BATA DA KASON KOMAI A HUKUNCIN ALLAH DA MANZONSA (S.A.W.W)
Duk da cewa ba za a zarqi malaman wannan zamani kai tsaye ba domin su ma haka suka tarar rubuci cikin littafansu daga magabatansu, sai dai za a iya zarginsu ta hanyar rashin amfani da hankali wajen tantance qarya da gaskiya.
Yana daga cikin abubuwan da aka jirkita na addinin muslimci karkatar da haqiqanin koyarwar Allah da Manzonsa (S.A.W.W) game da al'amarin rabon gado (inheritance).
Allah (T) ya bamu hankali ne don mu riqa tadabburin ayoyinSa don gane gaskiya daga qarya na abubuwan da za a kawo mana na son zuciya cikin addininmu na muslimci.
CIN GADON 'YAR'UWA TARE DA 'YA
Za muyi nazari cikin littafin Allah don sanin me yace game da hukuncin cin gado na 'yar'uwa ko dan'uwa yayin da dan'uwansu ke da 'ya ko da (son).
Allah (S.W.A) na cewa;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
يَسۡتَفۡتُونَكَ قُلِ ٱللَّهُ يُفۡتِيكُمۡ فِي ٱلۡكَلَٰلَةِۚ إِنِ ٱمۡرُؤٌاْ هَلَكَ لَيۡسَ لَهُۥ وَلَدٞ وَلَهُۥٓ أُخۡتٞ فَلَهَا نِصۡفُ مَا تَرَكَۚ وَهُوَ يَرِثُهَآ إِن لَّمۡ يَكُن لَّهَا وَلَدٞۚ فَإِن كَانَتَا ٱثۡنَتَيۡنِ فَلَهُمَا ٱلثُّلُثَانِ مِمَّا تَرَكَۚ وَإِن كَانُوٓاْ إِخۡوَةٗ رِّجَالٗا وَنِسَآءٗ فَلِلذَّكَرِ مِثۡلُ حَظِّ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۗ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ أَن تَضِلُّواْۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمُۢ . (٦٧١)
" SUNA YI MAKA FATAWA: KACE " ALLAH NA YI MUKU FATAWA CIKIN KALALA. IDAN MUTUM YA HALAKA BA SHI DA 'DA (bai haihu ba) KUMA YANA DA 'YAR'UWA, TO, TANA DA RABIN ABINDA YA BARI. KUMA SHI MA ZAI GAJE TA IN HAR ITA MA BATA DA 'DA (bata haihu ba). IDAN KUMA (su 'yan'uwa matan su biyu ne), TO, SUNA DA BIYU BISA UKU DAGA ABINDA (dan'uwansu) YA BARI. IDAN KUMA 'YAN'UWAN SUN KASANCE MAZA DA MATA NE, TO, NAMIJI NA DA KASO BIYU NA MACE. ALLAH NA YI MUKU BAYANI (dalla-dalla) DON KADA KU BACE, KUMA ALLAH MASANI NE GAME DA KOMAI."
(NISA'I, AYA 176)
NAZARI
___________
Idan muka nazarci ayar za muga Allah ya ambaci cewa 'yar'uwa za taci rabin abinda dan'uwanta ya bari ne in har bai haihu ba, domin kalmar (WALAD) anan ba tana nufi 'Da (son) bane, a'a tana nufin bai haihu bane ko kuma ya haihu amma abinda ya haifa din ba ya raye. Kaga anan Allah ya kawo sharadin za taci gadon dan'uwan nata ne bai bar wani abu raye daga cikin abinda ya haifa ba. Saboda haka samuwar 'ya ya kawar da 'yar'uwa bisa fadin Allah (T). Hakama dan'uwanta zai gaje ta ne in har bata haihu ba. Za mu iya fahintar WALAD da Allah yayi amfani da ita cikin wannan ayar data gaba ba tana nufin da (son) bane, a'a, tana nufin haihuwa ne
يُوصِيكُمُ ٱللَّهُ فِيٓ أَوۡلَٰدِكُمۡۖ لِلذَّكَرِ مِثۡلُ حَظِّ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۚ فَإِن كُنَّ نِسَآءٗ فَوۡقَ ٱثۡنَتَيۡنِ فَلَهُنَّ ثُلُثَا مَا تَرَكَۖ وَإِن كَانَتۡ وَٰحِدَةٗ فَلَهَا ٱلنِّصۡفُۚ وَلِأَبَوَيۡهِ لِكُلِّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا ٱلسُّدُسُ مِمَّا تَرَكَ إِن كَانَ لَهُۥ وَلَدٞۚ فَإِن لَّمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلَدٞ وَوَرِثَهُۥٓ أَبَوَاهُ فَلِأُمِّهِ ٱلثُّلُثُۚ فَإِن كَانَ لَهُۥٓ إِخۡوَةٞ فَلِأُمِّهِ ٱلسُّدُسُۚ.........(11)
" ALLAH NA YI MUKU WASIYYA CIKIN 'YA'YAYENKU, NAMIJI NA DA KASO BIYU NA MACE . IDAN 'YA'YA MATAN SUKA FI BIYU TO, SUNA DA BIYU BISA UKU NA ABINDA AKA BARI, IDAN KUMA TA KASANCE ITA 'DAYA CE, TO, TANA DA RABI. SU KUWA MAHAIFA KOWANNE DAGA CIKINSU YANA DA 'DAYA BISA SHIDA NA DAGA ABINDA YA BARI IN HAR YANA DA 'DA (Walad), IDAN KUWA BA SHI DA 'DA MAHAIFANSA NE KADAI SUKA GAJE SHI, TO, UWARSA NA DA 'DAYA BISA UKU, IDAN KUMA YANA DA 'YAN'UWA, TO, UWARSA NA DA 'DAYA BIDA SHIDA........
