@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ANA HUKUNTA MAWAQI NE DA ABINDA YAYI FURUCI DA SHI
A ma'ana ta hausa akan bambance tsakanin wadannan abubuwa biyu, wata waqa da kuma waqe.
Ita waqa ana fassara ta ne da nau'in kalmomin dake fitowa daga bakin wanda ya rerata, idan ta zama ta shafi nisadi ne ko roqo ko kuma yabon wani masarauci ko mai kudi ko kuma dan siyasa akan ce mata waqa.
Ita kuwa waqe ana fassarata ne da abinda ya shafi addini, kamar yabon Annabi (S. A. W. W) ko iyalan gidansa (A. S) ko kuma dai wasu bayin Allah salihai (Waliyyai).
Amma a muslimce babu wani abu wai shi waqe da ake bambance shi da waqa. Duk wani abinda za a rera shi kawai sunansa waqa, sai dai kuma ace wacce irin waqa ce ?
Allah (T) ya ambaci masu rera waqa da suna Shu'arah, sai kuma yayi mana bayanin bambancinsu inda yake cewa :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
﴿ وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلْغَاوُۥنَ (224)
" KUMA SU MAWAQA HALAKAKKU NE KE BIN SU. "
Cikin wannan aya bai bambance mana su ba, ya dai gaya mana ne matsayinsu da irin masu bin su, wanda hakan ke nuna mana su mawaqan da masu bin su duk halakakku ne. Sai ya nuna mana siffarsu cikin ayar dake biye kamar haka :
أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِي كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ *
" BA KAGA SU CIKIN KOWANNE TAFKI DIMUWA SUKE BA "?
وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لا يَفْعَلُونَ.
" KUMA SU SUNA FADIN ABINDA BA SHI SUKE AIKATAWA BA "?
Wannan shine siffofin mawaqa abin zargi wadanda ba a son ayyukansu dana mabiyansu, domin duk abinda suke yi babu Allah a ciki.
Daga nan kuma sai ya ambata mana nau'in mawaqa wadanda ya yarda da ayyukansu dana mabiyansu, inda yake cewa :
إِلا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَذَكَرُوا اللَّهَ كَثِيرًا وَانْتَصَرُوا مِنْ بَعْدِ مَا ظُلِمُوا وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنْقَلَبٍ يَنْقَلِبُونَ .
" SAI DAI WADANDA SU KAYI IMANI (cikin abinda suke fadi) KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA (cikin furucin nasu) KUMA SUKA AMBACI ALLAH DA YAWA, KUMA SU KAYI TAIMAKO (wajen bada kariya ga wanda aka zalunta) BAYAN AN ZALUNCE SHI. TO, DA SANNU WADANDA SU KAYI ZALUNCI ZA SU SAN CIKIN WACCE MAJUYA AKE JUYAR DA SU (wato cikin wacce irin makoma ake koyar da su)? "
(SURATUL-SHU'ARAH:224-227)
Sai kuma aka sami riwaya daga Darul-Qudniy yake cewa :
«4353» حَدَّثَنَا يَعْقُوبُ بْنُ إِبْرَاهِيمَ الْبَزَّازُ حَدَّثَنَا الْحَسَنُ بْنُ عَرَفَةَ حَدَّثَنَا إِسْمَاعِيلُ بْنُ عَيَّاشٍ عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ زِيَادِ بْنِ أَنْعُمَ عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ رَافِعٍ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((الشِّعْرُ بِمَنْزِلَةِ الْكَلاَمِ حَسَنُهُ كَحَسَنِ الْكَلاَمِ وَقَبِيحُهُ كَقَبِيحِ الْكَلاَمِ)).
Ya'aqub Bn Ibrahim Al-Bazzaazu ya bamu labari: Hassan Bn Arafata ya bamu labari: Isma'il Bn Ayyaash ya bamu labari daga Abdurrahman Bn Zayaadi Bn An'umu, daga Abdurrahman Bn Raafi'i, daga Abdullahi Bn Amruu Bn Ass yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace :
" ITA WAQA TANA MATSAYIN MAGANA CE, KYAWUNTA SHINE KYAWUN MAGANA, KUMA MUNINTA SHINE MUNIN MAGANA. "
(SUNAN, DARUL-QUDNIY: HADISI MAI LAMBA :4353)
Saboda haka ba wani abu ne waqa ba face magana, ana iya yin mummuniya ko kyakkyawuya. Idan ya zama an kyautata waqa ya zama an kyautata magana. Idan kuma aka munana waqa an munana magana.
Saboda haka duk waqa waqa ce, furucin da ya fito cikinta kawai ake fassara wacce irin waqa ce.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
19th May, 2022/ 18th Shawwal, 1443.