Falalolin Ahlul-Bayt (A.S) cikin Qur'ani da Sunnah


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DUK WANDA YACE MAKA AKWAI WADANDA SUKA FI AHLUL-BAIT MATSAYI KACE MASA MAQARYACI NE

Sakamakon qiyayyar da wadanda suka karbi muslimci bisa tilas (KARHAN) don gudun qasqancin duniya yasa suka qirqiro wadansu maganganunsu na qarya wadanda ke nuna cewa akwai wasu masu daraja cikin Sahabbai wadanda suka fi iyalan Annabi (S.A.W.W) daraja, kuma sun qirqiro wadannan hadisai ne don su bushe hasken gidan Annabi (S.A.W.W), sai dai kuma Allah ya qi sai ya cika haskenSa.

Saboda haka yanzu insha Allahu za mu kawo kadan daga cikin ayoyi da hadisan da su kayi magana kan falalar Ahlul-Bait (A.S) wadanda suka fi na kowa cikin Qur'ani da sunnah (Hadith). Ga su kamar haka;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

       AYAR MUBAHALA

An sami wasu daga cikin Nasaran Najran masu qarya magana Isah (A.S) da kuma Annabi Muhammad (S.A.W.W) da yazo a matsayin Annabin qarshe, shine Allah (S.W.A) yake ce masa;

(1)- فَمَنۡ حَآجَّكَ فِيهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ فَقُلۡ تَعَالَوۡاْ نَدۡعُ أَبۡنَآءَنَا وَأَبۡنَآءَكُمۡ وَنِسَآءَنَا وَنِسَآءَكُمۡ وَأَنفُسَنَا وَأَنفُسَكُمۡ ثُمَّ نَبۡتَهِلۡ فَنَجۡعَل لَّعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَى ٱلۡكَٰذِبِينَ (١٦)

" DUK WANDA YAYI MAKA JAYAYYA CIKINSA BAYAN ABINDA YAZO MAKA NA DAGA ILIMI, KACE; " KU ZO MU KIRAYI 'YA'YAYENMU DA 'YA'YAYENKU DA MATANMU DA MATANKU DA KAWUKANMU DA KAWUKANKU, SA'AN NAN MUNYI QANQAN DA KAI MU SANYA LA'ANAR ALLAH TA TABBATA KAN MAQARYACI (tsakanina daku)."

(Al-Imraan:61)

To, wannan al'amari ya faru ne a Madinah yayin da Annabi (S.A.W.W) ke da mata da kuma yawan Sahabbai, amma da shike shine mai fassara ayar Qur'ani a aikace sai ya bayyana matan da yake nufi da 'ya'ya da kuma kawukan nasu kamar yadda yazo cikin riwayar dake biye;

وقال أبو بكر بن مردويه حدثنا سليمان بن أحمد حدثنا أحمد بن داود المكي حدثنا بشر بن مهران حدثنا محمد بن دينار عن داود بن أبي هند عن الشعبي عن جابر قال قدم على النبي صلى الله عليه وسلم العاقب والطيب فدعاهما إلى الملاعنة فواعداه على أن يلاعناه الغداة قال فغدا رسول الله صلى الله عليه وسلم فأخذ بيد علي وفاطمة والحسن الحسين ثم أرسل إليهما فأبيا أن يجيبا وأقرا له بالخراج قال فقال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم والذي بعثني بالحق لو قاللا لأمطر عليهم الوادي نارا

Abubakar Bn Mardawaihi yace: Sulaiman Bn Ahmad ya bamu labari, Ahmad Bn Dawud Al-Makiy ya bamu labari, Bashar Bn Mihran ya bamu labari, Muhammad Bn Dinaar ya bamu labari daga Dawud Bn Abiy Hindu, daga Sha'abiy, daga Jabir yace: " Aqeeb da 'Dayyib sunzo wajen Manzon Allah (S.A.W.W) (suna qalubalantarsa), sai ya kiraye su zuwa ga yin Mubahala (tsineneniya). Sai su kayi masa alqawarin cewa washe gari za suyi wannan tsinuwa dashi. Yace: " Sai Manzon Allah (S.A.W.W) ya wayi gari yana riqe da hannun Aliyu da Fadimatu da Hassan da Hussaini (A.S), sannan ya aika zuwa gare su, sai suka qi su amsa (saboda ganin wadannan tsarkakan fuskoki). Sai suka nuna qinsu da fitowa. Yace: Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace:

