@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
GASKIYAR ANNABI (S.A.W.W) DA IKHLASINSA BAI HANA AN ZARGE SHI BA
Gaskiya, riqon amana, kunya, girmama na gaba da kuma mutunta na qasa shaida ce wacce aka yiwa Manzon Allah (S A.W.W) tun daga halin quruciyarsa, kuma ita ce kyakkyawar shaidar data bi shi har ya kai dan shekara arba'in (40) a duniya.
Bai tashi samun suka cikin wadannan kyawawan dabi'u nasa ba har sai bayan cika shekaru arba'in, a yayin da Allah ya umarce shi kan cewa ya kirayi al'umma zuwa kadaita Shi cikin bauta.
Fara isar da wannan saqo na Ubangijinsa ke da wuya sai ya soma cin karo da munanan maganganu daga al'ummar da sukayi masa wannan kyakkyawar shaida, suna cewa shi maqaryaci ne, boka ne, mawaqi ne kuma masihirci.
Wadannan maganganu sun tayar masa da hankali, amma tunda umarni ne na Allah bai fasa isar dashi kamar yadda aka umarce shi ba. Ba wani abu ne yasa aka qirqiro masa wadannan batanci ba sai don bin son zuciya da qin tabbatuwar abinda ake kiransu zuwa gare shi (kadaita Allah).
Cikin wannan yanayi ya qare rayuwarsa ba tare da ya sami cikakkiyar yarda da amincewa daga dukkan wadanda ke qarqashinsa ba. Rashin gaskata shi da rashin amince masa cikin dukkan abinda yake fada yasa tsoro da firgici cikin zuciyarsa har ya kasa furta kalmar qarshe wacce Ubangijinsa yayi masa umarni da ya isar da ita, har sai da ya ba shi tabbacin kariya daga gare Shi (S.W.A) sannan ya isar da wannan saqo.
Wannan saqo kuwa shine inda Allah ke cewa;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
" YAA KAI ANNABI ! KA ISAR ABINDA AKA SAUKAR ZUWA GARE KA DAGA UBANGIJINKA, IDAN BAKA AIKATA BA (haqiqa) BA KA ISAR DA SAQONSA BA, KUMA ALLAH ZAI KARE KA DAGA MUTANE."
Jin wannan bushara ta ba shi kariya tasa ya tsayar da mutane a filin Ghadeer ya isar da wannan saqo na cewa Imam Ali (A.S) ne jagoran kowanne mumini a bayansa.
Duk da wannan kariya da Allah ya ba shi bai hana wani fitowa ya zarge shi da cewa ya fifita dan'uwansa a kansu ba, kuma hakan bai hana abinda yake jin tsoro ya auku a kansa ba, domin qaryatawa yake tsoro, kuma abinda ya farun kenan a bayansa, har ma wasu su kayi taron sirri kan cewa sai sun kashe shi. Allah ya sanar dashi har ya tura Usamatu Bn Zaid yaje ya jiyo masa makircin da suke qullawa a kansa.
Darasin dake cikin wannan shine, in dai kana yin abu don Allah ne to, kada ka ji tsoron zargin masu zargi ko zagin masu zagi. A duk lokacin da ka tashi fadin gaskiya ka dogara kawai ga Allah kamar yadda yake cewa;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
" فَبِمَا رَحۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمۡۖ وَلَوۡ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلۡقَلۡبِ لَٱنفَضُّواْ مِنۡ حَوۡلِكَۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ وَشَاوِرۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِۖ فَإِذَا عَزَمۡتَ فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَوَكِّلِينَ." (٩٥١)
" SABODA RAHMA DAGA ALLAH KAYI RANGWAME A KANSU, DA ACE KA KASANCE MAI FUSHI MAI KAUSHIN ZUCIYA DA ZUN WATSE DAGA GEFEN KA. KA YAFE MUSU (kan duk abinda suka yi maka) KUMA KA NEMA MUSU GAFARA KUMA KA (jawo su a jika don tausayawa) YI SHAWARI DASU CIKIN AL'AMARI. IDAN KUMA KAYI AZAMA (wajen aikata wani abu na Ubangijinka sabanin abinda suke so), TO, KA DOGARA GA ALLAH (kawai ba tare da tunanin wacce irin fassara za suyi maka ba), LALLE ALLAH NA SON MASU DOGARO (gare Shi)."
(Al-IMRAN:159)
Tarihin quruciyar Sayyid Zakzaky (H) har zuwa yau abin sha'awa ce da fatan kasancewa kamarsa, domin ya taso cikin kyawawan dabi'u wadanda ko maqiyi ne ba zai zage shi ba. Amma fara wannan kira nasa don a dawo kan tsarin Allah ta hanyar karantarwar Annabi (S.A.W.W) da Iyalan gidansa (A.S) sai ya zama matsayinsa ya canza a wajen wasu har daga cikin 'yan'uwansa na jini, alhali kafin wannan lokaci basu zarge shi ba.
Yana daga cikin abinda wasu ke fada a kansa har zuwa yau, wai shi kafiri ne Zindiqi, suna hukunta masa hukuncin kisa da cewa wai ya kafirta. Wannan sai ya nuna mana irin abinda aka yiwa Manzon Allah (S.A.W.W) kenan kawai don ya zo musu da gaskiya daga Ubangijinsu.
To, yanzu kai a matsayinka na wanda ba wani ba kuma ba kowa ba in an kwatantaka da wadannan salihan bayin Allah dana bada misali a kansu, kace za kaji zafin wanda ya zage ka ko kaji tsoron zubewar mutuncinka wajen wasu don ka fadi gaskiya ?
IDAN HAR DON ALLAH KAKE YI BA ZA KAJI TSORON ZARGI KO ZAGIN MASU ZAGI BA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
2nd February, 2022/ 1st Rajab, 1443.