𝑫𝑨'𝑨𝑾𝑨𝑹 𝑫𝑨 𝑴𝑼𝑲𝑬 𝒀𝑰: – 𝑺𝑯𝑨𝑰𝑲 𝑰𝑩𝑹𝑨𝑯𝑬𝑬𝑴 𝒁𝑨𝑲𝒁𝑨𝑲𝒀 (𝑯)


 Daga_ Faruq Sani Kudan

Mu yanzu mene ne aikin mu a al'ummar nan da muka samu kan mu? Shiru za mu yi kowa ya yi ta kansa, ya je ya yi Sallarsa, alabashi al'ummar ta gama lalacewa ? Ko kuma za mu miΖ™e ne mu kira al'ummar mu ce a dawo ga addini ? To wannan maganar da nake, gaskiyar magana ya fara tun a cikin Ζ™arshen Saba'inoni ne, loΖ™acin muna Ι—alibai. To kuma a Ζ™arshen Saba'inonin ne aka yi wata waΖ™i'ar da ta girgiza duniya, shi ne juyin musulunci na Iran, a loΖ™acin da ake ganin kamar addini ya zama tsohon ya yi.

Na'am akwai yunΖ™uri da aka rinΖ™a samu. An samu yunΖ™uri na mutane irin su Hassan Albanna ( Allah ya rahamshe shu?), Wanda ya assasa 'Ikhwanul Musulmin', akwai kuma yunΖ™uri irin na su Sayyid Abul A'ala Maududi, wanda shi ma ya kafa 'Jama'atul Islami', aka ja shi da ra'ayi ya shiga siyasa, aka tsaya takara. 'Jama'ati Islami' ta zama jam'iyar siyasa, La- samahallah, 'Blander' irin wannan ake gudun aukuwa. To kuma shi ma irin wannan 'Blander', 'yan 'lkhwan' sun auka masa, yayin da wani Sarki FaruΖ™ ya ce zai yi Shari'ar Musulunci, suka ce masha Allah! Suka yi masa mubaya'a, da irin waΙ—annan bilandodi.

''Sai ga juyi wanda ya fita daban, shi ne, juyin Imam Khomaini (KS), shi bai faΙ—a tarko irin na siyasa ba, kuma ya tsaya Ζ™yam! To, sai ga shi kawai ya fitar da samfuri na irin da'awar Annabi (S) a wannan loΖ™aci, a yayin da mutane suke ganin kamar addini ba zai yiwu ya dawo ba. To masha Allah, ka ga shikenan ma ga samfur mun gani, ba kawai abin da muke fatan zai yiwu, wasu suna ce mana ba zai yiyu ba, ga shi ya yiwu akan idanun mu. Don haka ne ma kafircin duniya ya ankara da irin haΙ—arin juyin musulunci na Iran zai kawo, ya ga cewa da can shi ya Ι—auka ya gama da duniyar Musulmi.

Ya Ι—auka shikenan duniya ya riga ya mata 'Definition' kuma an gama, shi musulunci ya koma babin abin da ya kira addini, ''Personal Affairs'' tsakanin mutum da ubangijinsa, ya riga ya ci duniya da yaΖ™i akan cewa yanzu duk nizamin da za a bi sunan shi rashin ruwa da addini, ya raba addini da siyasa, wato mulki daban siyasa daban. Addini ya taΙ“a mulki, amma a zamanin da ne, loΖ™acin da kai bai waye ba. Yanzu duniya ta cigaba, ba lokacin yin wannan ne ba. 

Bilhasali ma mun taΙ“a yin taro irin wannan a jami'a, muka kawo cewa yadda addini ya kafu ya yi iko (a baya), har wani ya yi mana raddi, da cewa eh an ji, addininku ya taΙ“a iko da duniya a wani loΖ™aci, amma loΖ™acin kai bai waye ba ne, a wannan zamani cigababbe ba zai yiwu a dawo da addini ba, zamanin 'Science' da 'Technology'. To kama-kama da'awa tun zai yiwu ko ba zai yiwu ba.

Har na karanta ' Article' Ι—in wani, ya bani mamaki, shi ban Ι—auka ma ' Symphatizer' bane, amma sai na ga ya rubuta ' article' , amma na ga 'part one' ne, ya saka masa 'title' 'To be or not to be' wato zai yiwu ko ba zai yiwu ba. To sai ya ce a saurare shi a Ι“angare na biyu. A Ζ™arshen Ι“angaren na farkon, sai ya yi ishara ya zuwa ga wannan Harka. Ya ce ga shi muna da 'ya'yanmu da Ζ™anne mu da yanzu suke ce ma a koma ga addini. Tambaya ita ce, zai yiwu ( a komawa Addinin) ko ba zai yiwu ba? A saurare mu a rubutu na gaba, to ban ga na gaban ba, loΖ™acin ina tsare ne, ban kuma ga cigaban maganar ba kome ya ce ? Oho.

Daga_ faruq Sani Kudan (Abban Jeedah) 

17/1/2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post