Fahimta ta game da bude sabon shafi – Ado Isah Guda


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DA JI KAI-TSAYE SHINE ADDINI DA YANZU BABU WANDA KE KAN ADDININ MANZON ALLAH (S.A.W.W)

Sayyid Zakzaky (H) rahma ce ga wannan al'umma, khass ga 'yan'uwa almajiransa masu yin tamassuki da Ahlul-Bait (A.S). Bai taba zama fitina ga al'umma ba kuma ba zai zama ba har duniya ta tashi.

Kiransa a kullum shine a dawo zuwa ga tsarin Allah a matsayin abinda zai tafiyar da rayuwarta a duniya baki daya, kuma ya zama tsirarmu ranar gobe qiyama.

Har zuwa yau mafi yawan al'umma basu fahinci haqiqanin kiransa da manufarsa ba, shi yasa take dada nutsewa cikin rudani ba tare da sanin mafita ba. A kullum ji kake ana kuka tare da addu'ar Allah ya kawo mafita saboda halin da ake ciki na zalunci da fin qarfi da kuma quncin rayuwa, alhali Allah ya kawo mafita sai dai anqi a bita ne.

'Yan'uwa almajiran Sayyid Zakzaky (H) sun fada cikin jarrabawa mafi girma da muni wacce basu taba ganinta ba kafin wannan lokaci. Wannan jarrabawa kuwa ita ce waqi'ar Zaria wacce ta bayyanar da abubuwa masu yawan da ba za su taba qirguwa ba.

Ta gaskata fadin Sayyid (H) inda yake cewa:

" WANNAN TAFIYA AKWAI MUTUWA CIKINTA, WANDA BAI SHIRYA BA KADA YA SHIGO CIKINMU."

Sannan kuma ta gaskata fadin Allah (S.W.A) inda yake cewa;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ

الٓمٓ (١) أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتۡرَكُوٓاْ أَن يَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا وَهُمۡ لَا يُفۡتَنُونَ( ٢ ) وَلَقَدۡ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡكَٰذِبِينَ (٣)

BISMILLAHIR-RAHMANUR RAHEEM

A.L.M

" ASHE MUTANE SUNYI ZATON A BARSU HAKA (kawai) SUCE: MUNYI IMANA (a baka) " ALHALI BA A JARRABCE SU BA ?

HAQIQA AN JARRABCI WADANDA KE GABANINSU, DOMIN ALLAH YASAN WADANDA SU KAYI GASKIYA (cikin abinda suke yi) KUMA YASAN MAQARYATA (masu yaudarar kansu)."

        (Ankabut, aya 2-3)

Kuma tabbas wannan waqi'a ta fitar da lamarin a sarari, domin an san masu yi da gaskiya kuma an san maqarya.

Sai kuma Allah ya qarfafi masu yi da gaskiya don su qara qaimi da juriya da kuma dakewa da cewa;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

وَلَا تَهِنُواْ وَلَا تَحۡزَنُواْ وَأَنتُمُ ٱلۡأَعۡلَوۡنَ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ (٩٣١)

 إِن يَمۡسَسۡكُمۡ قَرۡحٞ فَقَدۡ مَسَّ ٱلۡقَوۡمَ قَرۡحٞ مِّثۡلُهُۥۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيۡنَ ٱلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَيَتَّخِذَ مِنكُمۡ شُهَدَآءَۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلظَّٰلِمِينَ ( ٠٤١)

" KUMA KADA KUYI RAUNI (don ganin abinda ya faru a kanku) KUMA KADA KUYI BAQIN CIKI (da ganin kun rasa wasu daga cikinku), ALHALI KUNE MADAUKAKA IN DAI KUN KASANCE MUMINAI.

IDAN MA WANI MIKI (wound) NE YA SAME KU (na rasa wani bangare na jikinku) HAQIQA MISALIN IRIN WANNAN MIKI YA SAME JAMA'AR (ko da kuwa baku gani a jikinsu qarara ba), WADANNAN WASU KWANUKA NE MUKE JUJJUYASU TSAKANIN MUTANE DOMIN ALLAH YASAN WADANDA SU KAYI IMANI (na gaskiya) KUMA YA KWASHI SHAHIDAI DAGA CIKINKU (kamar yadda kuka gani don daukaka darajarku), KUMA ALLAH BA YA SON AZZALUMAI !"

