Me yasa jami'an tsaron Najeriya ke afkawa musulmi masu nuna goyon baya ga Falasɗinu ? | Habib Nasrallah

Daga © Habib Nasrallah

Abin ban takaicine da ban mamaki kasar da kowa ke da hakkin yayi addini daidai da fahimtarsa Kuma ya aikatashi ya aikace a bisa tsarin kundun tsarin kasar, Amman a wayi gari Ana AFKAWA musulman da suke goyan bayan Palatine wannan abin ban mamakine da Kuma nunawa duniya cewa mahaukatane ke mulkin kasar Nigeria.

    Kasashe daban daban ciki har da kasashen turai, duk karshen azimin watan ramadana sukan Yi taruka Dan nuna goyen bayansu ga Palatine, bazaka taba ji sun afkawa Yan kasarsuba Amman ban da kasata Nigeria. 

   Duk da irin halin da muke fuskanta na rashin tsaro duk lokacin da zaka fita baka da kwanciyar hankali Sai kaga kadawo gida, a wasu lokutan ma hatta kana cikin gida baka da aminci, Amman duk da haka gwamnati takasa magance rashin tsaro a Nigeria Amman a haka suke afkawa mutanan da Basu da makami laifinsu Dan sun nuna bayan goyen su ga Palatine.

  Idan harko goyan bayan Palatine laifine ya kamata gwamnati tayi doka ta hana batarinka sa ana kashe musulmi haka kawaiba. 

Akarshe kiranmu ga gwamnati Nigeria da jamian tsaro. 

    Ya kamata gwamnati Nigeria tasan cewar matsalar Yan Nigeria ba wai masu goyan bayan Palatine matsalarsuba matsalar mu shine kusamarwa da Yan kasa tsaro kuraya Yan kasa cikin amince ba kurinka kashesuba.

   Haka Suma JIMIAN TSARON Nigeria ya kamata kuyi tunani musamman idan Kai muslmine kokasan illar shekar da jinin Dan Adam guda daya a Duran kasa? Idan kai ba ka yarda da samuwar Allah ba, ai kana da hankali, tayaya gwamnati da ba ta iya biyama bukatunka ba kullum jia iyau ana turaku ana kasheku badare ba Rana, tare da cewar babu wani Abu da gwamnatin Nigeria take tsinanawa iyalanku bayan ku, watakila Wandanda kuke kashewa iyaye, Yaya, mata, kanne, su zasu taimaki iyalanka bayan da aka turaka aka kasheka, musamman lokacin da gwamnati ta kori iyalanka daga barrack bayan mutuwar ka ya kamata jamian tsaro Nigeria suyi wannan tunanin.

 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post