🍂🦋____ kowa yasan cewa anayin aure ne don koyi da sunnar manzon tsira (SAW), kuma dan bautawa mahalicci, sannan da shi ne ake fatar samun karuwar al'umma ta gari.
Abin takaici ne ko ince bakin ciki yadda amare da angwayen yanzu suka canza yanayi na hidimar aure daga mai wahala ( kowa yasan kafin ayi aure hidimar sai kowane bangare sun ji a jikinsu, sannan ina magana akan yadda mafiya rinjayen al'ummar mu sune masu rufin asiri ne ba masu kudi ba) zuwa mafi tsananin wahala, ta hanyar kawo wasu ababen da ba wajibi bane a cikin auren, sannan ba abinda zasu karawa auren saima dai ragewa.
🦋🍂____ A da idan za ayi bikin yarinya to anyi kokarin tsiya ayi Ihsani a islamiyyarsu, daga shi sai daurin aure da walima, cikin sauki da rashin wahalar da juna, amma yanzu karya na driving mutane sunajin cewan dole sai anyi tarin events kafin a daura aure, wanda wannan events din ba abinda suke karawa aure, wallahi saidai daukan zunubi, saboda duk yanda kuka nuna a bikinku zaku kiyaye indai kun tarki kauyewa, Arebian night, kwallo, bridal shower, da duk wani shagali da zaya hada maza da mata to wallahil azeem sai an sabi Allah a cikinsa.
Ga karin takaicin cewan su wa'yannan events din da wahalan gaske kaga wurin da za ayisu ya zama cikin gari, dole sai anyi nisa da gari, inda ba wanda yasan me ake shukawa sai Allah, na farko kun wahalar da masu kashe kudi suje sanna kun hada maza da mata ta yadda daukan zunubi baya wahala a wurin, sannan ku kanku kun kashe kudi wurin ganin kun kama wurin da kuma kayatar dashi.
🍂🦋____ Duk events din akeyi a yanzu masu kudi ne suka fara kawo mana shi, sune dama can basu dauki aikata irin hakan bakin komi ba, zakaga a event daya an kashe kudin da wallahil azeem sai a aurar da wata diyar talakan cikin yanayi na rufin asiri, amma sune za'a saka a event, kuma idan har so ake dole ya kayatar to sai an kashe kudi da yawa, idan ba haka ba kuwa ko Kunyi to bazaya baku abinda kuke soba ( ma'ana bazaya kai na wanda Suka zubar da kudade agunba).
Karin abin takaici zakaga anyi events a biki ayi kadan anyi hudu, sannan kowane kudin da aka kashe basu ya kamata ace an kashe b ( ina nufin ya kamata kudin sufi haka, amma saboda yanayin rayuwa ba'ayi hakan ba) kuma a karshe sai kaga ankai yarinya gidanta kaga Ashe bai ida gininsa ba, ko akwai wani abu da bai karasa ba, yanzu tsakani da Allah meye abu mafi muhimmanci da kammala gida da duk abinda yake wajibi gareka, da kuma wannan events din wanda ba abinda suke karawa aure sai zunubi?.
🦋🍂____ shawara ta gareku amare da angwaye, karku biyewa makaryata, domin su sun rigada sun tara, kaiko dan gidan malam shehu gini kadai aka barma saika jigata, ku ragewa kanku nauyin yin events kudin kuyi abinda ya kamata dashi, zaku ragewa kanku zunubin da ake dauka a wurin, sannan zaku rage ayyukan auren wanda dama sune ya kamata kuyi, karya a cikin aure baida wani alfanu saima wahala da zaku bama kanku ku bama mutane, hausawa na cewa daidai girman kurji daidai ruwan cikinsa, haka in bakida gashin wance kar kiyi irin kitson wance.
Komi zamuyi mu rika duba yanayi na rayuwa da kuma hakkin Allah a kanmu, Allah ya bawa ma'auta da masu shirin yi zaman lafiya da zuri'a ta gari ya karesu daga dukkan sharri, masu niyya kuma Allah ya hada kowa da abokin zama na gari.
🦋✍️____ Zarah A Zamsarf 🥀✨