Yadda ya kamata ka kasance kenan a matsayin ka na wanda ba Ma'asumi ba !


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

FIKIRA IRIN TA UMAR BN KHADDAB (R.A)

Annabawan Allah da Manzanni (A.S) da kuma iyalan Annabi (S.A.W.W) da wasu tsiraru daga bayinSa sune wadanda Allah ya katange daga aikata sabo ko kuskure. Cikin jimlar wadannan dana ambato babu wanda ya taba aikata wani aiki sannan daga baya yayi nadama saboda ganin ya yi shi bisa kuskure. Amma bayan wadannan babu wanda ba ya aikata aiki ko yayi furuci ba tare da yayi nadamar wani abu daga ciki ba.

Har cikin Sahabban Manzon Allah (S.A.W.W) in ka cire iyalansa babu wani mai yaqini kan aikinsa saboda saninsu na aikata abubuwa da Allah ya hane su.

Ga misalin magana daya daga Umar Bn Khaddab.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

قال عمر رضي الله عنه: ما أبالي على أي حال أصبحت، أعلى ما أحب، أم على ما أكره، ذلك لأني لا أدري الخير فيما أحب أو فيما أكره.

Umar (R.A) yace: " BANA DAMUWA AKAN WANNE IRIN YANAYI NA WAYI GARI CIKINSA. ABINDA NAFI DAMUWA A KANSA SHINE, ABINDA NAKE SO DA ABINDA NAKE QI, DOMIN BAN SAN ALKHAIRIN A CIKIN ABINDA NAKE SO NE KO KUMA CIKIN WANDA NAKE QI NE BA."

      (Mawa'izus-Sahabah)

                  DARASI

               ___________

Kunga anan abinda Umar Bn Khaddab ke tabbatarwa shine, ba shi da yaqini cikin ayyukansa ko nace cikin abinda yake so da abinda yake qi, shi yasa yake damuwa don rashin masaniyarsa kan haka. Idan ya zamana cewa kaima baka san abu mai kyau ko mummuna cikin abinda kake so ko kake qi ba, to, dole ka damu kan haka.

Amma ga wanda yake da yaqini cikin zuciyarsa, wato ya san mummuna da kyakkyawa cikin abinda yake so da abinda yake qi, to, ba zai shiga cikin damuwa ba, domin kuwa ya san daidai. Sai dai kuma in zai biye son zuciyarsa wacce Allah yace tana umarni da aikata mummuna.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        (08137925034)

8th December, 2021, 4th Jimada-Ulah,1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post