" NA RANTSE DA WANDA YA AIKO NI DA GASKIYA ! DA ACE SUN FADE TA (sun yarda anyi wannan tsineneniyar) DA KUWA ANYI MUSU RUWAN DUWATSU NA WUTA !"

قال جابر وفيهم نزلت « تعالوا ندع أبناءنا وأبناءكم ونساءنا ونساءكم وأنفسنا وأنفسكم » 

قال جابر « أنفسنا وأنفسكم » رسول الله صلى الله عليه وسلم وعلي بن أبي طالب « وأبناءنا » الحسن والحسين « ونساءنا » فاطمة وهكذا رواه الحاكم في مستدركه « 2/593 594 »

Jabir yace: " A kansu aka saukar { KUZO MU KIRAYI 'YA'YAYENMU DA 'YA'YAYENKU DA MATAYENMU DA MATAYENKU DA KAWUKANMU DA KAWUKANKU."

Jabir yace: " KAWUKANMU DA KAWUKANKU " Manzon Allah (S.A.W.W) ne da Aliyu Bn Abiy 'Dalib, " DA 'YA'YAYENMU DA 'YA'YAYENKU " kuma Hassan ne da Hussaini, " DA KUMA MATAMMU " Fadimatu (S.A) ce."

Kamar haka Hakeem ya fitar cikin Mustadrak nasa, J:2, Sh:593/594)

Kenan Annabi (S.A.W.W) da Ali sune tsarkakakkun mazajen waccan lokaci, kuma Fadimatu ita ce mafificiyar mata wacce ta tsaya a madadinsu, sannan Hassan da Hussaini (A.S) a matsayin tsarkakakkun 'ya'ya cikin 'ya'yayen al'ummar kakansu (S.A.W.W).

          AYAR TSARKAKA

(2)- .......إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُذۡهِبَ عَنكُمُ ٱلرِّجۡسَ أَهۡلَ ٱلۡبَيۡتِ وَيُطَهِّرَكُمۡ تَطۡهِيرٗا (٣٣)

" ABIN SANI (kawai) ALLAH NA NUFIN YA TAFIYAR MUKU DA QAZAMTA NE IYALAN GIDA KUMA YA TSARKAKEKU TSARKAKEWA."

          (Ahzaab:33)

قال ابن جرير حدثنا ابن حميد حدثنا عبد الله بن عبد القدوس عن الأعمش عن حكيم ابن سعد قال ذكرنا علي بن أبي طالب رضي الله عنه عند أم سلمة رضي الله عنها فقالت في بيتي نزلت « إنما يريد الله ليذهب عنكم الرجس أهل البيت ويطهركم تطهيرا » قالت أم سلمة جاء رسول الله صلى الله عليه وسلم إلى بيتي فقال لاتأذني لأحد فجاءت فاطمة رضي الله عنها فلم أستطع أن أحجبها عن أبيها ثم جاء الحسن رضي الله عنه فلم أستطع أن أمنعه أن يدخل على جده وأمه ثم جاء الحسين فلم أستطع أن أحجبه عن جده صلى الله عليه وآله وسلم وأمه رضي الله عنها ثم جاء علي رضي الله عنه فلم أستطع أن أحجبه فاجتمعوا فجللهم رسول الله صلى الله عليه وسلم بكساء كان عليه ثم قال هؤلاء أهل بيتي فأذهب عنهم الرجس وطهرهم تطهيرا فنزلت هذه الآية حين اجتمعوا على البساط قالت فقلت يا رسول الله وأنا قالت فو الله ما أنعم وقال إنك إلى خير.

