@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED@
ASALIN SOYAYYARTA SHINE YIN KOYI DA ITA (S.A)
Kamar yadda shahararren mawaqin gwagwarmayarnanne Alhaji Mustapha Umar Baba Gadon Qaya yayi wata waqa mai suna SON ANNABI KOYI DASHI, to, kamar haka yake, son Sayyidah Fatimah (S.A) shine koyi da ita cikin mu'amalarta da mijinta, zamantakewa da jama'ah da kuma ibadarta da tausayin bayin Allah baki daya.
Sau da yawa ana samun mutane masu nuna murnarsu ta haihuwar fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S.A.W.W) da kuma murnar haihuwar sauran A'imma da Ma'asumai (A.S) baki daya, sai dai kuma murnar tasu takan zama tamkar biki ne, domin ba sa daukar wani abin koyi daga dabi'un wadanda ake murnar haihuwar tasu.
Idan ya zama kana murna ta haihuwar wani Sha'a'ir na Allah amma ba ka koyi dashi daga kyawawan dabi'unsa, to, ya zama biki kake yi ba aikin lada wanda kake fatan samun sakamakonsa ba. Ita murnar haihuwa ta Annabi (S.A.W.W) da Iyalan gidansa (A.S) ibada ce wacce ake samun lada ta hanyar yinta, amma in ya zama biki kake yi to, babu wani ladan da kake samu sai dai nishadi.
'DABI'UN SAYYIDAH FATIMAH ZAHRAH (S.A)
Za mu kawo wasu nassosi dake nuna kyawawan dabi'un Sayyidah Fatimah (S.A) a matsayin Maulidin shafin (Ma'asumah Nigerian News Updates) don tunatarwa ga 'yan'uwa maza da mata don mu dau darasi daga rayuwarta (S.A)
GA KADAN DAGA CIKI
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
(1)- قرب الإسناد السِّنْدِيُّ بْنُ مُحَمَّدٍ عَنْ أَبِي الْبَخْتَرِيِّ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ: تَقَاضَى عَلِيٌّ وَ فَاطِمَةُ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ ص فِي الْخِدْمَةِ فَقَضَى عَلَى فَاطِمَةَ بِخِدْمَةِ مَا دُونَ الْبَابِ وَ قَضَى عَلَى عَلِيٍّ بِمَا خَلْفَهُ قَالَ فَقَالَتْ فَاطِمَةُ فَلَا يَعْلَمُ مَا دَاخَلَنِي مِنَ السُّرُورِ إِلَّا اللَّهُ بِإِكْفَائِي رَسُولُ اللَّهِ ص تَحَمُّلَ رِقَابِ الرِّجَالِ."
Ya zo cikin Qarrabul-Isnaad na Sindiyyu Bn Muhammad daga Abu Bakhratariy, daga Abu Abdullah daga babansa (A.S) yace:
" Aliyu da Fatimatu sun nemi hukunci zuwa ga Manzon Allah (S.A.W.W) cikin yin hidima, sai ya hukunta yin ayyukan cikin gida zuwa bakin qofa ga Fadimatu, kuma ya hukunta abinda ke bayansa ga Aliyu." Yace, sai Fadimatu:
" BAI SAN ABINDA YA SANYA NI CIKIN FARIN CIKI BA SAI DAI ALLAH DA MANZON ALLAH WANDA YA KALLAFA MIN ABINDA KE HAWA KAN WUYAN MAZAJE."
Idan muka kwatanta ayyukan cikin gida dana waje za muga ba qaramin aiki ne ke cikin gida ba, amma Annabi (S.A.W.W) ya dora shi kan Sayyidah (S.A).
Wannan babban aiki kuwa shine bada tarbiyyah ga 'ya'ya da karantar dasu wanda yafi kowanne aiki wahala, ita kuma ta qarawa kanta da sarrafa abinci ga mai gudanta da 'ya'yan don neman qarin lada.
Mu kuwa mafi yawan matanmu ba haka suke ba, domin maimakon bada tarbiyya ga 'ya'ya sai dai su lalata tarbiyyarsu ta hanyar nuna mummunan zamantakewarsu da mazajensu, da qoqarin nuna musu hanyar banza ta samun kudi.
Ita kuwa Sayyidah (S.A) tayi farin ciki da wannan aikin da mahaifinta ya zabar mata, kuma ta kiyaye wannan aiki har ya zama babu wani abinda za a zargeta akai ko a zargin 'ya'yanta ta fuskacin mummuniyar tarbiyya.
