Kambama Khalifa Usman: 'Daukaka daraja ko cin zarafin Manzon Allah (S)' ??


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

QOQARINSU SHINE SU NUNA CEWA USMAN BN AFFAN YA FI ANNABI (S.A.W.W) KUNYA

Mun sha fada a baya cewa, idan ka cire Imam Ali (A.S) cikin manyan Sahabbai babu wani wanda za a kawo falalarsa ba tare da an ci zarafin Manzon Allah (S.A.W.W) ta wata fuska ba.

Wannan kuwa na da alaqa ne da irin qarerayin da ake yi na cewa Sayyidina Abubakar, Umar da Usman na gaba da Imam Ali (A.S) a girman daraja. Saboda hakane ake qirqiro wasu hadisai don tabbatar da wannan shadi-fadin nasu.

Ita kuwa qarya in dai har anyi ta, to, dole ya zama an qara qirqiro wasu qarerayin don a tabbatar da qaryar farko a matsayin gaskiya. A qoqarin hakan kuma sai a taba darajar Manzon Allah (S.A.W.W) ba fifita wani ba tare da ganin matsayin wanda aka taba martabar tasa ba.

Bari mu kawo misali guda daya kan wani hadisi da aka kawo a matsayin martabar Sayyidinah Usman Bn Affan.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

503- حَدَّثَنَا حَجَّاجٌ ، حَدَّثَنَا لَيْثٌ ، حَدَّثَنِي عُقَيْلٌ ، عَنِ ابْنِ شِهَابٍ ، عَنْ يَحْيَى بْنِ سَعِيدِ بْنِ الْعَاصِ ، أَنَّ سَعِيدَ بْنَ الْعَاصِ أَخْبَرَهُ ، أَنَّ عَائِشَةَ زَوْجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، وَعُثْمَانَ حَدَّثَاهُ : أَنَّ أَبَا بَكْرٍ اسْتَأْذَنَ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، وَهُوَ مُضْطَجِعٌ عَلَى فِرَاشِهِ ، لَابِسٌ مِرْطَ عَائِشَةَ ، فَأَذِنَ لِأَبِي بَكْرٍ وَهُوَ كَذَلِكَ ، فَقَضَى إِلَيْهِ حَاجَتَهُ ، ثُمَّ انْصَرَفَ ، ثُمَّ اسْتَأْذَنَ عُمَرُ ، فَأَذِنَ لَهُ وَهُوَ عَلَى تِلْكَ الْحَالِ ، فَقَضَى إِلَيْهِ حَاجَتَهُ ، ثُمَّ انْصَرَفَ ، قَالَ عُثْمَانُ : ثُمَّ اسْتَأْذَنْتُ عَلَيْهِ ، فَجَلَسَ ، وَقَالَ لِعَائِشَةَ : " اجْمَعِي عَلَيْكِ ثِيَابَكِ " ، فَقَضَى إِلَيَّ حَاجَتِي ، ثُمَّ انْصَرَفْتُ ، قَالَتْ عَائِشَةُ : يَا رَسُولَ اللَّهِ ، مَا لِي لَمْ أَرَكَ فَزِعْتَ لِأَبِي بَكْرٍ ، وَعُمَرَ ، كَمَا فَزِعْتَ لِعُثْمَانَ ؟ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " إِنَّ عُثْمَانَ رَجُلٌ حَيِيٌّ ، وَإِنِّي خَشِيتُ إِنْ أَذِنْتُ لَهُ عَلَى تِلْكَ الْحَالِ ، أَنْ لَا يَبْلُغَ إِلَيَّ فِي حَاجَتِهِ " ، وقَالَ اللَّيْثُ : وَقَالَ جَمَاعَةُ النَّاسِ : إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، قَالَ لِعَائِشَةَ : " أَلَا أَسْتَحْيِي مِمَّنْ يَسْتَحْيِي مِنْهُ الْمَلَائِكَةُ " ، حَدَّثَنَا يَعْقُوبُ ، حَدَّثَنَا أَبِي ، عَنْ صَالِحٍ ، قَالَ ابْنُ شِهَابٍ : أَخْبَرَنِي يَحْيَى بْنُ سَعِيدِ بْنِ الْعَاصِ ، أَنَّ سَعِيدَ بْنَ الْعَاصِ أَخْبَرَهُ ، أَنَّ عُثْمَانَ ، وَعَائِشَةَ حَدَّثَاهُ ، أَنَّ أَبَا بَكْرٍ اسْتَأْذَنَ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، وَهُوَ مُضْطَجِعٌ عَلَى فِرَاشِهِ ، لَابِسٌ مِرْطَ عَائِشَةَ . . فَذَكَرَ مَعْنَى حَدِيثِ عُقَيْلٍ .

