Mu'ujizozin Isah Al-Masihu Dan Maryama (A.S)


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

YANA RAYAR DA MATATTU TARE DA YIN HALITTA DA IZNIN ALLAH

Tarihin haihuwar Annabi Isah Al-Masihu (A.S) bata zama boyayyiya ba domin Allah ya kawo mana shi cikin Alqur'ani mai bada labarin gaskiya abin gaskatawa. Sannan kuma Isah (A.S) ya zo ne a matsayin Annabi Manzo kuma mai bayar da busharar zuwan Annabin qarshe kuma shugaban dukkan Annabawa da Manzanni (A.S) wato Annabi Muhammad (S.A.W.W).

Annabi Isah (A.S) ya kebantu da wasu abubuwa ko kuma mu'ujizozi da suka sha bamban da sauran mu'ujizozin sauran Annabawa (A.S), domin yazo da mu'ujizozin da wani Annabi bai zo da irinsu ba.

MU'UJIZOZINSA (A.S)

Yana daga cikin mu'ujizozinsa yin magana tun yana jariri akan shinfidar goyonsa kamar yadda yazo cikin ayoyin dake biye. Kuma hakan ya faru ne a daidai lokacin data haife shi kuma take tsoron zargi daga mutanenta yayin data haife shi. Shine ya kiraye ta kamar haka;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 

" فَنَادَىٰهَا مِن تَحۡتِهَآ أَلَّا تَحۡزَنِي قَدۡ جَعَلَ رَبُّكِ تَحۡتَكِ سَرِيّٗا (٤٢) وَهُزِّيٓ إِلَيۡكِ بِجِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ تُسَٰقِطۡ عَلَيۡكِ رُطَبٗا جَنِيّٗا (٥٢)

فَكُلِي وَٱشۡرَبِي وَقَرِّي عَيۡنٗاۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ ٱلۡبَشَرِ أَحَدٗا فَقُولِيٓ إِنِّي نَذَرۡتُ لِلرَّحۡمَٰنِ صَوۡمٗا فَلَنۡ أُكَلِّمَ ٱلۡيَوۡمَ إِنسِيّٗا (٦٢ )

" SAI YA KIRAYE TA DAGA QARQASHINTA (cewa) KADA KIYI BAQIN CIKI, HAQIQA UBANGIJINKI YA SANYA MIKI WANI MARMARO A QARQASHINKI.

KUMA KI GIRGIZA KUTUTTUREN DABINO ZUWA GARE KI ZAI ZUBU A KANKI YANA NUNANNE MAI DADI.

KUMA KICI KISHA KIJI SANYIN IDANUWA, IDAN KUMA KI KAGA WANI DAGA CIKIN 'YAN ADAM (wanda zai tuhume ki) KICE MASA: " LALLE NI INA YIN NAYI BAKANCEN AZUMI GA MAI RAHMA, SABODA HAKA BA ZANYI MAGANA DA WANI 'DAN ADAM BA."

          (Maryam:24-26)

Wadannan sune kalaman farko da suka fara fitowa daga bakin Yesu Al-Masihu (few seconds) bayan haihuwarsa.

Yayin da mutanen gari suka soma tuhumarta game da ganin jaririn yaro alhali basu santa da wani mummunan aiki ba sai tayi nuni zuwa gare shi don ya basu amsa. Shine ya amsa musu kamar haka;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

قَالَ إِنِّي عَبۡدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِيَ ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلَنِي نَبِيّٗا (٠٣ ) وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيۡنَ مَا كُنتُ وَأَوۡصَٰنِي بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمۡتُ حَيّٗا ( ١٣ ) وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَتِي وَلَمۡ يَجۡعَلۡنِي جَبَّارٗا شَقِيّٗا (٢٣) وَٱلسَّلَٰمُ عَلَيَّ يَوۡمَ وُلِدتُّ وَيَوۡمَ أَمُوتُ وَيَوۡمَ أُبۡعَثُ حَيّٗا ( ٣٣)

" YACE: " NI BAWAN ALLAH NE AN BANI LITTAFI KUMA AN SANYA NI ANNABI.

KUMA AKA SANYA NI MAI ALBARKA A DUK INDA NAKE, KUMA AKAYI MIN WASIYYA GAME DA (yin) SALLAH DA (bayar) ZAKKAH MATUQAR INA DA RAI.

KUMA MAI BIYAYYA GA MAHAIFIYATA (wanda hakan ke nuna cewa ba shi da uba) KUMA BAI ZANYA NI MAI TSAURIN KAI KO RASHIN RABO BA.

KUMA AMINCI YA TABBATA A GARE NI A RANAR DA AKA HAIFE NI DA RANAR DA NAKE MUTUWA DA KUMA RANAR DA NAKE TASHI RAYAYYE."

         (Maryam:30-33)

Wadannan ayoyi sun qara fitar mana da mu'ujizozinsa na yin magana tare da cewa shi Uwa kadai yake da ita babu Uba gare shi, sabanin yadda sauran Annabawa ke da Uwa da Uba.

