Ba a tambayar mutum dalilin dukan matarsa — in ji Umar Bm Khaddab


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED

HUJJAR DA TA SABAWA QUR'ANI DA SUNNAR ANNABI (S.A.W.)

Sau da yawa wasu ba sa ganin abubuwan da ake kawowa daga magabata a matsayi darasi, yawanci suna dauka ne cewa kuskurensu ko kawo gyara cikin wasu ayyukansu a matsayin cin mutunci.

Shi addini ba kayan gado bane kuma ba ra'ayi bane ballantana ace duk abinda mutum ya kawo na ra'ayinsa ya zama addini. Saboda haka dole a riqa yin magana kan irin wadannan kura-kuran don kada a dauke su a matsayin addini har mutane su halaka.

MATSAYIN DUKAN MACE A MUSLIM

Dukan mace (mata) ba ya daga cikin koyarwar Manzon Allah (S.A.W.W) ballantana ace an rangwanta wajen yinsa, sai dai an samu cewa Umar Bn Khaddab ba ya ganin dukan mata a matsayin laifi ko kuskure kamar yadda yazo daga bakinsa.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

120- حَدَّثَنَا سُلَيْمَانُ بْنُ دَاوُدَ يَعْنِي أَبَا دَاوُدَ الطَّيَالِسِيَّ ، قَالَ : حَدَّثَنَا أَبُو عَوَانَةَ ، عَنْ دَاوُدَ الْأَوْدِيِّ ، عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ الْمُسْلِيِّ ، عَنِ الْأَشْعَثِ بْنِ قَيْسٍ ، قَالَ : ضِفْتُ عُمَرَ ، فَتَنَاوَلَ امْرَأَتَهُ ، فَضَرَبَهَا ، وَقَالَ : يَا أَشْعَثُ ، احْفَظْ عَنِّي ثَلَاثًا حَفِظْتُهُنَّ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " لَا تَسْأَلْ الرَّجُلَ فِيمَ ضَرَبَ امْرَأَتَهُ ، وَلَا تَنَمْ إِلَّا عَلَى وَتْرٍ " ، وَنَسِيتُ الثَّالِثَ

نحو

Imam Ahmad Bn Hambal ya riwaito cewa: Sulaiman Bn Dawud ya bamu labari, wato baban Dawud Ad-'Dayaalisiyyi yace: Abu Awanata ya bamu labari daga Dawuda Al-Awdiyyi, daga Abdurrahman Al-Musliyyi, daga Ash'Ass Bn Qais yace: Umar ya wayi gari sun sami sabani da matarsa, sai ya doke ta ! Sannan ya

" Yaa Ash'As, ka kiyaye abubuwa uku daga gare ni wadanda na kiyaye su daga Manzon Allah (S.A.W.W)

" KADA KU TAMBAYI MUTUM (dalilinsa) NA DUKAN MATARSA, KUMA KADA KUYI BACCI FACE KUNYI WUTRI" Na manta na ukun (inji Umar)

(MUSNAD AHMAD, HADISI MAI LAMBA 12!

                  NAZARI

                __________

Tabbas cikin wannan hadisi na Umar akwai qarya cikinsa domin ba daga Annabi (S.A.W.W) ya ji maganar ba, ya fadeta ne kawai don ya kare mummunan aikinsa ta hanyar yiwa Annabi (S.A.W.W) qarya. Dalili kuwa shine, babu inda Annabi (S.A.W.W) ya koyar da cewa ana iya dukan mace a aikace saboda wani laifin da tayi, kuma bai taba yin umarni game da haka ba, sannan bai taba gani an aitaka a gabansa yayi shiru ba. To, ta yaya zai fadi wannan magana wai idan kaga mutum ya bugi matarsa kar ka tambaye shi dalili.

ALLAH BAI YI UMARNI DA YIN DUKA

Mu bibiyi wannan ayar dake qasa mu gani.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

ٱلرِّجَالُ قَوَّٰمُونَ عَلَى ٱلنِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ  بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ وَبِمَآ أَنفَقُواْ مِنۡ أَمۡوَٰلِهِمۡۚ فَٱلصَّٰلِحَٰتُ قَٰنِتَٰتٌ حَٰفِظَٰتٞ لِّلۡغَيۡبِ بِمَا حَفِظَ ٱللَّهُۚ وَٱلَّٰتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ  وَٱهۡجُرُوهُنَّ فِي ٱلۡمَضَاجِعِ وَٱضۡرِبُوهُنَّۖ فَإِنۡ أَطَعۡنَكُمۡ فَلَا تَبۡغُواْ عَلَيۡهِنَّ سَبِيلًاۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيّٗا كَبِيرٗا(

" MAZAJE SU KE DA IKO AKAN MATA SABODA FIFIKON DA ALLAH YA FIFITA SASHESU AKAN SASHE, DA KUMA CIYAR DASU DA SUKE YI DAGA DUKIYARSU. ITA SALIHA MAI QANQAN DA KAI MAI TSARE GHAIBUN DA ALLAH YA TSARE. IDAN HAR KU KA JI TSORON BIJIREWARSU, TO, KUYI MUSU WA'AZI KUMA KU QAURACE MUSU A MAKWANCI KUMA KUYI MUSU BARAZANA. IDAN HAR SU KAYI MUKU BIYAYYA TO, KADA KU NEMI WATA DAMA A KANSU (wajen cutar dasu don gani suna haquri da ku da yi muku biyayya), LALLE ALLAH MADAUKAKI NE MAI GIRMA.

          (NISA'I, AYA TA 3)

NB:- Ita wannan kalma ta barazana ana iya yinta ta hanyoyi dabam amma ba ta hanyar duka ba. Misali za ka iya ce mata in har bata bar abinda take yi maka ba za ka hadata da mahaifanta ko za ka sake ta. 

