Daga kyawawan zantukan Hikima na Imam Ali (A.S) Fita ta biyu (2)


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DUKKAN WANI ABINDA BA YA AMFANARWA YANA CUTARWA

Cigaba:-

-‏من أقوال الإمام علي عليه السلام:

Cikin zantukansa na hikima (A.S) yana cewa;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

(6) " كن في الدنيا ببدنك وفي الآخرة بقلبك وعملك."

" KA KASANCE CIKIN DUNIYA DA GANGAR JIKINKA, A CIKIN LAHIRA KUMA DA ZUCIYARKA DA AYYUKANKA."

Shi gangar jiki ba shi da wani amfani in ba anan duniya ba, saboda haka duk wani abinda za kayi masa zai qare ne anan duniya.

Ayyuka kuwa dasu ake zuwa lahiya, mummuna ne ko kyakkyawa. Duk wanda tunaninsa shine lahirarsa ba zai taba shagala daga aikata kyawawan ayyuka ba.

(7) " ليس بمؤمن من لم يهتم باصلاح معاده."

" DUK WANDA BAI DAMU DA GYARA MAKOMARSA (LAHIRARSA) BA BA MUMINI BANE.

Mumini kadai ke damuwa wajen gyaran makomarsa, amma duk wanda ba mumini bane za kaga damuwarsa kawai ita ce ya duniyarsa za tayi kyau? Saboda haka sai ya kasance kullum a gyaranta yake maimakon gyaran lahirarsa.

(8) " كلما لا ينفع يضر والدنيا مع حلاوتها تمر والفقر بعد الغنى بالله لا يضر."

" DUK WANI ABINDA BA YA AMFANARWA TO, YANA CUTARWA. KUMA (ita) DUNIYA DA ZAQINTA TANA SHUDEWA, TALAUCI KUWA BAYAN WADATUWA DA ALLAH BA YA CUTARWA.

Yi nazari sosai ka gani, babu wani abinda za ka aitawa wanda ba shi da amfani gare ka face ya cutar da kai. Wannan abu kuwa ko zama ne ko aiki ne ko kuma magana ce. Matuqar dai ka nazarci abinda ka aikata ko abinda ka nisanta matuqar ba shi da wani amfani gare ka, to, zai cutar da kai.

Shi kuwa talauci in dai har ka wadatu da abinda Allah ya hukunta a kanka ba za ka taba yin hasara ko ka cutu ba, domin haka Allah yaso ya ganka kuma hakan shine alkhairi gare ka tunda haka Allah yaso ya ganka.

(9) " من قنع بقسم الله استغنى."

" DUK WANDA YA WADATU DA KASON (da) ALLAH (yayi) ZAI WADATU."

Babu wanda zai yarda da qaddarar Ubangiji face ya wadatu a lahirarsa, domin duk abinda kaga Allah ya hukunta a kanka to, haka yaso kuma haka ne mafi dacewa da kai. Wannan kaso kuwa na arziqi ne ko lafiya ce ko kuma 'ya'ya, domin za kaga wani cikin wadata da lafiya da kuma arziqin 'ya'ya, wani kuma sai Allah ya jarrabce shi da rashin ko daya (1) daga cikin wadannan.

(10) " صدقة العلانية تدفع ميتة السوء."

" SADAQA TA BAYYANE TANA TUNKUDE MUMMUNIYAR MUTUWA."

Idan aka ambaci sadaqa ta hada dukkan wani nau'i na ciyarwa, wannan sadaqa ka bayar da ita ne a matsayin imfaqi don taimakawa wajen aikin wani alheri ko kuma ka ciyar ne ga mabuqata ko ka bayar da ita ne ga wani don sauqe nauyin da ya hau kansa na bashi ko makamantansu.

Fa'idar yin sadaqa a bayyane yana qarawa masu qoqari qoqarin ciyarwa kuma yakan sa wadanda ba sa qoqari suyi koyi da dashi.

Idan ya zama ana neman sadaqa (imfaqi) don yin wani aiki ko taimakawa wani sai aka sami wani mai qoqari ya fito fili ya taimaka da wani abu mai kauri kamar ace kudi #10,000, to, yin hakan zai qarfafi wanda ke da nufin bayar da qanqani ya qara don ganin wannan qwazo naka.

Saboda haka duk mai wannan dabi'a ba zai taba yin mummuniyar mutuwa ba da iznin Allah.

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        (08137925034)

13th January, 2022/ 10th Jimada-Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post