DAGA WA'AZOZIN IMAM ALI (A.S)
Allah (S.W.A) ya qaddara rayuwar bayinSa ne bisa jarrabawowi ta hanyoyi mabambanta, wasu akan jarraba su da ni'ima wasu kuma a jarraba su da bala'i.
Mafi yawan wadanda ake jarraba su da ni'imomi ba muminai bane, kamar yadda ake jarraba mafi yawan muminai da bala'i. Mafi yawa in kaga mumini ba za kaga an jarraba shi da ni'ima ba sai dai bala'i don a nuna maka cewa salihan bayi da bala'i ake jarraba su.
Babban misali shine, mafi yawan Manzannin Allah an jarrabe su ne da bala'i kala-kala gwargwadon yadda matsayinsu yake wajen Ubangiji. Su kuwa fajirai an fi jarraba su da ni'ima, kamar dukiya ko mulki kamar yadda aka bawa Fir'auna da Qaruna.
Sai ya zama cewa cutarwa da muzgunawa da qazafe-qazafe ga muminai shine babban jarrabawar da Allah ke yi musu don su sami babban matsayin da ya tanada musu.
A yau in kaga anyi taron dangi kan mutum ana aibanta shi ko cutar da shi, to, wannan ita ce babbar alama ta gane mumini bawa Allah na qwarai abin riqo da kuma koyi da shi.
Muna da manyan bayin Allah guda biyu abin misali a wannan qasa, domin su suka siffantu da irin jarrabawar da aka yiwa Manzanni (A.S), wato ina nufin SAYYID ZAKZAKY (H) da kuma SHEIKH ABDUL-JABBAR SHEIKH NASIRU KABARA (H).
Abinda ake yi musu na zalunci ya sha bamban da dukkan wani abinda ake yiwa wasu koma bayansu, wannan yasa na tuno da wa'azin Imam Ali (A.S) inda yake cewa;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
قال علي رضي الله عنه: يا ابن آدم، لا تفرح بالغنى، ولا تقنط بالفقر، ولا تحزن بالبلاء، ولا تفرح بالرخاء. فإن الذهب يجرب بالنار، وإن العبد الصالح يجرب بالبلاء. وإنك لا تنال ما تريد، إلا بترك ما تشتهي. ولن تبلغ ما تؤمل إلا بالصبر على ما تكره. وابذل جهدك لرعاية ما افترض عليك.
Imam Ali (A.S) yace:
" YAA KAI 'DAN ADAM ! KADA KAYI FARIN CIKI DA (ganin) WADATA (da ka samu), KUMA KADA KA YANKE TSAMMANIN (samun rahma don ka sami kanka cikin) TALAUCI , KUMA KADA KAYI BAQIN CIKI SABODA BALA'I, KUMA KADA KAYI FARIN CIKI DON SAMUN SAUQI, DOMIN ITA ZINARI ANA JARRABATA NE DA WUTA, SHI KUWA BAWA SALIHI ANA JARRABA SHI NE DA BALA'O'I. KUMA LALLE KAI BA ZA KA SAMI ABINDA KAKE NUFI BA HAR SAI TA HANYAR BARIN ABINDA KAKE SHA'AWA, KUMA BA ZA KA KAI GA (cimma) ABINDA KAKE AIKATAWA BA HAR SAI DA HAQURI KAN ABINDA KAKE QI, KUMA KA ZAGE DAMTSENKA WAJEN KIYAYE ABINDA AKA FARLANTA SHI A KANKA."
(Mawa'izus-Sahaba)
SHARHI
_________
Abinda wannan magana ta Imam Ali (A.S) ke koyar damu shine, samun wadata ba tsoron Allah cikinta ba abin farin ciki bane, kuma don ka sami kanka cikin talauci kada ka yanke samun wadata daga Allah, domin ko ta kubuce maka anan duniya matuqar ka bi Allah da Taqaqa to, za ka wadatu a lahira.
Sannan kuma dukkan wani bala'i (jarrabawa) da za ka fuskanta daga azzalumai ko maqiya ko mahassada kada kayi baqin ciki da hakan, domin babu wanda ya tsira da irin haka daga Manzanni (A.S), kuma don ka ganka cikin sauqi ba tare da cutuwa daga azzalumai ba kada kayi farin ciki, domin Fir'auna da mashawartansa basu tsira daga azabar Allah ba.
Sannan kuma ana nuna mana cewa tarin dukiya (Zinari) da wuta za a jarraba ta ranar alqiyama, idan ta taru ta hanyar kirki ce kuma aka ciyar da ita ta hanyar kirki, to, ka tsira daga wuta. Shi kuwa bawa salihi dole a jarrabe shi da bala'o'i anan duniya don aga shin abinda yake fada ko yake yi da gaske ne.
Kuma ka sani ba za ka taba samun abinda kake nufi na ganin tabbatuwar addini ko ganin Annabi (S.A.W.W) da iyalansa (A.S) sune mafifita kan kowa ba dole sai ka bar dukkan wasu sha'awowi na duniya. Haka kuma ba za ka taba cimma wannan buri naka ba har sai ka yi haquri daga dukkan abinda zai faru a kanka, kuma ya zama ka dage ka tsaya qyam kan abinda Allah ya dora maka.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
9th January, 2022/ 6th Jimada-Sani, 1443.