne ba a bayyane ba.  Domin da ace ba a karantawa ba zai zama ya bada ma'ana ace ba a bayyanawa ba, sai dai ace ba a karantawa, Saboda sai ana karantawar ne za a iya sanin a bayyane ake karantawa ko a boye. 


(2)- Cikin Hadisi mai lamba 1217 kuma darusa biyu aka fitar. Na farko shine ba a bayyanar da Basmala, na biyu kuma Anas yana tabbatar da cewa ai da karatun Fatiya ake fara bude sallah, wanda hakan ke kore karanta Basmala a farkon karatu. 


(3)- A Hadisi mai lamba 1220 kuma Anas din ya qara tabbatar da cewa duk sallolin da yayi a bayan mutanen hudun nan suna fara bude karatun sallarsu ce da karanta Suratul-Fatihatul Kitaab. 


(4)- Cikin wannan riwaya ta Hadisi mai lamba 1221 kuma yayin da aka tambayi Anas game da menene farkon abinda Annabi (S. A. W. W) yake fara bude sallarsa da karanta shi sai yace don menene ba ayi masa tambaya game da abinda ya sani ba, kuma ma babu wanda ya taba yi masa irin wannan tambaya. Alhali cikin Hadisi na 1220 kuma ya nuna cewa da karatun Fatiya ake bude sallah. 


Idan ya zamana yana irin wadannan maganganu masu cin karo da juna ya kamata ace ana karbar riwaya daga gunsa bisa qa'ida ta malaman Hadisai? 


KUYI NAZARI YAA MA'ABOTA HANKALI  !!!


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


10th July, 2022/  11th Zul-Hijjah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post