ISHARA KAN ZAMA HUJJA GA MAI HANKALI
Yau ba dogon rubutu zanyi kamar wanda na saba ba, sannan ba ruwan hujjoji zan zubo kamar yadda ake zubo su kan wata mas'ala ko subhar da maqiya muslimci ke kawowa ba.
Zan taqaita kawai kan wata ishara ko aya data bayyanna game da Sayyid Zakzaky (H) bayan wannan waqi'ar Zariya wacce Buhari ya aiwatar.
Maganganu sun bayyana ki sun gabata daga mutane masana cewa irin abinda ya faru ga Sayyid (H) zai yi wuya ace mutum ya rayu, kuma ko da ace ya rayu ba zai amfanar ba, amma sai Allah ya nunawa kowa cewa ai shine mai ikon kashewa da rayawa, shi ke warkarwa ba wanda ake warkar dashi ba.
Bayan dagargaza wasu sassa na jikinsa ta kai har ruwan idanunsa ya tsiyaye kuma idon ya ciro ya fadi qasa, amma ba tare da wata qwaqqwarar jinya ba Allah ya dawo masa da komai nasa.
Qasusuwansa da ruka rududduge sun dawo daidai, sannan idonsa 🧐na hagu wanda ya tsiyaye kuma ya fado qasa ya koma daidai yadda ya zama yana amfani dashi kamar yadda yake yi a baya. Wannan kuwa ba qaramar aya bace wacce Allah ya nunata ga al'umma kamar yadda yake bayyanar da ayoyinsa kan Annabawa (A.S) ga al'umma.
Ga misali za mu bayar cikin hotuna ko za su zama inza ga masu hankali da rabauta.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
6th January, 2022/ 3rd Jimada-Sani, 1443