A irin wannan rana ta haihuwar shugabar matan duniya Sayyida Fatima Az-zahra(A.s) ina taya ku murna da farin ciki ga jagora Shaikh Zakzaky (H) da uwar dakina Malama Zeenatu tare da Mahaifiyata da Mahaifina da dukkanin Malamaina murna da zagayowar ranar haihuwar Sayyida Zahra ƴar Manzon Rahama (a.s) a irin wannan rana ta 20 ga watan Jimada Sani (Hijiriyyah).
Taya murna ta musamman ga dukkannin yan uwana na wulaya dana jini da dukkanin al'ummar duniya musulmi da kirista murna da wannan rana mai daraja.
Allah Ta'ala Ya sanya mu daga cikin ceton Sayyida Zahra, Ya maimaita mana na shekaru masu zuwa cikin lafiya da yalwar arziƙi.
– Abubakar Ibraheem Kudan
20th Jimada Sani,1442
23rd January, 2022