Ibn Jarir ('Dabari) yace: Ibn Humaid ya bamu labari, Abdullahi Bn Abdul-Quddus ya bamu labari daga A'amashu daga Hakeem Ibn Sa'ad yace: " An ambaci Aliyu Bn Abiy 'Dalib (R.A) a wajen Ummus-Salamata (R.A) sai tace: " A cikin gidana aka saukar;

" ABIN SANI ALLAH NA NUFIN YA TAFIYAR DA QAZANTA NE DAGA GARE KU IYALAN GIDA, KUMA YA TSARKAKEKU TSARKAKEWA." Ummus-Salamata tace:

" Manzon Allah (S.A.W.W) ya zo gidana sai yace;

" KADA KI YIWA WANI IZNIN SHIGOWA."

Sai Fadimatu (R.A) tazo, ni kuma ba zan iya hanata shiga ga mahaifinta ba, sa'an nan Hassan (R.A) yazo, ni kuma ba zan iya hana shi shiga zuwa ga kakansa da mahaifiyarsa ba, sa'an nan Hussaini (R.A) yazo, ni kuma ba zan iya shiga tsakaninsa da kakansa (S.A.W.W) da mahaifiyarsa (R.A) ba. Sa'an nan Aliyu (R.A) yazo, ni kuwa ba zan iya shiga tsakaninsa. Sai suka hadu, sai Manzon Allah (S.A.W.W) ya lullube su da mayafin da yake kansa, sa'an nan yace:

" WADANNAN SUNE IYALAN GIDANA, KA TAFIYAR MUSU DA QAZANTA KUMA KA TSARKAKESU TSARKAKEWA."

Sai wannan aya ta sauka yayin da suka taru akan shimfida. Tace: " Sai nace yaa Ma'aikin Allah, har dani (cikin wannan tsarkakar?) Yace:

" WALLAHI BAN AMINCE BA ! KE DAI KINA KAN NAKI ALKHAIRIN (amma na cikin wannan tsarkakar ba)."

Sa'an nan an sami wata riwayar daga ita Ummus-Salamata wacce tazo cikin Musnad na Imamu Ahmad Bn Hambal, hadisi mai lamba 25,910, sai dai dan bambancin lafazi.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

25910- حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ نُمَيْرٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا عَبْدُ الْمَلِكِ يَعْنِي ابْنَ أَبِي سُلَيْمَانَ ، عَنْ عَطَاءِ بْنِ أَبِي رَبَاحٍ ، قَالَ : حَدَّثَنِي مَنْ سَمِعَ أُمَّ سَلَمَةَ , تَذْكُرُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ فِي بَيْتِهَا ، فَأَتَتْهُ فَاطِمَةُ بِبُرْمَةٍ ، فِيهَا خَزِيرَةٌ ، فَدَخَلَتْ بِهَا عَلَيْهِ ، فَقَالَ لَهَا : " ادْعِي زَوْجَكِ وَابْنَيْكِ " , قَالَتْ : فَجَاءَ عَلِيٌّ , وَالْحُسَيْنُ , وَالْحَسَنُ ، فَدَخَلُوا عَلَيْهِ ، فَجَلَسُوا يَأْكُلُونَ مِنْ تِلْكَ الْخَزِيرَةِ ، وَهُوَ عَلَى مَنَامَةٍ لَهُ عَلَى دُكَّانٍ تَحْتَهُ كِسَاءٌ لَهُ خَيْبَرِيٌّ , قَالَتْ : وَأَنَا أُصَلِّي فِي الْحُجْرَةِ ، فَأَنْزَلَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ هَذِهِ الْآيَةَ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا سورة الأحزاب آية 33 , قَالَتْ : فَأَخَذَ فَضْلَ الْكِسَاءِ ، فَغَشَّاهُمْ بِهِ ، ثُمَّ أَخْرَجَ يَدَهُ ، فَأَلْوَى بِهَا إِلَى السَّمَاءِ ، ثُمَّ قَالَ : " اللَّهُمَّ هَؤُلَاءِ أَهْلُ بَيْتِي وَخَاصَّتِي ، فَأَذْهِبْ عَنْهُمْ الرِّجْسَ ، وَطَهِّرْهُمْ تَطْهِيرًا , اللَّهُمَّ هَؤُلَاءِ أَهْلُ بَيْتِي وَخَاصَّتِي ، فَأَذْهِبْ عَنْهُمْ الرِّجْسَ ، وَطَهِّرْهُمْ تَطْهِيرًا " , قَالَتْ : فَأَدْخَلْتُ رَأْسِي الْبَيْتَ ، فَقُلْتُ : وَأَنَا مَعَكُمْ يَا رَسُولَ اللَّهِ ، قَالَ : " إِنَّكِ إِلَى خَيْرٍ ، إِنَّكِ إِلَى خَيْرٍ " , قَالَ عَبْدُ الْمَلِكِ : وَحَدَّثَنِي أَبُو لَيْلَى ، عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ ، مِثْلَ حَدِيثِ عَطَاءٍ سَوَاءً , قَالَ عَبْدُ الْمَلِكِ : وَحَدَّثَنِي دَاوُدُ بْنُ أَبِي عَوْفٍ أَبُو الْحَجَّافِ ، عَنْ شَهْرِ بْنِ حَوْشَبٍ ، عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ بِمِثْلِهِ سَوَاءً .

