Jaridar Al-akhbar ta kasar Lebanon ta bayar da rahoton cewa, A baya-bayan nan ne wasu masu shiga tsakani suka aike da sako daga gwamnatin Amurka zuwa ga kungiyar Hizbullah, inda suka yi kira da a hada kai da kungiyar don gudanar da bincike kan kasar Labanon.
Shi ma dan jaridan kasar Lebanon Hussein Morteza ya ruwaito a shafinsa na Twitter cewa, Seyed Hashem Safi al-Din, shugaban majalisar zartarwa ta kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana a cikin wani shiri cewa Amurkawa sun yi kokari tare da fatan ganin sun cimma matsaya da shugabanin kungiyar Hizbullah.
A cewar dan jaridar na Labanon, shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah ya kara da cewa: Daya daga cikin masu shiga tsakani ne ya isar da wannan sako, kan cewa sun bayyana aniyarsu da shirye-shiryensu na yin shawarwari a kan dukkan batutuwa.
Kungiyar Hizbullah ta yi watsi da bukatar ba tare da an yi wata tattaunawa ba.
Har yanzu dai gwamnatin Amurka ba ta mayar da martani kan rahoton ba, kamar yadda kuma ba ta tabbatar da shi ko kuma musanta shi ba.