@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BA ZA KA SAMI ALJANNAH BA HAR SAI KA NEME TA
Kuskure ne ko nace rudar da kai ne ace mutum yana son samun kudi amma kullum yana kwance akan gadonsa, ko kuma ace yana son ilimi amma kullum yana gona ko kasuwa ba tare da fitar da wani lokaci na zuwa wajen malami ba.
Haka kuma ba zai taba yiwuwa ba ace mutum na tsoron jin zafin wuta amma kullum yana tare da ita don biyan wata buqata tasa. Dole ya zamana ya nisanceta kafin ya kubuta daga jin zafinta.
To, kamar hakane ba zai taba yiyuwa ace kana son Aljannah ba amma kuma ba ka aikata komai don neman samun yardar Allah. Kamar dai mai aikata sabo (sin) ne, ba zai yiwu ace ya shiga Aljannah ta wannan hanya ba, dole ya zama ya nisanci aikata abinda Allah ya hane shi.
Ya zo cikin riwaya daga Imam Ali (A.S) kamar haka;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
قال علي رضي الله عنه لرجل: ما تصنع؟ قال: أرجو وأخاف. قال: من رجا شيئًا طلبه، ومن خاف شيئًا هرب منه.
Imam Ali (A.S) ya cewa wani mutum: " ME KAKE AIKATAWA (na wani aiki a rayuwarka) ?" Yace: Ina fata (hope) kuma ina jin tsoro (fear)." Yace:
" DUK WANDA KE FATAN (ya sami wani abu) YANA NEMANSA (ne ba ya kwanta akan gadonsa ba tare da ya nema ba), KUMA WANDA KE JIN TSORON WANI ABU (na cutuwa gare shi) YANA GUDU NE DAGA GARE SHI."
(Mawa'izus-Sahabah)
Ashe babban kuskure ne mutum ya riqa cewa Allah yasa mu cika da imani amma ba ya aikata wani abu na imanin, kuma rudar kaine yace Allah ya raba mu da wuta amma kuma kullum cikin sabawa Allah yake ta hanyar zaluntar bayin Allah da cin amana da kuma aikata dukkan wani nau'in ayyukan da Allah ya hane mu aikata shi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
26th December, 2021/ 21st Jimada-Ulah, 1443.