................" YAA UBANGIJI WADANNAN SUNE IYALAN GIDANA KUMA KEBANTATTUNA ! KA TAFIYAR MUSU DA QAZANTA KUMA KA TSARKAKESU TSARKAKEWA. "

Tace: " Sai na shigar da kaina cikin dakin, sai nace: Nima ina tare daku (cikin wannan tsarkin) yaa Ma'aikin Allah? " Yace:

" KE DAI KINA KAN ALKHAIRI ! KE DAI KINA KAN ALKHAIRI (amma ba cikin wannan tsarkakar tamu ba) ."

(Musnad Ahmad, hadisi mai lamba 25,910.)

Kunga anan ita da kanta ta tabbar da cewa basu cikin Ahlin Annabi (S.A.W.W) wadanda aka tsarkake.

    AYAR KUSANTAKA

(3) ......قُل لَّآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ أَجۡرًا إِلَّا ٱلۡمَوَدَّةَ فِي ٱلۡقُرۡبَىٰۗ وَمَن يَقۡتَرِفۡ حَسَنَةٗ نَّزِدۡ لَهُۥ فِيهَا حُسۡنًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ شَكُورٌ (٣٢)

" KACE: BANI TAMBAYARKU WANI LADA (cikin saqon da nazo muku dashi na alkhairi) SAI DA (ku nuna) QAUNARKU CIKIN MAKUSANTANA."

  (Suratul-Shurah:23)

وقال ابن أبي حاتم حدثنا علي بن الحسين حدثنا رجل سماه حدثنا حسين الأشقر عن قيس عن الأعمش عن سعيد بن جبير عن ابن عباس رضي الله عنه قال لما نزلت هذه الآية « قل لا أسألكم عليه أجرا إلا المودة في القربى » قالوا يا رسول الله من هؤلاء الذين أمر الله بمودتهم قال فاطمة وولدها عليهم السلام

Ibn Abiy Hateem yace: Aliyu Bn Hussaini ya bamu labari, wani mutum ya bamu labari, Hussainil-Ash'qari ya bamu labari daga Qais daga A'amashu daga Sa'eed Bn Jubair, daga Ibn Abbas (R.A) yace: " Yayin da aka saukar da wannan aya; " KACE ! " BANI TAMBAYARKU WANI LADA FACE SOYAYYA CIKIN MAKUSANTA." Suka ce:

" Yaa Ma'aikin Allah ! Wadanne mutanene wadannan wadanda Allah ke umartarmu da mu so su ?" Yace:

" FADIMATU DA 'YA'YAYENTA AMINCI YA TABBATA A GARE SU."

