Mai hankali ya fi kusa da Ubangiji fiye da mai yin hukunci ba tare da hankali ba


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MAI HANKALI YA FI KUSA DA UBANGIJI FIYE DA MAI YIN HUKUNCI BA TARE DA HANKALI BA 

Ba qaramin kuskure bane ko rashin sani ace wai sharia sabanin hankali ce. A kowanne lokaci sharia na tafiya ne daidai da hankali, idan har kaga ta saba da hankali to, ka kirata hauka ba sharia ba, domin duk abinda ka sani mai kyau na tafiya ne da hankali.

Abinda yafi dacewa a fada a fahintata shine, sharia sabanin jahilci, domin bisa jahilci akan iya hukunta wani al'amari sai kuma yazo sabanin sharia, saboda sharia na tafiya ne da ilimi da hankali.

Bari mu duba wasu riwayoyi don musan matsayin hankali a sharia, suna sabawa ne ko kuma dai tare suke tafiya.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

 قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ مَا قَسَمَ اللَّهُ لِلْعِبَادِ شَيْئاً أَفْضَلَ مِنَ الْعَقْلِ فَنَوْمُ الْعَاقِلِ أَفْضَلُ مِنْ سَهَرِ الْجَاهِلِ وَ إِفْطَارُ الْعَاقِلِ أَفْضَلُ مِنْ صَوْمِ الْجَاهِلِ وَ إِقَامَةُ الْعَاقِلِ أَفْضَلُ مِنْ شُخُوصِ الْجَاهِلِ وَ لَا بَعَثَ اللَّهُ رَسُولًا وَ لَا نَبِيّاً حَتَّى‏ يَسْتَكْمِلَ الْعَقْلَ وَ يَكُونَ عَقْلُهُ أَفْضَلَ مِنْ عُقُولِ جَمِيعِ أُمَّتِهِ وَ مَا يُضْمِرُ النَّبِيُّ فِي نَفْسِهِ أَفْضَلُ مِنِ اجْتِهَادِ الْمُجْتَهِدِينَ وَ مَا أَدَّى الْعَاقِلُ فَرَائِضَ اللَّهِ حَتَّى عَقَلَ مِنْهُ وَ لَا بَلَغَ جَمِيعُ الْعَابِدِينَ فِي فَضْلِ عِبَادَتِهِمْ مَا بَلَغَ الْعَاقِلُ إِنَّ الْعُقَلَاءَ هُمْ أُولُو الْأَلْبَابِ الَّذِينَ قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ‏- " إِنَّما يَتَذَكَّرُ أُولُوا الْأَلْبابِ‏."

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 92

Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa;

" BABU WANI ABU DA ALLAH YA RABA SHI GA BAYI WANDA YAFI HANKALI. BACCIN MAI HANKALI YA FI (aikin) GAJIYA NA JAHILI, KUMA SHAN RUWAN (rashin yin azumin) MAI HANKALI YA FI FALALA DAGA AZUMIN JAHILI, KUMA TSAYUWAR MAI HANKALI (ba tare da ya aikata wani abu ba) YA FI AIKIN JAHILI, KUMA ALLAH BAI TABA AIKO DA MANZO KO ANNABI BA HAR SAI YA CIKA MASA HANKALI, SAI HANKALINSA YAFI HANKALIN DUKKAN AL'UMMA. KUMA ABINDA KE BIJOROWA (na tunani) CIKIN ZUCIYAR ANNABI YA FI IJTIHADIN MUJTAHIDAI (masu qoqari wajen fitar da hukunci ba tare da aiki da hankali cikinsa ba). 

KUMA MAI HANKALI BA ZAI SAUKE WANI ABINDA ALLAH YA FARLANTA MASA BA HAR SAI YA HANKALCE SHI (ta hanyar tunani da sanin cewa lalle wanda yayi masa wannan umarni ya cancanta da ayi masa biyayya, ba wai bawan zai aikata kawai don anyi masa umarni bane). KUMA DUKKAN BAYI BA ZA SU KAI GA SAMUN FALALAR IBADARSU BA KAMAR YADDA MAI HANKALI ZAI KAI BA. LALLE MA'ABOTA HANKALI SUNE MASU HANKALIN NAN DA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YACE:

" LALLE MASU HANKALI KADAI KE WA'AZANTUWA."

NB:- Hankali shine ke yarda da tabbatar da cewa abinda aka zartar wanda yazo daidai da shariar Allah da Manzonsa (S.A.W.W) ita ce daidai, amma rashin hankali na kallon shariar Allah da Manzonsa (S.A.W.W) ne a matsayin ba daidai ba, shi yasa aka zabi hukuncin wanin Allah a matsayin shi yafi dacewa ayi aikin da shi.

 رُوِيَ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ أَنَّهُ قَالَ: أَسَاسُ الدِّينِ بُنِيَ عَلَى الْعَقْلِ وَ فُرِضَتِ الْفَرَائِضُ عَلَى الْعَقْلِ وَ رَبُّنَا يُعْرَفُ بِالْعَقْلِ وَ يُتَوَسَّلُ إِلَيْهِ بِالْعَقْلِ وَ الْعَاقِلُ أَقْرَبُ إِلَى رَبِّهِ مِنْ جَمِيعِ الْمُجْتَهِدِينَ بِغَيْرِ عَقْلٍ وَ لَمِثْقَالُ ذَرَّةٍ مِنْ بِرِّ الْعَاقِلِ أَفْضَلُ مِنْ جِهَادِ الْجَاهِلِ أَلْفَ عَامٍ.

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 95

An riwaito daga Ibn Abbas (R.A) yana cewa:

" ASALIN ADDINI AN GINA SHI NE KAN HANKALI, KUMA AKA FARLANTA FARILLAI BISA HANKALI, KUMA UBANGIJINMU ANA SANINSA NE DA HANKALI, KUMA ANI TAWASSULI ZUWA GARE SHI DA HANKALI. MAI HANKALI YA FI KUSA GA UBANGIJINSA FIYE DA MASU FITAR DA HUKUNCI BA TARE DA HANKALI BA. KUMA KOMAI QANQANTAR AIKIN ALHERI NA MAI HANKALI YA FI (girman lada) FIYE DA JIHADIN JAHILI NA SHEKARA DUBU ."

Ashe kuwa tunda asalin addini an gina shi ne bisa hankali, to, dole kuwa sharia tazo daidai da hankali ba sabaninsa ba in dai har ta Allah da Ma'aikinsa (S.A.W.W) ce.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

          (08137925034)

19th January, 2022/ 16th Jimada-Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post