Imam Ahmad yace: Hajjaj ya bamu labari, Laithee ya bamu labari, Uqailu ya bani labari daga Ibn Shihaab, daga Yahya Bn Sa'eed Bn Ass, cewa Sa'eed Bn Ass ya ba shi labari cewa A'ishatu matar Annabi (S.A.W.W) da Usman sun ba shi labari:

Lalle Abubakar ya nemi iznin (shiga wajen) Manzon Allah (S.A.W.W) alhali yana kishingide akan shimfidarsa ya sanya rigar A'ishatu, sai ya yiwa Abubakar izni cikin wannan hali, ya biya masa buqatarsa sannan ya tafi.

Sannan Umar ya nemi izni, sai yayi masa izni (na shigowa) cikin yanayin da yake ciki (ba tare da ya ji kunya ba), ya biya masa buqatarsa sannan (shi ma) ya fita.

Usman yace: " Sannan nima na nemi izninsa, sai ya (tashi) ya zauna (maimakon ya tsaya a halin da yake ciki). Sai ya cewa A'ishatu: " KI 'DAUKE TUFAFINKI (wanda na lulluba dashi)." Sai ya biya min buqatata sannan na juya."

A'ishatu tace: " Yaa Ma'aikin Allah ! Me yasa ni ban ganka ka firgita yayin da kaga Abubakar da Umar ba kamar yadda ka firgita da (ganin) Usmana ?" 

Manzon Allah (S.A.W.W) yace: " AI SHI USMAN MUTUM NE MAI JIN KUNYA (Abubakar da Umar kuwa ba su da kunya), SAI NAJI TSORON IN HAR NAYI MASA IZNI A WANNAN HALI (da nake ciki) BA ZAI IYA ISAR MIN DA BUQATARSA BA."

Laithuu yace: Jama'ar mutane suka ce: Lalle Manzon Allah (S.A.W.W) ya cewa A'ishatu:

" YANZU BA ZANJI KUNYAR WANDA MALA'IKU KE JIN KUNYARSA BA?"

Ya'aqubu ya bamu labari, Babana ya bamu labari daga Salih. Ibn Shihaab yace: Yahya Bn Sa'eed Bn Ass ya bani labari cewa: Lalle Sa'eed Bn Ass ya ba shi labari cewa Usman da A'ishatu sun ba shi labari cewa Abubakar ya nemi iznin shiga ga Manzon Allah (S.A.W.W) alhali yana kishingide akan shimfidarsa ya sanya rigar A'ishata ......sai ya ambaci ma'anar hadisin Uqail."

(MUSNAD IMAMU AHMAD, HADISI MAI LAMBA 503)

                    DARASI

             ______________

Cikin wannan hadisi za mu iya fitar da darasosi masu yawan gaske, amma dai za mu taqaita kan wadannan.

(1)- Manzon Allah (S.A.W.W) na iya aikata wata dabi'a abin zargi wanda ba ya jin kunyar Allah balle ta Mala'ikun dake tare da shi, sannan kuma zai iya aikata wani abu a gaban wasu ba tare da jin kunyarsu ba.