(4)- إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ سَيَجۡعَلُ لَهُمُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وُدّٗا( ٦٩)

" LALLE WADANDA SU KAYI IMANI KUMA SUKA AIKATA AIKIN KIRKI, TO, MAI RAHMA ZAI SANYA MUSU SOYAYYA."

(Maryam:96)

Dangane da wannan ayar Manzon Allah (S.A.W.W) yace:

" BA MAI SONKA YAA ALI SAI MUMINI, KUMA BABU MAI QINKA SAI MUNAFUKI."

- Majma'uz-Zawa'id, J:9, Sh:125.

- Kashiful-Ghumma, Sh:42.

(5)- وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ مِنَ ٱلۡمَآءِ بَشَرٗا فَجَعَلَهُۥ نَسَبٗا وَصِهۡرٗاۗ وَكَانَ رَبُّكَ قَدِيرٗا (٤٥)

" KUMA SHINE YA HALICCI MUTUM DAGA RUWA, KUMA YA SANYA SHI NASABA DA SURUKUTA, KUMA UBANGIJINKA YA KASANCE MAI IKO NE (wajen yin dukkan abinda yaga dama)."

(Furqaan:54)

An ruwaito daga Ibn Abbas (R.A) yace: " Na ji Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa:

" ALLAH (T) YA NUNA HASKE GA ADAM (A.S) SAI YACE: " YAA UBANGIJI WANNAN WANNE HASKE NE ? SAI YACE: " WANNAN HASKEN 'YA'YANKA NE MUHAMMADU DA ALIYU , NA HALICCE SU KAFIN KAI DA SHEKARA DUBU HAMSIN (50,000). WANNAN HASKE YA KASANCE A GOSHIN ADAMU (A.S) HAR YA SADU DA HAWWA'U, YA KASANCE YANA ISA ZUWA GA TSATSO TSARKAKKA DA MAHAIFU TSARKAKKA HAR YAZO GA ABDUL-MUDALLIB . AN SANYA WANNAN HASKE A JIKIN ABDUL-MUDALLIB ZUWA KIBIYOYI BIYU, KIBIYA 'DAYA TA MANZANCI, KIBIYA 'DAYA TA WALICCI, SAI KIBIYAR SAQO (manzanci) TA SHIGA GA ABDULLAHI, KUMA KIBIYAR WILAYA TA SHIGA GA ABI 'DALIB. WANNAN SHINE FADIN ALLAH (T) A WANNAN AYA."

Sannan KUMA an riwaito daga Ibn Sirina cewa wannan aya ta sauka NE kan Annabi da Ali Bn Abi 'Dalib, wanda shi ya auri Fadimatu , shine wanda aka halitta daga ruwa kuma aka sanya shi nasaba da surukuta.

(Shi dan'uwa ne na jini kuma siriki)

- Tafsirin Al-Allama Abu Abdullahi Muhammad Bn Ahmad Al-Ansari Al-Qurdabi, ALJAMI'UL-HAKIMUL QUR'AN, J:13, SH:60, (Madaba'ar Al-Zahirah, shekara ta 1357 bayan Hijra.

- Al-Allama Sa'alabi, kamar yadda yazo cikin Al-Umda na Al-Allama Ibn Badri, Sh;151.

(6)- وَٱعۡتَصِمُواْ بِحَبۡلِ ٱللَّهِ جَمِيعٗا وَلَا تَفَرَّقُواْۚ.......(103)

" KUMA KUYI RIQO DA IGIYAR ALLAH GABA 'DAYA KADA KU RARRABA."

(Al-Imraan:103)

Ya zo daga Imam Ja'afarus-Sadiq (A.S) yana cewa:

" MUNE IGIYAR ALLAH."

Za mu taqaita anan insha Allahu saboda gudun tsawaitawa.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

8th January, 2022/ 5th Jimada-Thani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post