"Wace Riba Azzalumai Suka Ci Na Kisan Kiyashin Zaria"? _Mlm Qaseem Shehu Shinkafi


Ya tambayi azzalumman Shugabannin Nigeria,a zaman Zikira da ya gudana a Shinkafi Jihar Zamfara

________________________________

fatimaboutique.fh@gmail.com

________________________________


Yau Juma'a 17/12/2021 Yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Ya'aqoub Zakzaky (H) sun gabatar da Zikira na tunawa da Shekaru 6 da kisan kiyashin Zaria da ya gudana a 2015.


Wakilin yan uwa musulmi Malam Qaseem Shehu Shinkafi ne ya gabatar da jawabi akan Waqi'ar Zaria. A jawabin nashi ya jajantawa Yan uwa wannan mummunan musiba da tarihi ba zai manta da ita ba madamar duniya na wanje.


Malamn Qaseem ya bayyana waki'ar Zaria da cewa ranekune (ranekun 12-24) a matsayin ranar da aka dan Adam ya kashe dan Adam,kisa na rashin mutunci,rashin Imani da rashin mutuntaka!


Malam Qaseem Shehu ya ambaci wasu abubuwan da suka faru,kuma ya tambayi azzalummai nasarar da suka samu a wannan mummunan aikin ta'addanci da suka gabatar! "Na'am,kunyi kisa ga wadanda Allah ya rabauta da Matsayi na musamman,matsayi na Shahada,duk dan gwagwarmaya gurinsa ya cika yana Shahidi! Saboda haka babu nasara da azzalummai suka samu" Inji Malam Qaseem Shehu Shinkafi.


A bangaren Yan uwa kuma Malamin ya kirayi Yan uwa da su tsayu kyam da gaske akan wannan tafarki,yan uwa su nemi Sabati,su nemi kusanci zuwa ga Allah,su gyara dabi'unsu domin neman uzuri a wurin Allah.


Malam Rabi'u Mainasara ne ya kammala da addu'a aka sallami yan uwa.


#neverforget

#neverforgive

#ZariaGenocide

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post