(2)- عيون أخبار الرضا عليه السلام بِالْأَسَانِيدِ الثَّلَاثَةِ عَنِ الرِّضَا عَنْ آبَائِهِ عَنْ عَلِيِّ بْنِ الْحُسَيْنِ ع أَنَّهُ قَالَ حَدَّثَتْنِي أَسْمَاءُ بِنْتُ عُمَيْسٍ قَالَتْ كُنْتُ عِنْدَ فَاطِمَةَ ع إِذْ دَخَلَ عَلَيْهَا رَسُولُ اللَّهِ ص وَ فِي عُنُقِهَا قِلَادَةٌ مِنْ ذَهَبٍ كَانَ اشْتَرَاهَا لَهَا عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ ع مِنْ فَيْءٍ فَقَالَ لَهَا رَسُولُ اللَّهِ ص يَا فَاطِمَةُ لَا يَقُولُ النَّاسُ إِنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ مُحَمَّدٍ تَلْبَسُ لِبَاسَ الْجَبَابِرَةِ فَقَطَعَتْهَا وَ بَاعَتْهَا وَ اشْتَرَتْ بِهَا رَقَبَةً فَأَعْتَقَتْهَا فَسُرَّ بِذَلِكَ رَسُولُ اللَّهِ ص."
Ya zo cikin Uyyunil-Akbaar na Ridha (A.S) da isnadodi uku daga Ridha daga iyayensa daga Aliyu Bn Hussaini (A.S) cewa yace: " Asma'u Bnt Umais tace: " Na kasance wajen Fadimatu (A.S) yayin da Manzon Allah (S.A.W.W) ya shiga gareta, kuma cikin wuyanta akwai sarqa ta Zinari wanda Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A.S) ya saya mata daga abinda suke samu na Ghanima (Fai'u). Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace mata:
" YAA FADIMATU ! KADA FA MUTANE SUCE LALLE FADIMATU 'YAR MUHAMMAD TANA SANYA KAYA IRIN NA MASU GIRMAN KAI (Jabbirai)."
Sai ta tsinketa (daga wuyanta) ta sayar da ita kuma ta sayo baiwa (slave) da ita (kudin zarqar) ta 'yantata. Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yayi farin ciki da hakan."
Su kuwa mafi yawan matanmu na wannan zamani in kaga baqin cikinsu shine basu sami kayan ado masu tsada daga mazajensu ba, kuma idan suka samu sai su zame musu abin fariya ba wai qanqan da kai ga Allah da nuna godiyarsu gare Shi daya sa suka samu ba. Kuma ma sai ya zama burinsu shine su sami wadanda za su riqa yi musu hidima irin wannan wanda zai sanya musu ganin fifikonsu akan wasu. Yin haka kuwa bai zama koyi ga Sayyidah Fatimah (S.A) ba.
(3)- علل الشرائع ابْنُ مَقْبُرَةَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ الْحَضْرَمِيِّ عَنْ جَنْدَلِ بْنِ وَالِقٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عُمَرَالْمَازِنِيِّ عَنْ عُبَادَةَ الْكَلْبِيِّ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَلِيِّ بْنِ الْحُسَيْنِ عَنْ فَاطِمَةَ الصُّغْرَى عَنِ الْحُسَيْنِ بْنِ عَلِيٍّ عَنْ أَخِيهِ الْحَسَنِ بْنِ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ ع قَالَ: رَأَيْتُ أُمِّي فَاطِمَةَ ع قَامَتْ فِي مِحْرَابِهَا لَيْلَةَ جُمُعَتِهَا فَلَمْ تَزَلْ رَاكِعَةً سَاجِدَةً حَتَّى اتَّضَحَ عَمُودُ الصُّبْحِ وَ سَمِعْتُهَا تَدْعُو لِلْمُؤْمِنِينَ وَ الْمُؤْمِنَاتِ وَ تُسَمِّيهِمْ وَ تُكْثِرُ الدُّعَاءَ لَهُمْ وَ لَا تَدْعُو لِنَفْسِهَا بِشَيْءٍ فَقُلْتُ لَهَا يَا أُمَّاهْ لِمَ لَا تَدْعِينَ لِنَفْسِكِ كَمَا تَدْعِينَ لِغَيْرِكِ فَقَالَتْ يَا بُنَيَّ الْجَارَ ثُمَّ الدَّارَ."
Ya zo cikin Ilalus-Sharaa'i'i na Ibn Maqburata daga Muhammad Bn Abdullahi Al-Hadhramiyyi, daga Jandali Bn Waliqi, daga Muhammad Bn Umaral-Maaziniy, daga Ubadatal-Kalbiy, daga Ja'afar Bn Muhammad daga babansa daga Aliyu Bn Hussain daga Fadimatu As-Sugraah, daga Hussaini Bn Aliyu , daga dan'uwansa Hassan Bn Aliyu Bn Abu 'Dalib (A.S) yace:
" Naga mahaifiyata Fadimatu (A.S) ta miqe cikin daren juma'ah a wajen ibadarta (Mihraab), bata gushe ba tana ruku'u da sujadah har sai da hasken asuba ya dago. Kuma na ji ta tana addu'ah ga muminai (maza) da muminai (mata) tana ambaton sunayensu (daya-bayan-daya) tana yawaita addu'ah gare su. Ba ta yin wata addu'ah ga kanta (not purposely for herself). Sai nace mata: " Yaa mahaifiyata ! Don menene ba kya yiwa kanki addu'ah kamar yadda kike yi ga wasunki ?" Sai tace:
" YAA 'DANA ! (fara da) MAQWABCI SANNAN GIDA."
