KA KIYAYE WANNAN DON KADA WATA RANA KAJI KUNYA
Shi dai rabon gado umarni ne na Allah (T) wanda ya zama wajibi a raba shi ga magada komai qanqantar abin aka bari, kuma komai yawansa. Rashin raba shi ko jinkirta shi babbar fitina ce, domin yakan haddasa rikici da gaba da juna tsakanin magada .
To, wannan rabo Allah ne da Kansa ya raba a tsakanin magada ya bawa kowa kasonsa gwargwadon matsayin da yake dashi wajen mamacin, sai dai kuma idan hakan ta faru masana ne ke rabawa saboda ba kowa ke da ilimin hakan ba.
Kason kowa yazo cikin Alqur'ani, saboda haka idan an tashi kaso akan duba abinda Allah ne ya bawa kowa. Sai a fitar kason kowa a bashi a matsayin haqqinsa.
Abinda yau muke son nusarwa shine, akwai yanayin magada wadanda idan ka bawa kowa kason da Allah yace a ba shi cikin Qur'ani wani zai rasa kaso mai yawa, a qarshe ka rasa yadda za kayi. Saboda haka za mu kawo misali guda daya a lura dashi don kada wataran mai rabo yaji kunya.
MISALI
Mata ce ta rasu ta bar 'ya'ya mata guda biyu da Uwa da kuma mijinta, tare da dukiya #780,000.
To, abinda Allah ya fada ana shine, za a bawa 'ya'ya mata kaso biyu ne daga cikin ukun abinda aka bari, Uwa kuma tana da kaso daya daga cikin kaso shida na abinda aka bari, shi kuma miji yana da kaso hudu ne na daga abinda aka bari.
YADDA KASON ZAI KASANCE
Sakamakon kason yazo ne a qasaru (fraction), to dole ka nemo abinda ake kira qaramar lamba wacce za ta raba wannan qasarun ya fito daidai, wato (L.C.M). Ga shi kamar haka;
'Ya'ya Uwa Miji
2 1 1
____ _____ ____
3 6 4
8 + 2 + 3 = 13
___________________
12
A bisa tsari na yadda ake lissafa wannan don ya fito fili shine, ana daukar kason kowa ne bisa asalin tushen abin (origin), sai ayi sau (multiply) da adadin abinda aka bari bisa daya.
MISALI
(1) 'Ya'ya
Kason su zai zama ne kamar haka;
3 780,000
___ × _______=#520,000
12 1
(2)- Uwa
2 780,000
___ × ________=#130,000
12 1
(3)- Miji
3 780,000
___ × ________=#195,000
12 1
Wannan shine kason da yazo cikin Qur'ani, saboda haka idan aka tara dukkan kason zai zama kamar haka;
'Ya'ya =#520,000
Uwa =#130,000
Miji =#195,000
___________
Total=#845,000
___________
___________
A wannan kaso zai zama an sami qaruwar kudi #65,000 kenan, saboda haka idan ka dau kason kowa a lissafi ka ba shi, to, na qarshe kuwa ba zai sami abinda kace shine kasonsa ba.
YADDA YA KAMATA AYI
Abinda ya kamata ayi shine, za a tara kason kowa ne wanda yazo wajen neman mafitar nan, wato 8+2+3 sai ya zama 13. To, anan sai ayi amfani da 13 wajen rabo maimakon 12 da akayi da ita a kason farko. Wannan kaso shi ake kira Awl.
GA SABON KASON DA ZAI KASANCE
(1)- 'Ya'ya
8 780,000
___ × _______=#480,000
13 1
(2)- Uwa
2 780,000
__ × _______=#120,000
13 1
(3)- Miji
3 780,000
___ × ________=#180,000
13 1
To, bari mu tara wannan kaso mu gani ko zai zo daidai da abinda matar ta bari.
'Ya'ya= #480,000
Uwa = #120,000
Miji = #180,000
___________
Total= #780,000
___________
___________
Wannan shine haqiqanin hanyar da za abi wajen warware mas'ala irin wannan mai rikitarwa.
ABIN LURA
Idan mu kayi la'akari da kason farko dana qarshe za muga 'ya'ya sun rasa #40,000 daga kason farko, Uwa ta rasa #10,000, miji kuma ya rasa #15,000, amma kuma kaso na biyun ya zo daidai da abinda aka bari na dukiyar.
YAA ALLAH KA QARA MANA ILIMI MAI AMFANI
🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
2nd January, 2022/ 28th Jimada-Ulah, 1443.