Daga kyawawan zantukan Hikima na Imam Ali (A.S) Fita ta ɗaya (1)


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BAYAN ANNABI (S.A.W.W) BABU KAMAR IMAM ALI (A.S) A HIKIMAR ZANCE

Manzon Allah (S.A.W.W) shi yafi kowa hikimar zance kuma wanda yafi kowa kyawawan dabi'u da iya tarbiyya. Duk wata hikima da dabi'a wacce wani zai samu ba za a sami wanda zai tattara su kamar wanda Annabi (S.A.W.W) ya zaunar dashi a qarqashinsa tun daga halin quruciyarsa zuwa girmansa ba.

Wannan dalili yasa kaf cikin Sahabban Annabi (S.A.W.W) babu kamar Imam Ali (A.S) wajen tarbiyya da hikimar zance.

GA KADAN DAGA CIKIN ZANTUKANSA (A.S)

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

 -من أقوال الإمام علي عليه السلام:

(1)- " من لم يؤثر الآخرة على الدنيا فلا عقل له."

" DUK WANDA BAI FIFITA LAHIRARSA AKAN DUNIYARSA BA BA SHI DA HANKALI."

Wannan magana haka take wajen mai tunani, domin ko riddar da kaji aka ce anyi a bayan wafatin Annabi (S.A.W.W) ai fifita duniya ne kan lahira. Da lahirar aka fifita akan duniya da ba a halaka ba.

(2)- " طوبى لمن ذكر المعاد فأحسن."

" DADI YA TABBATA GA WANDA YA TUNA MAKOMARSA (lahira) KUMA YA KYAUTATA."

Duk wanda ba ya tuna makomarsa ba zai kyautata ayyukansa ba.

 (3)- " شاور ذوي العقول تأمن الزّلل والندم."

" KU NEMI SHAWARIN MA'ABOTA HANKALI, SAI KU AMINTU DAGA QASQANCI DA YIN NADAMA."

In dai za ka riqa neman shawarwarin masu hankali kafin ka zartar da wani abu ko ka aikata shi, to, ba za ka taba daukar qasqanci ko yin nadama bayan aikatawa ba.

Ai za kaga da yawa mutane na zartar da wani abu ko don ganin qarfin mulki ko dukiya, amma kuma daga qarshe sai su dau qaqanci da yin nadama.

(4)- " عليك بالسّكينه فإنّها أفضل زينه."

" NA HOREKA DA NUTSUWA (cikin komai naka), DOMIN SHI (nutsuwa) SHINE MAFIFIN ADO."

Duk kyan mutum da iliminsa da dukiyarsa da mulkinsa idan aka ce ba shi da nutsuwa, to, wawa za a dauke shi, domin zai riqa yin wasu dabi'u na zargi.

Yanzu da ace kana da mata biyu 🤓🤓 sai ya zama aka sami dayar kyakkyawa ce marar nutsuwa, kuma dayar ba ta kai dayar kyawu ba amma ta fi ta nutsuwa, to, in dai ba irin dabi'ar nan ta maza kake da ita ba sai ka ji nutsattsiyar nan ta fi nutsuwa cikin zuciyarka.

(5)- " عليك بالشّكر في السرّاء والضّرّاء."

" NA HORE KA DA YIN GODIYA CIKIN SAUQI DA TSANANI."

Ka zama mai godiya ga Ubangijinka cikin kowanne irin yanayi ka sami kanka, idan kana cikin wadata ko lafiya ka gode Masa, hakama in halin qunci kake ko jinya ka gode Masa.

Godiyarka gare Shi (T) cikin wadata qarin wata ni'ima ce da wadata gare ka, sannan rashin godiyarka gare Shi don ka sami kanka cikin quncin rayuwa ko jinya ba zai qare ka da komai ba, domin Shi yake da ikon wadata ka da yaye maka dukkan wata matsala da kake cikinta.

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

11th January, 2022/ 8th Jimada-Sani, 1443

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post