Ganawar Jagora (H) da mutanen Anyigba da Bidda


 Daga Sayyid Zakzaky Office

Ranar Talata 15 ga Jimadal-Thani, 1443 (18/01/2022) Jagoran Harkar Musulunci, Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da wakilai daga al’ummar garin Anyigba ta jihar Kogi, tare da Malamin addinin Musulunci Shaikh Muhammad Bello daga garin Bidda ta jihar Neja, a gidansa da ke Abuja.

Maziyartan sun hada da Alh. Muhammad Abdullahi, wanda yake sarki ne a al’ummar Igala, da kuma babban Malamin Darikar Tijjaniyya, wanda ya fahimci Mazhabar Ahlulbait (AS) ya kuma amsa da’awar Shaikh Zakzaky (H) na kira zuwa ga komawa tafarkin Allah, Shaikh Muhammad Ibn Muhammad daga garin Bidda, da sauran mutane daban-daban daga yankunan guda biyu.

Da yake Jawabi ga maziyartar, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara ne da yin tsokaci kan maganar da mai gabatarwa ya yi na cewa Shaikh Muhammad yace ya bar darikar Tijjaniya ya koma Shi’a. Sai Jagora (H) ya nuna musu cewa ba dole ne sai mutum ya bar Darika ba sannan ya zama Shi’a, ana iya hada duk biyun in an so, saboda daya Mazhaba ce, dayan kuma matafiyar Irfani ko Tasawwuf ce.

Jagara (H) yace: “Ai ba bukatar sai ya bar Tijjaniyya (kafin ya zama Shi’a). Mazhabar Malikiyya ne mutum zai bari sannan ya zama (mai bin Mazahabar) Jafariyya (Shi’a), amma yana iya yin Tijjaniyya.”

Shaikh Zakzaky ya kara da cewa: “Idan mutum Shi’a ne, zai iya yin Qadiriyya zai iya yin Tijjaniyya, kuma yana Shi’arsa. Amma Mazhaba akwai ta Jafariyya (ba zai yi Malikiyya ba). 

Ya kara da cewa: “Akwai bangarorin karatu a addinin nan guda uku muhimmai; na daya muna ce masa Tauhidi, wanda yake magana kan abubuwan da ya zama dole mutum ya yi imani da su, duk abin da za ka yi I’itikadinsa a zuciya shi yake magana a kai. Wato yana magana dangane da Allah, da Manzo da Annabta da ranar Lahira, duk abin da zai zama dole ka yi I’itikadinsu ka yarda da su, shi Tauhidi ke magana a kai. Wannan kamar yadda ake da Mazhaba a bangaren Fikihu, ana da abin da ake kira Firqa a bangaren Tauhidi, ko a bangaren Ahlussunnah akwai Ash’ariyya akwai Maturidiyya da sauransu, duk suna magana kan Aqa’id ne.

“Abu na biyu shine Mazhaba, wanda shi kuma yana magana dangane da Hukunce-hukunce ne, yadda za a yi ibada da mu’amaloli. Ibadodi sun hada da irin su sallah, azumi, zakka, hajji. Mu’amaloli kuma akwai aure, rabon gado, ciniki da ire-irensu. Mene ne wajibi, mene ne haramun, mene ne mustahabi, mene ne makaruhi, to shine abin da Fiqihu yake koyarwa. To a wannan ne ake samun Mazhabobi. Shine aka samu a tsakanin Ahlussunnah akwai Malikiyya, Shafi’iyya, Hanafiyya da Hambaliyya, wadannan ne fitattun mazhabobi guda hudu, amma akwai wasu (kari), wadannan kawai sun shahara ne. Haka nan kuma aka samu (Mazhabar) Jafariyya a bangaren Shi’a.

“To kuma akwai abin da ake cema Tasawwuf ko Irfani (wasu na cewa Tasawwuf, wasu na cewa Irfani), wannan yana koyar da kai wani irin tafiya ne na ruhi tsakaninka da Ubangijinka, ta nan aka samu Dariqu na sufaye. To, su sha’anin Irfani ya keta tsakanin Mazhaba, ba Mazhaba bane, za ka ga ma’abota Irfani din ko na ina ne, ko a wane Mazhaba suke, ko Shi’a suke, ko Sunnah, za ka ga suna da alaka da juna…

“Saboda haka mu fahimtarmu Irfani ko Tasawwuf, ko ma me kace masa, shine abin da ya shafi Darika, bashi da dangantaka da Mazhaba. Saboda haka idan mutum Batijjane ne, sai ya fahimci Mazhabar Ahlulbaiti (AS) ba yana nufin ya tashi a Tijjaniyya bane. Ballantana ma duk Darikokin nan da kake gani, kowanne sai ka ga sun ce asalinsu daga Amirulmuminin (AS) ne, kowanne sai ka ga yana da sila da Amirulmuminin da iyalan gidan Annabi (S). Kaga Shehu Abdulkadir Jilani jikan Imam Husaini (AS) ne, ka ga Shehu Ahmadu Tijjani kuma jikan Hasan (AS). 

“To kuma muna ganin cewa inda ma mutum zai bi diddigi sosai sosai ya binciko wace Mazhaba shi shehu Ahmadu Tijjani ke bi, zai ga cewa yana bin Mazhabar Ahlulbaiti (AS) ne, ko da mutane ba su sani ba, tunda Malikiyyar ta riga ta zama ita ce ta shahara a tsakan-kanin nan.” Inji Jagora (H).

