AMSA TA ILIMI DA HANKALI DAGA BAKIN IMAM JA'AFARUS-SADIQ (A.S)
Gurare da dama za ka riqa cin karo da maganganun malamai suna cewa Annabi (S.A.W.W) yace Allah na yarda da yardar Fatima, kuma yana fushi da fushinta. Wannan magana kuwa na tabbatar mana ne da cewa dukkan ayyukan Sayyidah Fatima da zantukanta gaskiya wadanda ba sa cin karo da umarnin Allah dana Ma'aikinsa (S.A.W.W).
Sai kuma ake samu wasu na cewa wannan magana ba haka bane, domin an samu ta riqa yin fushi bisa rashin dalili tare da bin son ranta.
Misalin da suke bayarwa shine, ai tayi fushi da Abubakar da ya hana mata Gado mahaifinta bisa hujjarsa ta cewa Annabi yace su Annabawa ba sa gado kuma ba a gadonsu. Suke cewa in kuwa wannan maganar gaskiya ce ana nuna cewa ne Allah na fushi da Abubakar kenan tunda ya fusata Fatimah (S.A). To, menene gaskiyar wannan magana ?
Za muji amsa daga bakin Imam Sadiq (A.S) insha Allah.
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
عَلِيِّ بْنِ الْمُنْذِرِ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ سَالِمٍ عَنْ حُسَيْنِ بْنِ زَيْدٍ عَنْ عَلِيِّ بْنِ عُمَرَ بْنِ عَلِيٍّ عَنِ الصَّادِقِ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَلِيِّ بْنِ الْحُسَيْنِ عَنِ الْحُسَيْنِ بْنِ عَلِيٍّ عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ ع عَنْ رَسُولِ اللَّهِ ص أَنَّهُ قَالَ: يَا فَاطِمَةُ إِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى لَيَغْضَبُ
لِغَضَبِكِ وَ يَرْضَى لِرِضَاكِ قَالَ فَجَاءَ صَنْدَلٌ فَقَالَ لِجَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ ع يَا أَبَا عَبْدِ اللَّهِ إِنَّ هَؤُلَاءِ الشَّبَابَ يَجِيئُونَّا عَنْكَ بِأَحَادِيثَ مُنْكَرَةٍ فَقَالَ لَهُ جَعْفَرٌ ع وَ مَا ذَاكَ يَا صَنْدَلُ قَالَ جَاءُونَا عَنْكَ أَنَّكَ حَدَّثْتَهُمْ إِنَّ اللَّهَ لَيَغْضَبُ لِغَضَبِ فَاطِمَةَ وَ يَرْضَى لِرِضَاهَا قَالَ فَقَالَ جَعْفَرٌ ع يَا صَنْدَلُ أَ لَسْتُمْ رَوَيْتُمْ فِيمَا تَرْوُونَ إِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى لَيَغْضَبُ لِغَضَبِ عَبْدِهِ الْمُؤْمِنِ وَ يَرْضَى لِرِضَاهُ قَالَ بَلَى قَالَ فَمَا تُنْكِرُونَ أَنْ تَكُونَ فَاطِمَةُ ع مُؤْمِنَةً يَغْضَبُ اللَّهُ لِغَضَبِهَا وَ يَرْضَى لِرِضَاهَا قَالَ فَقَالَ لَهُ اللَّهُ أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِسالَتَهُ.
Daga Aliyu Bn Munziri, daga Abdullahi Bn Saalim, daga Hussaini Bn Zaid, daga Aliyu Bn Umara Bn Aliyu, daga Sadiq Ja'afar Bn Muhammad, daga babansa daga Aliyu Bn Hussaini, daga Hussaini Bn Aliyu, daga Aliyu Bn Abu 'Dalib (A.S), daga Manzon Allah (S.A.W.W) yace:
" YAA FADIMATU ! LALLE ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YANA FUSHI DA FUSHINKI KUMA YANA YARDA DA YARDARKI ." Yace:
Sai Sandala yazo ya cewa Ja'afar Bn Muhammad (A.S), " Yaa Abu Abdullah! Lalle wadannan matasan suna zo mana da mummuniyar magana (wai) daga gareka take." Sai Ja'afar (A.S) yace:
" MENENE WANNAN YAA SANDALA ?" Yace:
" Sunzo mana da cewa wai ka basu labarin cewa lalle Allah na fushi da fushin Fatimah, kuma yana yarda da yardarta." Yace: Sai Ja'afar (A.S) yace:
" YAA SANDALA ! ASHE BA KU KUKA RIWAITO CIKIN ABINDA KUKE RIWAITOWA CEWA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA FUSHI DA FUSHIN BAWA MUMINI BA, KUMA YANA YARDA DA YARDARSA ?" Yace: " Hakane." Yace:
" TO, ME YASA KUKE INKARIN FADIMATU (S.A) TA ZAMA MUMINA HAR ALLAH YAYI FUSHI DA FUSHINTA KUMA YA YARDA DA YARDARTA ?" Yace: Sai yace masa:
" ALLAH SHI YASAN INDA YAKE SANYA SAQONSA (baiwarSa)."
Wannan hujja ce ta hankali wacce Imam Ja'afar (A.S) ya bawa Sandala, domin dukkan musulmi mai ilimi yasan Allah na fushi da wanda ya cutar da mumini, kuma yana son wanda ya farantawa mumini. To, idan kuwa an yarda da haka menene dalilin jayayya ko gani Sayyidah Fatimah (S.A) bata cancanta da Allah yayi fushi da fushinta ko ya yarda da yardarta ba?
Wannan hujja ta hankali kenan wacce babu wanda ya isa ya qaryata ta, kamar haka shari'ah ke tafiya daidai da hankali ba sabanin hankali ba.
Saboda haka duk wanda Sayyidah Fatimah (S.A) tayi fushi dashi Allah ma yayi fushi dashi.
معاني الأخبار الْقَطَّانُ عَنْ أَحْمَدَ الْهَمْدَانِيِ عَنِ الْمُنْذِرِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ سُلَيْمَانَ عَنْ إِسْمَاعِيلَ بْنِ مِهْرَانَ عَنْ عَبَايَةَ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ عَنِ النَّبِيِّ ص أَنَّهُ قَالَ: إِنَّ فَاطِمَةَ شِجْنَةٌ مِنِّي يُؤْذِينِي مَا آذَاهَا
وَ يَسُرُّنِي مَا سَرَّهَا وَ إِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى لَيَغْضَبُ لِغَضَبِ فَاطِمَةَ وَ يَرْضَى لِرِضَاهَا.7
Ya zo cikin Ma'anil-Akhbaar na Qaddanu, daga Ahmad Al-Hamdaaniy, daga Munziri Bn Muhammad, daga Ja'afar Bn Muhammad, daga Ja'afar Bn Sulaimanu, daga Isma'il Bn Mihraana, daga Abaayata, daga Ibn Abbas (R.A), daga Annabi (S.A.W.W) yace:
" LALLE FADIMATU TSOKA CE DAGA GARE NI, DUK ABINDA YA CUTAR DA ITA YANA CUTAR DANI, KUMA YANA FARANTA MIN RAI ABINDA YA FARANTA MATA, KUMA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YANA FUSHI DA FUSHIN FADIMATU, KUMA YANA YARDA DA YARDARTA.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج43، ص: 27
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
27th January, 2022/ 24th Jimada-Sani, 1443.