(2)- Abubakar da Umar ma basu da kunya tunda za su iya ganin Annabi (S.A.W W) cikin wani yanayi na kunya amma su ba za suji kunya ba.

(3)- Usman ya fi Annabi (S.A.W.W) kunya tunda zai iya ganinsa cikin wani irin yanayin da bai kamata ace wani ya gan shi ba amma shi (S.A.W.W) bai ji kunyar wasu su gan shi ba.

(4)- Wannan abinda Annabi (S.A.W.W) ya aikata abin zargi ne wanda bai dace ace mai kunya ya gan shi ba, sai dai in mutum marar kunya ne.

(5)- Wannan jin kunyar da Mala'iku ke yiwa Usman shi kadai ta nuna cewa yafi kowa jin kunya daga cikin Sahabbai har ma da mai sahabban tunda shi kadai aka riwaito cewa Mala'iku na jin kunyarsa. Kuma masu karin magana na cewa: " ME KUNYA NE AKE JIN KUNYARSA, AMMA JIN KUNYAR MARAR KUNYA TSORO NE!"

                    NAZARI

                 ___________

Akwai yiwuwar wani yace ai shi Abubakar da Umar suna da 'ya'yansu ne a cikin gidan, wato Annabi (S.A.W.W) na auren 'ya'yansu ne shi yasa ba zai ji kunyarsu ba.

Idan kuwa kace haka sai muyi maka tambaya da cewa;

(1)- Shin, ba ance Usman ya auri 'ya'ya biyu na Manzon Allah (S.A.W.W) ba?

(2)- Menene bambanci matsayin wanda kake auren 'yarsa da wanda yake auren 'yarka ko ya taba auren 'yarka ?

(3)- Ashe za ka iya jin kunyar wanda ya auri 'yarka amma kuma ba za kaji kunyar wanda kake auren 'yarsa ba?

(4)- Menene ya bambanta matsayin mijin 'yarka da uban matarka a wajenka ta fuskacin jin kunya?

ANNABI (S.A.W.W) YA FI KOWA JIN KUNYA

Kunya na daga cikin siffofi na kamalar Annabawa (A.S), shi yasa ma Allah ya ambaci da Manzonsa (S.A.W.W) da cewa;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

" وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٖ." (٤)

" KUMA LALLE HAQIQA KAI KANA KAN KYAWAWAN 'DABI'U MASU GIRMA."

(Suratul-Qalaam:4)

Sannan kuma Bukhari ya riwaito cewa;

 (6119) - حدثنا علي بن الجعد: أخبرنا شُعبة، عن قتادة، عن مولى أنس - قال أبو عبد الله: اسمه عبد الله بن أبي عتبة - سمعت أبا سعيد يقول: 

كان النبي صلى الله عليه وسلم أشد حياء من العذراء في خدرها ."

Aliyu Bn Ja'ad ya bani labari, Shu'aibata ya bamu labari daga Qatadata, daga bararren bawan Anas. Abu Abdullahi yace: Sunansa shine Abdullahi Bn Abiy Utbata. Na ji baban Sa'eed yana cewa:

" ANNABI (S.A.W.W) YA KASANCE SHI YAFI JIN KUNYA FIYE DA AMARYA CIKIN LULLUBINTA."

(Sahihul-Bukhari, Kitabul-Adaab, babun hayaa'i, hadisi mai lamba: 6119)

Tabbas wannan magana haka take, domin duk wani mai jin kunya Annabi (S.A.W.W) ya fi shi jin kunya, kuma wanda yafi kowa jin kunya shi za afi jin kunyarsa, sai dai ba a kawo cewa ana jin kunyar Annabi (S.A.W.W) wanda shi yafi kowa jin kunya ba.

" KUYI TUNANI YAA KU MA'ABOTA HANKALI."

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

15th January, 2022/ 13th Jimada-Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post