Jagoran Harka Islamiyya Sheikh Zakzaky (H) |
Dama ita Harka Islamiyya tun farkon farawarta 'As a matter of Policy' mun nuna cewa akwai mata. Duk da matan da muka fara da su 'yan kaΙan ne, amma tsayawarmu a kan cewa lallai shi fa addini akwai mata sai ya zama a wajenmu aka fara ganin shigar mata harkar addini.
Har aka zo ya zama su ma masu ra'ayoyi ba irin namu ba, su ma suka riΖa shigar da mata a cikin harkokinsu, sai dai sun san namu ya fi nasu, don mu namu mutum zai iya ganin kusan rabi da rabi ne.
Saboda haka shigar mata a Harka ya canza ( ba ma kawai Harkar kaΙai ba), har da ma ganin sauran al'ummar Musulmi ga addini, don ya sa hatta masu ra'ayoyi ba irin namu ba, yanzu za ka ga mata a cikin abubuwan da suke yi.
Wani tsokaci ne da Shaikh Zakzaky ya yi tun shekarun baya zantawarsa da wasu masu bibiyar cimma matsaya dan ajiye tarishi Harkar musulunci da manufarta.
@_ Faruq Sani Kudan (Abban Jeedah)
15/1/202h)
15/1/2022