Mutumin da zai iya qaryata maganar Sayyid Zakzaky (H), zai iya qaryata Annabi (S), Zakzaky jaddada maganar Annabi (S) yake yi


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MAGANA CE TA HUJJA BA WAI RASHIN SANIN ABINDA NAKE YI BA

Tunda na zama mukallafi har na fara bautar Allah bisa yaqinin ganin shi yafi cancanta dana bauta Masa ban ci karo ko hadu da wanda yake addinin dake fassara haqiqanin karantarwa Annabi (S.A.W.W) ba.

Naka saurari karatuka ko da'awowi na nasu maluma masu ganin sune akan daidai, amma sai naga sun tare a qarqashin zalunci suna masu yarda da wani tsarin daya sabawa na Mahaliccinsu. Ban taba ji sun soke wannan tsari ba kuma banji suna kira da a kauce masa ba. Maganganunsu sun saba da ayyukansu, kuma ayyukansu yayi hannun Riga da maganganunsu.

Sayyid Zakzaky (H) ne kadai wanda ban taba jin yayi magana sannan yazo daga baya ya canza ba. Haka kuma bai taba magana sannan ace aikinsa ya saba abinda yake fada ba. Duk rintsi ko qanji za ka tarar maganarsa iri daya ce da wacce aka saba jinta tun farkon da'awarsa.

Maganar Annabi (S.A.W.W) ce cewa:

"MALAMAI MAGADA ANNABAWA NE MATUQAR BASU SHIGA DUNIYA KUMA SUN CUDAYYA DA MAHUKUNTA BA....."

Sai ni kuma naga shine wanda bashi da wata alaqa da hukuma ballantana yabi tsarinsu na son zuciyarsu. Saboda haka naga shine samfurin da'awar Manzon (S.A.W.W) wanda ke cutuwa akan da'awarsa kamar yadda Manzanni (A.S) suka cutu. Idan ya fadi magana sai kaga tamkar Annabi (S.A.W.W) ya fada ko da kuwa bai kawo aya ko hadisi ba, kuma babu aya ko hadisin da zai qaryata wannan magana tasa.

Idan ya aikata aiki a aikace ba za ka sami aya ko hadisin daya soke wannan aiki nasa ba. Tun daga nan nasan aiki yake yi irin na Manzon Allah (S.A.W.W) ba tare da wani sabani ba. Saboda haka kuwa in har na qaryata maganarsa to, zan qaryata Manzon Allah (S.A.W.W) tunda aiki da zantukansu iri daya ne !

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      (08137925034)

13th December, 2021/ 8th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post