(NISA'I, AYA TA 11)
NAZARI
__________
Idan muka qara nazartar wannan aya za muga cewa Allah yayi amfani da kalmar WALAD cikinta. To, idan kace kalmar WALAD da akayi amfani da ita cikin wadannan ayoyi biyu na nufin da (son), to, idan kuma mutum ya bar 'ya mace ne ba namiji ba kana nufin hukuncin iyayen zai canza ne ? Kamar ace in ya bar 'ya mace ne ba daya bisa shida ne za a bawa kowanne daga cikin mahaifa ba ? Idan kuwa haka za a basu sai muce maka to, ashe kalmar WALAD na nufin haihuwa ne (namiji ko mace).
To, in har ya zama haka sai mu qara ce maka abinda yazo cikin aya ta 176 cikin suratun-Nisa'i shine 'yar'uwa ba za taci gadon dan'uwanta ba in har ya rasu ya bar 'ya mace raye. To, ta wanne dalili ne za ace 'ya na cin gado tare da 'yar dan'uwa ?
Idan kuma muka koma cikin hadisai za mu gani kamar haka;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
الإرشاد سُئِلَ أَبُو بَكْرٍ عَنِ الْكَلَالَةِ فَقَالَ أَقُولُ فِيهَا بِرَأْيِي فَإِنْ أَصَبْتُ فَمِنَ اللَّهِ وَ إِنْ أَخْطَأْتُ فَمِنْ نَفْسِي وَ مِنَ الشَّيْطَانِ فَبَلَغَ ذَلِكَ أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ ع فَقَالَ مَا أَغْنَاهُ عَنِ الرَّأْيِ فِي هَذَا الْمَكَانِ أَ مَا عَلِمَ أَنَّ الْكَلَالَةَ هُمُ الْإِخْوَةُ وَ الْأَخَوَاتُ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ وَ الْأُمِّ وَ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ عَلَى الِانْفِرَادِ وَ مِنْ قِبَلِ الْأُمِّ أَيْضاً عَلَى حِدَتِهَا قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ يَسْتَفْتُونَكَ قُلِ اللَّهُ يُفْتِيكُمْ فِي الْكَلالَةِ إِنِ امْرُؤٌ هَلَكَ لَيْسَ لَهُ وَلَدٌ وَ لَهُ أُخْتٌ فَلَها نِصْفُ ما تَرَكَ وَ قَالَ عَزَّ قَائِلًا وَ إِنْ كانَ رَجُلٌ يُورَثُ كَلالَةً أَوِ امْرَأَةٌ وَ لَهُ أَخٌ أَوْ أُخْتٌ فَلِكُلِّ واحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ فَإِنْ كانُوا أَكْثَرَ مِنْ ذلِكَ فَهُمْ شُرَكاءُ فِي الثُّلُثِ[13
An tambayi Abubakar game da (hukuncin) Kalala, sai yace: " Zan fada a kanta ne bisa ra'ayina, idan har na dace to, daga Allah ne, idan kuwa nayi kuskure (wajen bada amsa) to, daga gare ni ne kuma daga Shaidan. "
Sai labari ya riski shugaban muminai Imam Ali (A.S), sai yace:
" RA'AYI CIKIN WANNAN AL'AMARI BA ZAI WADATAR DASHI BA. AMMA BAI SAN CEWA KALALA SUNE 'YAN'UWA MAZA DA 'YAN'UWA MATA NE TA BANGAREN UWA DA UBA BA, DA KUMA BANGAREN UBA A KADAICE BA ? DA KUMA BANGAREN UWA BA? (wato kalala na kasancewa ne ta bangaren 'yan'uwa shaqiqai (full brothers and sisters) , da kuma bangaren uba LI'ABAI (consanguine brothers and sisters), ko kuma bangaren uwa LI'UMMAI (uttering brothers and sisters). ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA: " SUNA YI MAKA FATAWA, KACE: " ALLAH NA YI MUKU FATAWA GAME DA KALALA. IDAN MUTUM YA HALAKA KUMA BA SHI DA 'DA (bai haihu ba) AMMA KUMA YANA DA 'YAR'UWA, TO, TANA DA RABIN ABINDA YA BARI."
