Sanadi haɗu wata da ɗan shi'a ya sa duk kanin rayuwata ta canza, ina zaune sai wani ɗan shi'a ya ganni ya ce yana sona duk da ya ce yana sona banƙi amsa masa ba. Sai nace masa to amma kasan ku ance ba mutanan kirkibane saboda ance kuna auran mutu'a! To gaskiya duk da ana gaya min haka Ni ban yarda ba gashi kazo kace kana sona to ina ganin yadda dangina zasu tsaneni ne, saboda na auri ɗan shi'a! Ana cikin haka sai na amsa masa soyayya da yazo min da ita sai nace naji na amince kuma zan aure ka duk abin da zai faru dani wallahi zan jure.
Ni gaskiya ina san ɗan shi'a batun yanzu ba tun'ina ƙaramata naji ina ƙaunar 'yan shi'a, kuma ina san nayita, sai dai matsala da nake ganin zanfuskanta dan gane da 'yan 'uwa na akan zan'auri ɗan shi'a. Gaskiya abin da yasa 'yan shi'a suka yi min wallahi shigarsu tana birgeni sosai kuma suna jan ra'ayina sosai bantaɓa ganin mutane irin 'yan shi'a ba. Abin da yasa nace haka duk kanin wata shiga ta mutunci to ka nemi 'yan shi'a mabiya Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), kuma gaskiya magana babu wanda ya kai su, san iyalan gidan Manzon Rahama (S). Dukkan wata shidima da ake wa gidan Manzo Allah wallahi ina da yaƙini babu wanda ya kai 'yan shi'a acikin ƙasar nan dama dukkanin duniya.
To, Ni dai nasamu kwanciyar hankali kuma na samu natsowa sosai fiye da yadda rayuwata ta ke ada wallahi yanzu kuma ina shiga ta kamala ina shiga ta kaya mutuncin zanrufe jikina sosai zansa suttura mai mutunci zanje wajan ta'alim insaurari jawabai da addu'o'i da akeyi sosai kuma ina samun natsowa sosai fiye da yadda rayuwata take abaya. Zan iya cewa da duk inda zanje to wallahi baiwuce nasaka (Gyale ba) dukkanin wata unguwa da zanje agidanmu ko zuwa wani gari ko wajan 'yan 'uwa na sai dai na ''ya fa Gyale kawai'', abuna gaskiya da ina tafiya tsirara ne. Amma yanzu gaskiya mutuncin saka suttura ta ya dawo kuma nagane gaskiyar lamari .
Yanzu kuma Ni (Zainab) duk da bansoba ace zanbaka sunana ba amma dan Allah kada ka bai yana sunan nawa ba da sunan ma haifina. Maganar da nake san zanyi ita ce batu na gaskiya babu duk abin da akecewa 'yan shi'a sunayi dangane da auran mutu'a wallahi ƙarya ne saboda nayi (tattaki) a shekarar 2013, na biyo mutanan yankin Katsina state, saboda ance min 'yan shi'a sunayin zina da matansu wanccan ya yi amfani da matar wanccan wannan ma haka amma naje na gane wa idanuna sosai naga karya ne wallahi babu wani abu da yake faruwa . Yadda naga naso nashiga ɓangaran maza aka hanani waɗannan mutanan da ake cewa (Harisawa ne sukaƙi subarni nashiga cikin maza )! Amma wallahi sunhanani na shiga cikin su. Sannan naga babu wani na miji da zai shi go cikin mata ba abarin wani namiji yazo ga mata wannan tambayar da cecekuce da ake cewa 'yan shi'a suna yi to ƙarya ne?
Batun zaman aure: gaskiya muna zaman aure lafiya da mijina kuma gaskiya yana bani kulawa sosain gaske, tunda yanzu gashi harmunyi aure muna tare da ɗan mu Aliyu.
Gaskiya ina mai kira da matan da suke cewa bazasu auri 'yan shi'a ba gaskiya hangen da su ke yi wallahi sudaina duk ƙarya ce kawai akewa mabiya mazhabar Ahlul-Baiti wato 'yan shi'a mabiya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), mutane ne masu gyara rushin ɗan adam kuma ina da yaƙini wallahi 'yan shi'a suna kan dai-dai sosai makuwa. Saboda Ni naga haƙiƙanin gaskiya magana idan mutum yai duba da abin da ya faru a shekarar dubu biyu (2015) da gwamnatin ƙasar nan ta yi ruwan wuta na kisan kiyashi fiye da mutum +10000, aka kashe akayi musu kisan gillah, acikin birnin Zaria dake jahar Kaduna Nigeria. Amma sai gashi Allah ya nuna aya akan 'yan shi'a mabiya Shaikh Ibraheem Zakzaky dan Allah ya nunawa Mutane cewar zalinci baya ɗorawa saidai adalci ya yi ikonsa.
Wakilinmu: wanda ke zaune acikin garin kagara dake ƙafur l.g.a jahar Katsina state ya zanta da wata baiwar Allah dake zaune acikin wani gari anan kusa da garin kagara duk da cewa ita wannan baiwar Allah ta ce masa kada ya bai yana ta, kuma bisa haka ne yasa muka ɓoye sunan garin, haƙiƙa idan kaje yadda tayi baya ni to zaka tausaya mata kuma idan kaji yadda ta samu nasara wajan auran da tayi sanadiyar wani brother, da yace yana santa haƙiƙa ta wanke wannan Harka hata yadda tayabi Harkar ita kanta, da kuma zargin da akewa mabiya mazhabar shi'a duk ta ƙaryata masha Allahu.
Allahumma salli alah Muhammadu wa'ali muhammad.
Daga_ Faruq Sani Kudan
26/1/2022