(4)- علل الشرائع أَحْمَدُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ الْمَرْوَزِيُّ عَنْ جَعْفَرٍ الْمُقْرِي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ الْحَسَنِ الْمَوْصِلِيِّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَاصِمٍ عَنْ أَبِي زَيْدٍ الْكَحَّالِ عَنْ أَبِيهِ عَنْ مُوسَى بْنِ جَعْفَرٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ: كَانَتْ فَاطِمَةُ ع إِذَا دَعَتْ تَدْعُو لِلْمُؤْمِنِينَ وَ الْمُؤْمِنَاتِ وَ لَا تَدْعُو لِنَفْسِهَا فَقِيلَ لَهَا يَا بِنْتَ رَسُولِ اللَّهِ إِنَّكِ تَدْعِينَ لِلنَّاسِ وَ لَا تَدْعِينَ لِنَفْسِكِ فَقَالَتِ الْجَارَ ثُمَّ الدَّارَ.
Ya zo cikin Ilalus-Sharaa'i'i na Ahmad Bn Muhammad Bn Abdurrahman Al-Marwaziyyu, daga Ja'afarul-Muqriy, daga Muhammad Bn Hassan Al-Mausiliy, daga Muhammad Bn Aasim, daga Abu Zaidul-Kahhaali, daga babansa daga Musa Bn Ja'afar daga babansa daga iyayensa (A.S) yace: " Fadimatu (A.S) ta kasance idan za tayi addu'ah ta kanyi addu'ah ne ga muminai (maza) da muminai (mata), ba ta yin addu'ah ga kanta. Sai akace mata, yaa 'yar Ma'aikin Allah ! Lalle ke kina yin addu'ah ga mutane amma ba kya yi ga kanki. Sai tace:
" MAQWABCI SANNAN GIDA."
Wato abinda take koyar damu shine wannan ayar nan da Allah ya yabe su da ita cewa: " SUNA FIFITAWA AKAN KANSU KO DA KUWA SUNA DA BUQATUWA DA ABIN."
Yin hakan kuwa shine koyin da mahaifinta (S.A.W.W), domin har lokacin da Mala'ikan karbar rai yazo masa abinda ke fitowa daga bakinsa mai tsarki shine: " AL'UMMATA ! AL'UMMATA !!"
Wato a kullum su damuwa da damuwar al'umma ita ce babbar damuwarsu. Mu kuma na wannan zamani damuwar kanmu ita ce damuwa. Idan kuwa muka tabbata a haka haqiqa mu ba masoyanta na gaskiya bane tunda ayyukanmu yasha bamban da nata.
(5)- المناقب لابن شهرآشوب حِلْيَةُ أَبِي نُعَيْمٍ وَ مُسْنَدُ أَبِي يَعْلَى قَالَتْ عَائِشَةُ مَا رَأَيْتُ أَحَداً قَطُّ أَصْدَقَ مِنْ فَاطِمَةَ غَيْرَ أَبِيهَا.
Ya zo cikin Manaqeeb na Ibn Shahra-Ashub Hilyatu baban Nu'aim da kuma Musnad na Abu Yahla, A'ishatu (Ummul-muminina) tace:
" BAN TABA GANIN WANI MUTUM MAI GASKIYA KAMAR FADIMATU BA IN BA BABANTA BA."
Wato cikin shardar da Ummul-mumina ta yiwa Sayyidah Fatimah (S.A) shine gaskiyar magana kamar babanta, wanda hakan ke nuna cewa duk abinda kaji ya fito daga bakinta (S.A) gaskiya ne.
Wannan kuwa babban qalu-bale ne ga sistoci masu alaqantar da kansu gare ta, domin gaskiyar magana 69% daga cikinsu basu da gaskiya cikin mu'amalarsu da kuma maganganunsu.
وَ رَوَيَا أَنَّهُ كَانَ بَيْنَهُمَا شَيْءٌ فَقَالَتْ عَائِشَةُ يَا رَسُولَ اللَّهُ سَلْهَا فَإِنَّهَا لَا تَكْذِبُ.
Kuma an ruwaito daga gare shi (S.A.W.W) cewa, wani abu ya faru a tsakaninsu (A'isha da Fatimah), sai A'ishatu tace:
" YAA MA'AIKIN ALLAH ! KA TAMBAYETA DOMIN ITA BA ZA TAYI QARYA BA."
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج43، ص: 82
Wannan ba qaramar shaida bace kuma ba qaramin abin koyi bane daya kamata mu dauka daga rayuwar Sayyidah Fatimah (S.A) a daidai lokacin da muke tunawa da kuma murnar haihuwarta (S.A).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
24th January, 2022/ 21st Jimada-Sani, 1443.