KUMA ALLAH YA FADA YANA MAI CEWA: " IDAN MUTUM YA KASANCE AN GAJE SHI A MATSAYIN KALALA KO KUMA MACE KUMA YANA DA 'DAN'UWA KO 'YAR'UWA, TO, KOWANNE DAGA CIKINSU YANA DA 'DAYA BISA SHIDA, IDAN KUMA SUKA KASANCE SUNFI HAKA, TO, SAI SUYI TARAYYA CIKIN 'DAYA BISA UKU."
(NISA'I, AYA TA 13)
(إرشاد المفيد ص 107 طبع النجف.)
To, wannan aya kuma na magana ne kadai kan 'yan'uwa wadanda aka hadu dasu ta bangaren mahaifiya ba 'yan'uwa shaqiqai ko li'abai ba.
Sannan kuma ya zo cikin Tafsir na Ayyashi cewa;
تفسير العياشي عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ مُسْلِمٍ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: إِذَا تَرَكَ الرَّجُلُ أُمَّهُ وَ أَبَاهُ وَ ابْنَتَهُ أَوِ
ابْنَهُ فَإِذَا هُوَ تَرَكَ وَاحِداً مِنْ هَؤُلَاءِ الْأَرْبَعَةِ فَلَيْسَ هُوَ مِنَ الَّذِي عَنَى اللَّهُ فِي قَوْلِهِ- قُلِ اللَّهُ يُفْتِيكُمْ فِي الْكَلالَةِ لَيْسَ يَرِثُ مَعَ الْأُمِّ وَ لَا مَعَ الْأَبِ وَ لَا مَعَ الِابْنِ وَ لَا مَعَ الِابْنَةِ إِلَّا زَوْجٌ أَوْ زَوْجَةٌ فَإِنَّ الزَّوْجَ لَا يَنْقُصُ مِنَ النِّصْفِ شَيْئاً إِذَا لَمْ يَكُنْ مَعَهُ وَلَدٌ وَ لَا يَنْقُصُ الزَّوْجَةُ مِنَ الرُّبُعِ شَيْئاً إِذَا لَمْ يَكُنْ مَعَهَا وَلَدٌ.
Daga Muhammad Bn Muslim, daga Abu Ja'afar (A.S) yace: " Idan mutum yabar Uwarsa da Ubansa da 'yarsa ko dansa, to, idan har yabar daya (1) daga cikin hudun nan, to, bai kasance cikin wadanda Allah ya ambata cikin fadinSa:
" KACE: " ALLAH NA YI MUKU FATAWA CIKIN KALALA." ba.
Babu wanda zaiyi gado tare da Uwa ko tare da Uba ko tare da da ko tare da 'ya ba sai dai miji (husband) ko mata (wife). Domin shi miji ba a tauye masa wani abu daga rabi in dai har babu da (son/daughter) tare dashi, sannan kuma ba a tauyewa mata (wife) wani abu daga daya bisa hudu (one over four) in har babu wani da (son or daughter) tare da ita."
تفسير العيّاشيّ ج 1 ص 226
Wannan shine hukuncin Allah da Ma'aikinsa (S.A.W.W). Sai dai kuma wani abin mamaki an canza wannan hukunci na Allah an shigo da 'yan'uwa suna cin gado tare da 'yar dan'uwansu ko kuma mahaifiyar dan'uwansu.
Idan muka koma cikin aya ta 11 cikin suratun Nisa'i inda Allah ya ambaci cewa idan mutum ya rasu kuma yana da 'yan'uwa uwarsa na da kaso daya ne bisa shida ba hakan na nuna cewa 'yan'uwan na da gado bane, a'a, su dai sunyi sanadin ciro uwar mamacin ne daga samun kashi daya bisa uku zuwa samun kashi daya (1) daga cikin shida, wato dai sun qarawa uba qarfi ne.
WAI MENENE YA RUFEWA MUTANE IDO NE DAGA GANE GASKIYA HAR SUKA 'DORU SUNA HUKUNCI DA ABINDA YA SABAWA HUKUNCIN ALLAH DON MAGABATA SUN KAWO?
Lalle wannan ba zai TANA zama uzuri wajen Allah ba kace Masa ai haka ka ganin cikin littafan magabata, domin kuwa ya ba ka Al-Qur'ani kuma ya qara maka da hankali yace ka riqa yin tunani cikin ayoyinSa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
20th January, 2022/ 17th Jimada-Saniy, 1443.