Da yake bayani dangane da dalilin cigaba da zamansu ba tare da sun fita neman magani ba, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Mun dauka daga fitowarmu za mu yi waje ne mu samu kulawar likita, da muka zo muna sa rai kamar makon farko ma za mu tafi, aka nuna mana muna fitowa ma za a ba da ‘passport’ ba wani matsala, amma muka fito shiru, mako daya, mako biyu, uku, mako hudu, fasfo ya fito shiru, ya fito gobe shiru har yau, gashi yau watanmu shida amma har yau shiru.”

Ya ci gaba da cewa: “Kun ji a makon da ya wuce mun kai masu ba da fasfo din kara kotu, don ba dalilin da ya sa ba za su ba da ‘passport’ din ba.” Yace: “Don wancan karon da muka je India wajen neman maganin da suka je suka hana, su suka yi mana ‘passport’ din ba mun je ma ofishinsu bane, tunda duk bayanan da ke jikin ‘passport’ din yana nan a cikin kwakwalwar ‘computer’ dinsu, sun tsamo shi ne kawai suka bamu ba tare da mun je wajen ba. Ko yanzu ma za su iya tsamowa, ba wani dalili da ba za su yi ba.”

Ya kara da cewa: “In sun ce wanda ake da shi ya bace a hannunsu, to tsamo da wani ne za su yi, ba bukatar ma sai mun je ofishinsu, su fito mana da ‘passport’ ne kawai sababbi in wancan ya bace. To (amma), an bi duk matakan da ake dauka na nuna musu cewa wancan ya bace ga kuma dalilai da sauransu, amma kuma dai sun ki su bayar.”

Yace: “Har ma na san wani dan jarida yake tambayata wai ina tsammanin zan samu adalci a kotun nan kuwa? Nace ai dama ko bamu samu ba muna son ‘case’ dinmu ya zama an sani ne, an ga hujjojinmu, ala bashi ko sun ki dai, an san muna da hakki wanda aka hana mu.”

Da yake amsa bayanan da daya daga maziyartar ya gabatar, Jagora (H) ya karfafi bukatar samar da hanyoyin tarjama bayanan da ake yi da Hausa zuwa yarurruka daban-daban na al’umma don isar musu da sakon Harkar. Inda yace “Bai kamata yare ya zama abin da ke kawo ‘barrier’ (katanga a tsakani) ba.”

Ya kuma karfafe su da su cigaba da gudanar da ayyukansu a karkashin Da’irarsu da kuma dandamalolin da ake da su a Harka. “Baya ga abin da muke ce masa Da’ira wanda yake ko wane gari akwai shi, akwai kuma abin da muke ce ma Forum daban-daban muna da su, wanda su kuma suna la’akari da bukatun wurare daban-daban ne, kamar misali akwai Academic Forum, su in sun hadu da Ingilshi suke magana tunda su ‘Academicians’ ne, yarensu kenan, in suka hadu da shi suke magana, haka nan kuma akwai Fora daban-daban.

“Ku yanzu ‘already’ dama kuna da Da’irarku ko? To masha Allah, za ku (rika gudanar da abubuwa) karkashin Da’irarku, sannan kuma har ila yau za ku iya yin (wasu abubuwan) kuma karkashin Fora da ake da su, kamar Academic din, ‘Academicians’ amma za su yi na Academic Forum ne, ga ‘intellectuals’ nan a cikinku. Sai kuma sauran mutane gaba daya za ku iya yi karkashin Da’irarku, ko wane irin aiki ne.” Inji Jagora.

Yace: “To kuma yanzu in da wasu matsalolin da suka faru lokacin da ba mu nan, ina jin wadannan sun kau yanzu Insha Allahu. Ba lokacin kuma da za ku je ne ku kai kararku a yi muku gum da baki a yi shiru ba, yanzun kam insha Allahu idan kuna da ‘project’ ko kuna ganin ga abin da ku ya fi shafa, in kuka fada insha Allahu za a baku dama ku yi abinku Insha Allah.”

A karshe, Jagora (H) ya yi kasheji ga azzalumai kan cigaba da kulle-kullensu ga Harkar Musulunci. “Na sha fada musu cewa, in kuka saka bindiga (a kanmu) za ku tambatsa abin ne, domin wannan al’amari ba da bindiga aka yi shi ba, kuma bindiga ba za ta kawar da shi ba. Ka san abin da aka yi shi da karfi shine ake kawar da shi da karfi. To abin da yake na hankali, ba yadda za a yi ka kawar da imani da karfin tsiya. Ba yadda za a yi ka sa bakin bindiga ka harbe gaskiya ta mutu murus a neme ta a rasa. Ba zai yiwu ba, saboda dama ba bindiga ne ya kawo gaskiya ba, gaskiya asasinta daban ne, kuma gaskiyar ba biyu bace ballantana su fito da wata daban.”

Shaikh Zakzaky yace: “Yanzu ma sun fara daukan matakai na kurdawa da karairayi daban-daban. Nace oho dai kowanne ne ma za ku yi ku yi ta ta yi, don Shaidan fa baya mika wuya, kullum ya dinga kenan, yana ganin kamar zai yi nasara ne. shi yasa Allah Ta’ala yake cewa: “Ku yaqi mabiya shaidan don kullin shaidan rarrauna ne.” Shi kullum (Shaidan) yana amfani da salo guda daya, bai taba nasara ba, amma bai taba fasawa ba.”






@SZakzakyOffice

19/01/2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post