Wajibi ne sanin 'hadafin Harkar Muslunci' – Sheikh Zakzaky (H)


 _Daga Faruq Sani Kudan

To shi kenan dai, abin da muke cewa yanzu shi ne, mishkilar da muke fuskanta shi ne, akwai wani ana tafiya da shi a Harka ɗin, amma shi bai san ta inda aka ɗauko ba, bai san inda aka je ba. Saboda haka shi ya zo da wata fahimta tasa ta daban, to mai irin wannan fahimtar sai ya zauna, tun da abin da ya wuce, shi bai sani ba, da wuyar gaske da ya zama ya cafa ya yi kyakkyawar fahimta ga abun, sai ya tafi a haka nan.

Alal misali; akwai wata da aka tambaye ta, me ya sa take Harka? Sai ta ce (saboda) Son Ahlul-Baiti! 'Good Enough!', amma ban tsammanin ta fahimci abun sosai ba. Don haka yake da kyau irin waɗannan (Mu'utamarori,) manufar Mu'utamarori shi ne, a samu a kwakkwafa fikira, don ita fikira tana cigaba. Bari in muku misali da batun canzawa ɗin nan, menene canzawa? Canzawa shi ne kana abu fasa, ka yi wani abu daban. Alal misali da yanzu za a ce, sai mu ce yanzu dai gwagwarmayar nan dai ta ishe mu, kocikin waɗannan pipopi za mu shiga ɗaya, ko kuma za mu kafa ta mu (jam'iyyar). Ko mu shiga ''APC'' ko kuma kafa ''MBC'', sai a ce, yanzu sunan mu 'yan MBC. Shi kenan sai a ce MBC,. sai a ce yeeeeh! A tsayar da ɗan takara kawai a yi ta ihu

To wannan in ɗan kwamashiyal ya ga dama, sai ya ce ahaf, sun canza, sun koma suna Siyasa. To ka ga sosai canji ne wannan, tun da yake da can ga abin da ake yi, yanzu kuma an koma an ce za a tsaya takara ne.

Ko kuma mu ce gaskiyar al'amari shi ne, yanzu mun ga wannan al'amari da ɗan wahala, yanzu a shiga a gyara. Tun da akwai batun 'yan a shiga a gyara, don akwai masu wannan ra'ayin, ba mu san ina 'yan a shiga a gyara suka shiga ba, ko sun ''gyaggyaru'' ne ba mu sani ba. Shi ma sai a ce ai a baya ga ra'ayin su, amma yanzu kuma sun daina, sun daina sam-sam, sun koma sun ce da su za a dama abin da ake damawa.

'Yan Siyasa suna da wannan, har ma suna da wani slogan, 'If you cannot defeat them, join them', wato wannan take ne na 'yan siyasa, cewa, idan ɗan adawa ya yi adawar, ya yi adawar ya ga bai samu komai ba, sai ya ce to ya shiga jam'iyar da take mulki, shi ma a ɓantaro a bashi nasa, In aka yi magana, aka ce ya haka? Sai ya ce 'if you cannot defeat them, join them'.

To mu anan a siyasa, mutanen mu ba su san me ake ce masa adawa ba. Adawa 'yan Nijar suke cewa, mu kuma anan suna cewa hamayya. Adawa gaba kenan, to lallai adawan wasu suke yi sosai, idan mutum yana da wani ra'ayi, ba zai tsaya ƙyam akan wannan ra'ayin ba.

@Faruq Sani Kudan (Abban Jeedah)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post