(Al-Imraan, aya ta 139-140)

Tabbas wannan waqi'a ta qarawa masu imani imani tare da dakewa kamar yadda kowa ya sani.

Faruwar wannan al'amari da rashin nasarar da jahiliyya tayi sai ta canza salo yadda ta ratsa dukkan wani bangare na harka Islamiyyah don cimma wannan manufar da ba za ta taba cimmawa ba. Abubuwa suka riqa faruwa har Allah mai iko kan komai da kowa yayi dawowar Sayyid (H) cikinmu.

A BUDE SABON SHAFI AYI AIKI TARE

Farkon abinda ya fara yi shine qoqarin dinke barakar dake tsakanin mabiyansa kamar yadda Annabi (S.A.W.W) ya hada kan al'ummarsa ta hanyar cire qiyayya da gaba da kuma rashin fahintar dake tsakaninsu.

Cikin ganawarsa (H) da yayi da wasu wakilai daga 'yan'uwa na yankin Kano ya ambaci cewa:

" MALAM TURI NE YA TURA MALAM KABIRU ALKANAWI ZUWA KANO DA IZNINMU, KUMA MU MUKA TURA MALAM TURI, YANZU KUMA MUKA TURA DR SUNUSI. A TAFI AYI HAQURI DA JUNA A BUDE SABON SHAFI AYI AIKI TARE."

A fahintata wannan jawabi na Sayyid (H) ya dinke bakin kowa ne dayin wani furuci kan wani dan'uwa ko 'yar'uwa da make tunani ko ganin yayi ba daidai ba a baya ko kuma ya gaza cikin aikata wani aiki daya kamata ace yayi. Sannan kuma a qarfafi 'yan'uwa ne da jansu a jiki saboda kowa ya sake jiki ya qara qaimi wajen yiwa wannan harka aiki. Sai kuma naji na gani wasu qoqarinsu shine su fitinar da 'yan'uwa ta hanyar lalle sai su gamsur dasu cewa su wane da wane ba akan daidai suke ba.

A tawa fahintar shine kowa ya kame bakinsa yayi aiki kawai domin Allah. Shi kuwa mai kuskuren matuqar dama yana bin Sayyid (H) da ikhlasi ne zai fahinci kansa a matsayin wanda yayi kuskure a baya, sai ya tuba ga Allah ya nemi gafararSa kuma ya gyara ayyukansa don kada ya maimaita abinda ya faru a baya.

Cutar da addinin Allah na daga cikin abinda ake cewa:

" YIWA KAI ." ba wai cutar da mai yin kira kan addinin Allah bane. Saboda haka da zarar mutum ya fahinci haka sai ya tuba ga Allah ne kuma ya qudiri aniyar ba zai qara maimaita abinda yayi a baya ba.

Ba sharadi bane ace mutum sai ya fito fili ya nuna laifin da ya yiwa Allah a fili ba, abinda ya zama sharadi a Kansas shine in dora mutane yayi kan bata, to, dole ya fito ya bayyana musu cewa abinda ya dora su kansa fa a baya baya ne, yanzu ga daidai azo a bi.

Ko da shike munji wannan jawabi ne na Sayyid (H) daga baya, amma da farko munji ne ta hanyar joni daga wasu wakilai na yankin Kano ba wai kai-tsaye daga gare shi muka ji ba, kuma munyi imani da abinda muka ji daga bakinsu kafin muji kai-tsaye daga bakin Sayyid (H).

Abinda wannan ke koyar damu shine, ashe wakilci na da fa'ida, domin ba komai ne za ka iya ji kai-tsaye daga bakin wanda kake so kaji ba, kuma ta wannan haryar saqon Annabi (S.A.W.W) yazo zuwa gare mu. Duk wani saqo na Annabi (S.A.W.W) mun ji shi ne ta hanyar daga wane, daga wane, daga Annabi (S.A.W.W), wato an sami (chain of transmission).

Cikin hadisar Ghadeer bayan doguwar khudbar da Annabi (S.A.W.W)yayi sai yace musu:

" WANDA KE NAN YA ISARWA WANDA BAI NAN." Kuma ta wannan hanyar saqon ghadeer ya iso gare mu.

Da munce lalle sai mun ji kai-tsaye daga gare shi, to, da yanzu babu wanda ke kan addinin Allah wanda Annabi Muhammad (S.A.W.W) yazo da shi.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        (08137925034)

30th January, 2022/ 27th Jimada-Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post