Ina bautawa Allah ne kawai don ina sonsa (In ji Imam Sadiq (A.S)


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

HANYAR DA ZA KABI DON KASAN MATSAYINKA WAJEN ALLAH

Allah a matsayinsa na Ubangiji wanda ya umarce mu da mu bauta masa ya zama wajibi a nauta Masa matuqar dai da imani, sai dai kuma mutane na bauta Masa ne saboda wasu dalilai nasu. Kowa da ka sani yana bautawa Allah ne bisa wata manufa tasa, ba a hadu kan manufa daya (1) wajen bauta Masa ba.

Dalilan da yasa ake bautawa Allah ya kasu kashi uku ne, amma kai bisa wacce hujja kake bautar Ubangijinka ? Imam Ja'afarus-Sadiq (A.S) ya bayyana mana dalilan da yasa mutane ke bautar Ubangijinsu, kuma ya fada mana nasa dalilin na bautar Ubangijinsa kamar haka;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

علل الشرائع السِّنَانِيُّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ هَارُونَ عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ مُوسَى الْحَبَّالِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ الْحُسَيْنِ الْخَشَّابِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ الْحَسَنِ عَنْ يُونُسَ بْنِ ظَبْيَانَ قَالَ قَالَ الصَّادِقُ ع‏ إِنَّ النَّاسَ يَعْبُدُونَ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ عَلَى ثَلَاثَةِ أَوْجُهٍ فَطَبَقَةٌ يَعْبُدُونَهُ رَغْبَةً إِلَى ثَوَابِهِ فَتِلْكَ عِبَادَةُ الْحُرَصَاءِ وَ هُوَ الطَّمَعُ وَ آخَرُونَ يَعْبُدُونَهُ خَوْفاً مِنَ النَّارِ فَتِلْكَ عِبَادَةُ الْعَبِيدِ وَ هِيَ الرَّهْبَةُ وَ لَكِنِّي أَعْبُدُهُ حُبّاً لَهُ فَتِلْكَ عِبَادَةُ الْكِرَامِ وَ هُوَ الْأَمْنُ لِقَوْلِهِ تَعَالَى‏ وَ هُمْ مِنْ فَزَعٍ يَوْمَئِذٍ آمِنُونَ‏.'

" قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَ يَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ‏...." فَمَنْ أَحَبَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ أَحَبَّهُ اللَّهُ وَ مَنْ أَحَبَّهُ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ كَانَ مِنَ الْآمِنِينَ‏."

Ya zo cikin Ilalul-Shara'i'i na Sanaaniyyu daga Muhammad Bn Haruna, daga Ubaidullahi Bn Musa Al-Habbali, daga Muhammad Bn Hussaini Al-Kasshaabi, daga Muhammad Bn Hassan, daga Yunusa Bn Zabyaan yace: Sadiq (A.S) yace:

" LALLE MUTANE NA BAUTAWA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NE TA FUSKA UKU . 

(1)-/WANI YANKIN NA BAUTA MASA NE SABODA KWADAYIN SAMUN LADA, TO, WANNAN ITA CE IBADAR MASU KWADAYI, SUNE KWADAYAYYU.

(2)- WASU NA DABAN KUMA SUNA BAUTA MASA NE SABODA TSORON WUTA, TO, WANNAN ITA CE IBADAR MAI BAUTA, KUMA ITA CE TSORO.

(3)- AMMA NI INA BAUTA MASA NE (kawai) DON INA SONSA, WANNAN ITA CE IBADAR MASU KARAMCI, KUMA SHINE AMINCI SABODA FADINSA (T):

" ....... KUMA SU GAME DA FIRGICIN WANNAN RANA AMINTATTU NE."

" KACE: " IDAN KUN KASANCE KUNA SON ALLAH, TO, KU BI NI SAI ALLAH YA SO KU KUMA YA GAFARTA MUKU ZUNUBANKU......"

DUK WANDA KE SON ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA ALLAH ZAI SO SHI, KUMA WANDA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA SO SHI YA KASANCE CIKIN AMINTATTU."

علل الشرائع ج 1 ص 12.

Kowa ya san da wanda zaiyi biyayya ga wani saboda yana kwadayin abin hannunsa da wanda zai yi masa biyayya saboda tsoron azabarsa da kuma wanda zai yi masa biyayya kawai don yana sonsa ne ba don kwadayin abin hannunsa ko tsoronsa ba, to, mai yin biyayyar nan kawai don soyayya zai fi girman matsayi da mutunci wajen wannan mutumi.

TA YAYA ZA KA SAN MATSAYINKA WAJEN UBANGIJINKA ?

Yana da kyau da kuma fa'ida ga kowanne mutum yasan matsayinsa wajen Ubangijinsa tun daga nan duniya, ko kuma nace tun daga yanzu kafin lokaci ya qure masa.

 قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع‏ مَنْ أَرَادَ مِنْكُمْ أَنْ يَعْلَمَ كَيْفَ مَنْزِلَتُهُ عِنْدَ 

اللَّهِ فَلْيَنْظُرْ كَيْفَ مَنْزِلَةُ اللَّهِ مِنْهُ عِنْدَ الذُّنُوبِ كَذَلِكَ مَنْزِلَتُهُ عِنْدَ اللَّهِ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى‏."

Amirul-Muminina Imam Ali (A.S) na cewa:

" DUK WANDA KE SO DAGA CIKINKU YASAN YAYA MATSAYINSA YAKE A WAJEN ALLAH, TO, YA DUBA YAYA MATSAYIN ALLAH YAKE A WAJENSA YAYIN DA YA TASHI AIKATA WANI ZUNUBI. TO, KAMAR HAKANE MATSAYINSA YAKE WAJEN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA."

الخصال ج 2 ص 15.

Idan ya zama ba ka tuna Allah da kuma jin tsoronsa yayin da kake aikata abinda ya hane ka aikatawa, to, ka sani kai ba komai bane a wajensa fiye da yadda kaima ka dauke shi ba komai bane a wajenka yayin daka tashi aikata abinda ya hane ka.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      (08137925034)

4th January, 2022/ 30th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post