Siddiqai uku aka sani a duniyar Muslunci, in aka cire Annabawa (A.S)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

IDAN KA CIRE IMAM ALI (A.S) CIKIN AL'UMMAR ANNABI (S.A.W.W) BABU WANI SIDDIQI SAI DAI NA QARYA

Da yawa ana jin kalmar (SIDDIQ) amma ba a san ma'anarta ba, domin wasu sun dauka laqabi ne wanda ake laqabawa wanda aka ga dama, alhali ba haka abin yake ba.

Kalmar Siddiq tana nufin mai tsananin gaskata Allah da Manzonsa (S.A.W.W) ne, idan ya zamana Allah zaiyi umarni ko kuma ManzonSa (S.A.W.W) amma a sami shakku ko bijirewa tare da mutum, to, ba zai taba zama siddiqi ba.

Sannan kuma ma ba wani ne ke laqabawa wani wannan kalma ko wani ya laqabawa kansa da kansa ba, a'a, Allah ne da Manzonsa (S.A.W.W) suke sanya wannan suna ga wanda suka so bisa cancantarsa.

Za mu kawo misali domin musan lalle Allah ne da Manzo ke sanya wannan suna. Ga misali nan tafe insha Allahu.

Allah (S.W.A) na fada cikin Alqur'ani game da Annabi Idris (A.S) cewa;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ إِدۡرِيسَۚ إِنَّهُۥ كَانَ صِدِّيقٗا نَّبِيّٗا (٦٥)

" KUMA KU AMBATA CIKIN LITTAFIN IDRIS, LALLE SHI YA KASANCE SIDDIQI NE KUMA ANNABI."

        (Suratul-Maryam:56)

Anan Allah ne da kansa ya ambaci Annabinsa Idris (A.S) cewa siddiqi ne bayan matsayinsa na Annabtaka. Wanda hakan ke nuna mana ba lalle ne ya zama dukkan Annaba (A.S) na da wannan matsayi ba, domin cikin nasu ma akwai fifiko.

Kamar hakane ya zama cikin dukkan sahabban Manzanni (A.S) akwai fifiko tsakaninsu kamar yadda Allah ya fifita tsakanin AnnabawanSa (A.S). Ga misali daga Manzon Allah (S.A.W.W) kamar haka;

وَ عَنْ أَبِي لَيْلَى قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ الصِّدِّيقُونَ ثَلَاثَةٌ حَبِيبٌ النَّجَّارُ مُؤْمِنُ آلِ يس- الَّذِي قَالَ‏ يا قَوْمِ اتَّبِعُوا الْمُرْسَلِينَ‏ وَ حِزْقِيلُ مُؤْمِنُ آلِ فِرْعَوْنَ الَّذِي قَالَ‏ أَ تَقْتُلُونَ رَجُلًا أَنْ يَقُولَ رَبِّيَ اللَّهُ‏ وَ عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ وَ هُوَ أَفْضَلُهُمْ.

An karbo daga Abu Laila yace: Manzon Allah (S.A.W.W) yace:

" SIDDIQAI GUDA UKU NE, HABIBUN-NAJJAR MUMINU AALI YASEEN, WANDA YACE: 

" YAA KU MUTANE KUBI MANZANNI."

DA HIZQEELU MUMININ IYALAN FIR'AUNA WANDA YACE:

" YANZU (haka kawai) ZA KU KASHE MUTUM DON YACE: " UBANGIJINA SHINE ALLAH ?"

DA ALIYU BN ABIY 'DALIB, KUMA SHINE MAFIFICINSU (kamar yadda na zama mafifi cikin Annabawa) ."

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏89، ص: 296

Wannan ita ce shaida daga bakin da ba ya qarya, wato fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S.A.W.W). Wannan dalili yasa aka sami riwaya cikin Sunan na Ibn Majah inda yake cewa;

125- حدثنا محمد بن إسماعيل الرازي حدثنا عبيد الله بن موسى أنبأنا العلاء بن صالح عن المنهال عن عباد بن عبد الله قال: قال علي أنا عبد الله وأخو رسوله صلى الله عليه وسلم وأنا الصديق الأكبر لا يقولها بعدي إلا كذاب صليت قبل الناس بسبع سنين.

Muhammad Bn Isma'il Al-Raazeey ya bamu labari, Ubaidul-Lah Bn Musa ya bamu labari, Al-Alaa'i Bn Salih ya bamu labari daga Minhaal, daga Ubbadu Bn Abdullahi yace: Aliyu yace:

" NI BAWAN ALLAH NE KUMA 'DAN'UWAN MANZONSA (S.A.W.W), KUMA NINE SIDDIQI MAFI GIRMA ! BABU WANI BAYANA DA ZAI FADE TA (cewa shi siddiqi ne) SAI DAI MAQARYACI ! NAYI SALLAH SHEKARA SHIDA KAFIN MUTANE (in ka cire Annabi da Nana Khadijah)."

(Sunan-Ibn Majah, kitabul-Muqaddima, babun fadha'ilu As'habun-Nabiyyi, babin munaqibu Aliyu Bn Abiy 'Dalib, hadisi mai lamba 125)

MADALLAH DA WANNAN BUSHARA TA ALLAH DA MANZONSA (S.A.W.W)

 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      (08137925034)

28th December, 2021/ 23rd Jimada-Ulah, 1443.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah ya saka DA Alkhairi.
    Mun qaru sosai DA sanin wanene haqiqanin siqqidi daga bakin ma'aiki.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post