Azara ba mahaifin Annabi Ibrahim (A.S) ba ne; kawunsa (Amminsa) ne


AYOYIN QUR'ANI SUN TABBATAR DA; KALMAR UBA (أب) A LARABCI TAKAN ZO DA MA'ANAR KAWU, BABBA, AMMI (KANIN / YAYAN MAHAIFI / MAHAIFIYA, YAYA...).

Ibn Kasir (Babban malamin Ahlus-sunnah) ya na cewa:

"Sunan Mahaifin Annabi Ibrahim(as) shine Tarikh".

ﻫﻮ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﺑﻦﺗﺎﺭﺥ...

- ﺍﻟﺒﺪﺍﻳﺔ ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﻳﺔ ‏: ﻗﺼﺔ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﺍﻟﺨﻠﻴﻞ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﻟﺴﻼﻡ، ﺹ : 324.

Imam Suyuti (Babban malamin Ahlus-sunnah) ya nakalto cewa:

"Azara ba mahaifin Annabi Ibrahim(as) bane, kawunsa ne":

ﺇﻥ ﺁﺯﺭ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻭﺍﻟﺪ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ، ﺑﻞ ﻛﺎﻥ ﻋﻤﻪ.

- ﺍﻟﺤﺎﻭﻱ ﻟﻠﻔﺘﺎﻭﻱ : ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ﺍﻟﺤﺪﻳﺜﻴﺔ ‏: ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺒﻌﺚ ‏: ﻣﺒﺤﺚ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ ‏: ﻣﺴﺎﻟﻚ ﺍﻟﺤﻨﻔﺎ ﻓﻲ ﻭﺍﻟﺪﻱ ﺍﻟﻤﺼﻄﻔﻰ، ﺹ : 254.

Kalmar baba (الأب) ta na dokar ma'anar kani ko yayan mahaifi / Mahaifiya. Ga abinda da masana harshen Larabci suka ce akan ma'anar kalmar baba (الأب):

ﺍﻷﺏ: ﺍﻟﻮﺍﻟﺪ ﻭﺍﻟﺠﺪ ﻭ ﻳﻄﻠﻖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﻢ ﻭ ﻋﻠﻰ ﺻﺎﺣﺐ ﺍﻟﺸﺊ ﻭ ﻋﻠﻰ ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﺳﺒﺒﺎ ﻓﻲ ﺇﻳﺠﺎﺩ ﺷﺊ ﺃﻭ ﻇﻬﻮﺭﻩ ﺃﻭ ﺇﺻﻼﺣﻪ...

"(Kalmar) Baba (a Larabci tana daukar ma'anoni 5): 1 - Mahaifi. 2 - Kaka (mahaifin mahaifi). 3 - Kawu (kani ko yayan mahaifi). 4 - Ma'abucin wani abu. 5 - Wanda ya samar da wani abu.

- المعجم الوسيط من معاجم الراغب الأصفهاني، الميداني، ابن فارس...

Tabbas Qur'ani ya tabbatar mana da cewa; kalmar baba (الأب) ba mahaifi kawai ta ke nufi ba, Allah(swt) ya na cewa;

أَمْ كُنتُمْ شُهَدَاءَ إِذْ حَضَرَ يَعْقُوبَ الْمَوْتُ إِذْ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعْبُدُونَ مِن بَعْدِي قَالُوا نَعْبُدُ إِلَٰهَكَ وَإِلَٰهَ آبَائِكَ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ إِلَٰهًا وَاحِدًا وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ.

"Shin kuna gurin ne daf da lokacin da (Annabi) Yakub(as) zai yi wafati; yayinda ya ke cewa 'ya'yansa; me zaku cigaba da bautawa a bayana? Sai suka ce; zamu bautawa Ubangijinka, kuma Ubangijin babanninka (iyayenka); Ibrahim(as), Isma'il(as) da Is'haq(as)..."

[2. Al-Baqara : 133]

A wannan ayar, an yi amfani da kalmar اباء (iyaye), wacce ta ke jam'in mufradin kalmar أب ce. Kuma a ayar an saka Annabi Isma'il(as) a jerin iyayen Annabi Yakub(as); alhali kawunsa ne ba babansa mahaifi ba ne, kenan wannan ayar ta tabbatar mana kalmar baba tana dokar ma'nar kani ko yayan mahaifi?

Sannan Allah(swt) ya na cewa akan harshen Annabi Yusuf(as);

وَاتَّبَعْتُ مِلَّةَ آبَائِي إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ ۚ مَا كَانَ لَنَا أَن نُّشْرِكَ بِاللَّهِ مِن شَيْءٍ ۚ ذَٰلِكَ مِن فَضْلِ اللَّهِ عَلَيْنَا وَعَلَى النَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَشْكُرُونَ

"Ina kan turbar iyayena; Ibrahim(as), Is'haq(as) da Yakub(as)..."

[12. Yusuf : 38].

Shin Annabi Ibrahim(as) da Is'haq (as) iyayen Annabi Yusuf(as) ne ko kakaninsa? Kenan kalmar baba tana dokar ma'anar kaka?

Ko Hausawa ma kan kira duk wani babban mutum (datijo) da baba, hakama Hausawa kan cewa kani ko yayan mahaifi; baba, kuma su kan kiran mijin mahaifiya ko wanda ya riki mutum da baba, wannan ya tabbatar mana da cewa kalmar baba ba mahaifi kawai ta ke nufi ba.

➖➖➖➖➖➖➖➖➖

Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com

🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post