Kalmar (Dharb) da akayi amfani da ita cikin Qur'ani barazana take nufi ba wai duka ba, domin Allah yayi amfani da ita cikin wata aya inda yake cewa: " KUMA ALLAH NA BUGA MUKU MISALI...

Kunga buga misali ai ba duka yake nufi ba.

ANNABI (S.A.W.W) BAI TABA UMARNI DA YIN DUKA Ba

Yanzu za mu kalli abinda aka kawo game da Tafsirin ayar sama muga menene Annabi (S.A.W.W) yace game da haka.

(1)-  وأخرج عبد الرزاق وابن سعد وابن المنذر والحاكم والبيهقي عن إياس بن عبد الله ابن أبي ذئاب قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «لا تضربوا إماء الله

Abdurrazaq Bn Sa'ad da Ibn Munziri da Hakamu da Baihaqi sun fitar daga Iyaas Bn Abdullahi Bn Abiy Za'iba yace: Manzon Allah (S.A.W.W) yace;

" KADA KU BUGI BAYIN ALLAH (mata)

 فقال عمر: ذئرن النساء على أزواجهن، فرخص في ضربهن

 فأطاف بآل رسول الله صلى الله عليه وسلم نساء كثير يشكين أزواجه

Sai Umar yace: " Ai matan na yin tsageranci ne ga mazajensu." Sai Annabi (S.A.W.W) yayi musu rangwame (wai za su iya dukan nasu tunda tsageranci suke yi musu).

Sai ga shi mata masu yawa sun kewaye Iyalan Manzon Allah (S.A.W.W) suna kuka game da mazajensu (sun addabe su da duka)

 فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ليس أولئك خياركم

Sai Manzon Allah (S.A.W.W) yace;

" AI WADANNAN (mazaje masu dukanku) BA SU KASANCE DAGA ZABABBUNKU BA"

(2)-  وأخرج ابن سعد والبيهقي عن أم كلثوم بنت أبي بكر قالت: كان الرجال نهوا عن ضرب النساء، ثم شكوهن إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم، فخلى بينهم وبين ضربهن ثم قال: «ولن يضرب خياركم».

Ibn Sa'ad da Baihaqi sun fitar daga Ummu-Khulthum Bnt Abubakar tace: " Wani mutum yana dukan mata, sannan yakai qararsu zuwa ga Manzon Allah (S.A.W.W), sai ya shiga tsakaninsu da dukan da suke musu (ya hanasu kada su qara dukansu). Sa'an nan yac

" KUMA (ai) ZABABBUNKU (mazajen kirki daga cikinku) BA SA DUKA.

(3)-  وأخرج ابن أبي شيبة وأحمد والبخاري ومسلم والترمذي والنسائي عن عبد الله بن زمعة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «أيضرب أحدكم امرأته كما يضرب العبد، ثم يجامعها في آخر اليوم؟!».

Ibn Abu Shaibata da Ahmad da Bukhairi da Muslim da Tirmidhi da Nisa'i sun fitar daga Abdullahi Bn Zam'ata yace: " Manzon Allah (S.A.W.W) yace;

" YANZU 'DAYANKU ZAI RIQA DUKAN MATARSA KAMAR YADDA YADDA YAKE DUKAN BAWA ? SA'AN NAN (don ba shi da kunya) YA (nemi) SADUWA DA ITA A QARSHEN YINI.

(4)-  وأخرج عبد الرزاق عن عائشة عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «أما يستحي أحدكم أن يضرب امرأته كما يضرب العبد، يضربها أول النهار ثم يضاجعها آخره

Abdurrazaq ya fitar daga A'ishatu daga Annabi (S.A.W.W) yace;

" YANZU 'DAYANKU BA YA JIN KUNYA YA BUGI MATARSA KAMAR YADDA YAKE DUKAN BAWA? YA BUGE TA A FARKON YINI SA'AN NAN A QARSHEN YINI YA NEMI SADUWA (jima'i) DA DA ITA .

Tirmidhi ya fitar kuma Nisa'i ya inganta shi da Ibn Majah daga Amruu Bn Ahwaaz.

(Durrul-Mansur na Suyudi qarqashin Tafsirin aya ta sama.

                 TAMBAYA

(1)- Bisa la'akari da wadannan riwayo hudu (4) za mu iya cewa, a ina Annabi (S.A.W.W) yayi umarni ko bada damar dukan mace har ma yace ba a tambayar mutum dalili in ya bugi matarsa.

(2)- Anya kuwa ba Umar yana neman kare kansa da cigaba da aikata abinda Annabi (S.A.W.W) yayi hani a kansa bane kuma ya qirqiri qarya ya jinginata gare shi (S.A.W.W)

(3)- Yanzu idan aka ce babban Limaminku ko shugabanku cikin qungiyarku yana dukan matansa komai tsagerancinsu za su sanya shi cikin mai halin kirki.

(4)- Yanzu kai wanne ka dauka, dukan matarka kamar yadda Umar yake yi ko kuma nisantar dukanta kamar yadda Annabi (S.A.W.W) yayi han

MAI HANKALI KADAI KE IYA FAHINTAR WANNAN YA

Daga wakilanmu na Bauchi zone

Tare da Ado Isah Guda

        (0813792503

17th January, 2022/  14th Jimada-Sani, 14434)a.e.REi?i?)?a?YAa)s.?"e:».?"ce:

."e:

."e:»..". ن. ."e:.a:BA ..".S4)." ٤٣)i; BA ?_RI0)." :ce:ه.ةَ.a.CIa.i.W) @ne.


Tare da Ado Isah Guda.


        (08137925034)


17th January, 2022/ 14th Jimada-Sani, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post