YIN HALITTAR SURORI DA IZNIN ALLAH

Annabi Isah Al-Masihu ruhin Allah ya kebanto da wata mu'ujiza ta yin halitta da rayar da matattu da iznin Allah Ubangijinsa kamar yadda yazo a maganarsa cikin ayoyin dake biye;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

وَرَسُولًا إِلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ أَنِّي قَدۡ جِئۡتُكُم بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ أَنِّيٓ أَخۡلُقُ لَكُم مِّنَ ٱلطِّينِ كَهَيۡـَٔةِ ٱلطَّيۡرِ فَأَنفُخُ فِيهِ فَيَكُونُ طَيۡرَۢا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۖ وَأُبۡرِئُ ٱلۡأَكۡمَهَ وَٱلۡأَبۡرَصَ وَأُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۖ وَأُنَبِّئُكُم بِمَا تَأۡكُلُونَ وَمَا تَدَّخِرُونَ فِي بُيُوتِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ (٩٤ )

" KUMA MANZO ZUWA GA BANI ISRA'IL, (yake ce musu) : LALLE NI NA ZO MUKU DA AYOYI DAGA UBANGIJINKU (wanda ya halicce ku) , KUMA NI INA HALITTA MUKU SIFFAR TSUNTSU DAGA LAKA KUMA NA BUSA MASA RAI YA KASANCE TSUNTSU (ya tashi sama) DA IZNIN ALLAH. KUMA INA WARKAR DA MAKAFI DA MASU KUTURTA KUMA NA RAYAR DA MATATTU DA IZNIN ALLAH. KUMA INA BAKU LABARI DA ABINDA KUKE CI (ba tare dana ganshi ba) DA MA ABINDA KUKE AJIYEWA CIKIN GIDAJENKU (ba tare dana gani ko wani ya bani labari ba). LALLE CIKIN HAKA AKWAI AYOYI GARE KU IN HAR KUN KASANCE MASU IMANI."

               (Al-Imran:49)

Kamar yadda ya fada da bakinsa cewa duk abinda yake yi dinnan da iznin Allah yake yi, sai Allah da kansa ya qara fada don su sani muma mu sani cewa da iznin Allah yake yin komai saboda matsayinsa.

إِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱذۡكُرۡ نِعۡمَتِي عَلَيۡكَ وَعَلَىٰ وَٰلِدَتِكَ إِذۡ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِ تُكَلِّمُ ٱلنَّاسَ فِي ٱلۡمَهۡدِ وَكَهۡلٗاۖ وَإِذۡ عَلَّمۡتُكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَۖ وَإِذۡ تَخۡلُقُ مِنَ ٱلطِّينِ كَهَيۡـَٔةِ ٱلطَّيۡرِ بِإِذۡنِي فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيۡرَۢا بِإِذۡنِيۖ وَتُبۡرِئُ ٱلۡأَكۡمَهَ وَٱلۡأَبۡرَصَ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡ تُخۡرِجُ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡ كَفَفۡتُ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ عَنكَ إِذۡ جِئۡتَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ (٠١١)

" YAYIN DA ALLAH YACE: YAA ISAH 'DAN MARYAMA ! KA TUNA NI'IMATA A KANKA DA KUMA KAN MAHAIFIYARKA YAYIN DANA QARFAFEKA DA RUHI MAI QARFI, KANA YIN MAGANA DA MUTANE CIKIN SHIMFIDAR GOYO DA KUMA GIRMANKA. DA KUMA LOKACIN DANA SANAR DA KAI LITTAFI DA HIKIMA DA ATTAURA DA LINJILA. DA KUMA YAYIN DA KAKE HALITTA SIFFAR TSUNTSU DAGA LAKA DA INZINA, KUMA KAYI HURI CIKINSA SAI YA ZAMA TSUNTSU DA IZNINA, KUMA KAKE WARKAR DA MAKAFI DA MASU KUTURTA DA IZNINA. DA KUMA LOKACIN DA KAKE FITAR DA MATATTU DA IZNINA, DA KUMA LOKACIN DANA KANGE BANI ISRA'ILA DAGA GARE KA YAYIN DA KAZO MUSU DA HUJJOJI BAYYANANNU HAR WADANDA SUKA KAFIRTA DAGA CIKINSU SUKA CE: " BA KOMAI BANE WANNAN FACE SIHIRI BAYYANANNE."

         (Ma'idah:110)

YA ROQI ALLAH YA SAUKAR DA ABINCI DAGA SAMA

Yana daga cikin qarin mu'ujizozinsa roqon Allah daya saukarwa al'ummarsa abinci nunanne daga sama ba suka ci ba tare da sun sha wahalar girkawa ba.

قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ ٱللَّهُمَّ رَبَّنَآ أَنزِلۡ عَلَيۡنَا مَآئِدَةٗ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ تَكُونُ لَنَا عِيدٗا لِّأَوَّلِنَا وَءَاخِرِنَا وَءَايَةٗ مِّنكَۖ وَٱرۡزُقۡنَا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّٰزِقِينَ (٤١١ )

" ISAH 'DAN MARYAMA YACE: YAA ALLAH UBANGIJINMU KA SAUKAR MANA DA DARBA DAGA SAMA ZUWA GARE MU DOMIN YA ZAMA RANAR BIKI (food festival day) GANA FARKONMU DANA QARSHENMU , KUMA (ya zama wata) AYA DAGA GARE KA (wanda ko mai sihiri ba zai iya yinsa ba), KUMA KA AZURTA MU DOMIN KAINE MAFI ALKHAIRIN MASU AZURTAWA."

             (Ma'idah:114)

Allah ya amsa masa wannan roqo nasa ya saukar musu abinci dafaffe daga sama albarkacin Isah Al-Masihu (A.S).

AMINCI YA TABBATA A GARE KA RANAR DA AKA HAIFE KA DA RANAR DAKA MUTU DA KUMA RANAR DA ZA A TASHE KA KANA RAYAYYE !!!

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        (08137925034)

25th December, 2021/ 15th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post