Hikimomin Yau Da Gobe (1)


 Abbagano✍️

• Koda matar ka tana da dabi'un da baka so... To godiya da yabo suna iya sanya ta ,ta canza

• Ka nisanci mutanen da suke kokarin kashe maka gwuiwa.. Domin manyan mutane kullum kokarinsu shine su nuna maka kaima wata rana zaka zama babba

• Duk lokacin da ka lura cewa an gaji dakai, gara ka tattara kayan ka , ka fice tunda sauran mutumcin ka.

• Bai kamata kayi rayuwar bakin ciki ba Saboda mutumin da yake rayuwarshi cikin walwala bai damu dakai ba

• Wanda yake son ka a halin tsanani da walwala, ba tare da yana jiran wani abu daga gareka ba.

Sannan yake Hakuri dakai a halin fushi da farin cikin ka, ba tare da ya boye wani mummuna ba a ranshi

To shine aboki na hakika.

• Da kasan gaggawar da mutane zasuyi wurin mantaka bayan mutuwa.. Da bazakai kokarin neman yardar kowa ba sai Allah

• Mafi yawan damuwa tana faruwa ne saboda dogon tunani akan ta, domin dogon tunani yana kirkiro har matsalolin da babu su.

• Kada ka yaudari kanka... Idan har ka gano wani aibu a tare dakai to kayi kokarin gyarawa.. Domin dukkan mutane muna da aibu...saidai wanda yafi kowa hikima shine wanda ya fisu kokarin gyarawa.

Gaskiyar lamari :

Mafi yawan damuwa mune ke jawo ma kanmu shi misalin :

1- Mutanen da basa sonmu amma muna bibiyarsu

2- Tunanin da yake takura mu, amma muna bijiro dashi

3- Labaran da suke cutar damu amma muke sauraronsu.

4- Maudu'an da suke kuntata mana amma muke tattauna su.

Ka kirkirarwa kanka yanayi mai kyau...ka kauracewa abunda zai cutar dakai.

√ Rashin masoyanmu daidai yake da rashin launi a jikin hoto... Shidai bai rabamu da rayuwa ba, amma ya rabamu da jin dadin rayuwa.

√ Ka lura da kanka sanda kake cikin fushi , domin ka gane dabi'unka.

Ka lura da mu'amalarka da wanda ya cuta maka, domin kasan cigaban ka.

Ka lura da tattaunawarka da wanda ya saba maka a ra'ayi domin ka gane zurfin fahimtarka da tunaninka

Bai zamo dole sai ka fadi duk abinda ka sani ba.

amma kayi kokarin aikata abinda ka sani, gwargwadon iyawar ka.

√ Wasu suna gasgata karya idan tazo daga masoyansu...wasu kuma suna karyata gaskiya idan tazo daga makiyansu

√ Babu wata matar da take kwace mijin wata...saidai akwai matar data watsar da mijinta shikuma ya tafi neman farin cikinsa wurin wata

√ wanda yake son fure dole ya girmama Qayar shi... Ka saurari wanda ya saba maka a ra'ayi da kyau domin ka amfana. Domin wanda yake ce maka ((Eh)) a koda yaushe bazai karama tunaninka zurfi ba

√ Kada ka rusa gadar daka biyo ta samanta...la'alla wata rana zaka bukaci dawowa

√ Yawan sauraron karya zai iya sanya mutum ya gasgata ta...kuma tayi mashi tasiri sosai

√ Kada kayi kokarin sai kayi nasara a kowace jayayya...wani lokacin samun zukata yafi samun nasara.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post