ANA YIN BULALA MARAR ADADI GA WANDA YA BADA SHAIDAR QARYA
Shaida wani ginshiqi ne a muslimci wanda ke kawo daidaito cikin al'umma. Idan ya zama babu shaida da shaidu za a sami barna da ta'addanci cikin qasa, shi yasa in aka sami shaidar qarya al'amra kan tabarbare.
Allah (S.W.A) yayi magana game da bayar da shaidar gaskiya a gurare da da dama cikin Al-Qur'ani, ga misalin wasu daga cikinsu.
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
الآيات البقرة - " وَ مَنْ أَظْلَمُ مِمَّنْ كَتَمَ شَهادَةً عِنْدَهُ مِنَ اللَّهِ و قال تعالى وَ لا يَأْبَ الشُّهَداءُ إِذا ما دُعُوا[1]
" WANENE MAFI ZALUNCI KAMAR WANDA YA BOYE SHAIDAR (gaskiya) A WAJENSA DAGA ALLAH ?
Kuma Allah (T) yace: " KUMA KADA MASU BAYAR DA SHAIDA SU QI (zuwa) IDAN AN KIRA SU."
Wadannan ayoyi biyu suna nuna mana ne babu mutum mafi zalunci kamar wanda yasan gaskiya amma ya boye ta. Kuma haramun ne ga wanda yasan abu amma ya qi zuwa in har an neme shi don bayar da shaida.
و قال سبحانه-" وَ لا تَكْتُمُوا الشَّهادَةَ وَ مَنْ يَكْتُمْها فَإِنَّهُ آثِمٌ قَلْبُهُ وَ اللَّهُ بِما تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ[2]
Kuma Allah (S.W.A) yace:
" KUMA KADA KU BOYE SHAIDA (alhali kuna sane), DUK WANDA YA BOYE TA HAQIQA YA 'DAU ZANUBI A KANSA, KUMA ALLAH MASANI NE GAME DA ABINDA KUKE AIKATAWA."
النساء - " يا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ بِالْقِسْطِ شُهَداءَ لِلَّهِ وَ لَوْ عَلى أَنْفُسِكُمْ أَوِ الْوالِدَيْنِ وَ الْأَقْرَبِينَ إِنْ يَكُنْ غَنِيًّا أَوْ فَقِيراً فَاللَّهُ أَوْلى بِهِما فَلا تَتَّبِعُوا الْهَوى أَنْ تَعْدِلُوا وَ إِنْ تَلْوُوا أَوْ تُعْرِضُوا فَإِنَّ اللَّهَ كانَ بِما تَعْمَلُونَ خَبِيراً." [3]
" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! KU KASANCE MASU TSAYUWA DA ADALCI MASU BAYAR DA SHAIDA DOMIN ALLAH, KO DA AKAN KAWUKANKU NE KO AKAN MAHAIFA DA MAKUSANTA. IDAN YA KASANCE (wanda ake bayar da shaidar a kansa) MAWADACI NE KO MABUQACI TO, ALLAH NE MAFI CANCANTA DASU. KADA KUBI SON ZUCIYARKU (wajen bayar da shaida) KU KASA YIN ADALCI. IDAN KUKA KARKATA KO KUKA KAUDA KAI (wajen fadar gaskiya), TO, LALLE ALLAH YA KASANCE MAI BADA LABARI GAME DA ABINDA KUKE AIKATAWA."
المائدة - " يا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ لِلَّهِ شُهَداءَ بِالْقِسْطِ وَ لا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَآنُ قَوْمٍ عَلى أَلَّا تَعْدِلُوا اعْدِلُوا هُوَ أَقْرَبُ لِلتَّقْوى." [4]
" YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! KU KASANCE MASU TSAYUWA DOMIN ALLAH MASU BAYAR DA SHAIDA DA ADALCI, KADA QIYAYYAR WASU TASA BA ZA KUYI ADALCI BA, KUYI ADALCI SHINE MAFI KUSA DA TSORON ALLAH."
Da Allah ya tashi yabon mutanen kirki da kuma siffantasu sai yace:
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
الفرقان - " وَ الَّذِينَ لا يَشْهَدُونَ الزُّورَ." [5]
" KUMA SUNE WADANDA BADA SHAIDAR ZURR (shaidar qarya)."
Kuma yace:
المعارج - " وَ الَّذِينَ هُمْ بِشَهاداتِهِمْ قائِمُونَ." [6].
" SUNE WADANDA KE TSAYUWA WAJEN BAYAR DA SHAIDARSU (ta gaskiya)."
(1) سورة البقرة: 22.
(2) سورة البقرة: 283.
(3) سورة النساء: 135.
(4) سورة المائدة: 8.
(5) سورة الفرقان: 72.
(6) سورة المعارج: 33.
Wadannan kadan ne daga cikin ayoyin da su kayi gargadi game da bayar da shaidar gaskiya. Amma duk da haka sai ya zama wadanda ma ya kamata ace su suke yi umarni game da bin wadannan ayoyi sai ya zama sune masu bayar da shaidar qarya saboda wata qiyayya dake cikin zukatansu don cimma muradunsu na duniya.
Bayan wadannan ayoyi da muka kawo za mu bibiyi bayansu da qarin wasu kadan daga cikin hadisai don qarin bayani kansu. Ga su kamar haka:
غوالي اللئالي رُوِيَ فِي كِتَابِ التَّكْلِيفِ لِابْنِ أَبِي الْعَزَاقِرِ رَوَاهُ عَنِ الْعَالِمِ ع أَنَّهُ قَالَ: مَنْ
شَهِدَ عَلَى مُؤْمِنٍ بِمَا يَثْلِمُهُ أَوْ يَثْلِمُ مَالَهُ أَوْ مُرُوَّتَهُ سَمَّاهُ اللَّهُ كَذَّاباً وَ إِنْ كَانَ صَادِقاً وَ مَنْ شَهِدَ لِمُؤْمِنٍ مَا يُحْيِي بِهِ مَالَهُ أَوْ يُعِينُهُ عَلَى عَدُوِّهِ أَوْ يَحْفَظُهُ دَمَهُ سَمَّاهُ اللَّهُ صَادِقاً وَ إِنْ كَانَ كَاذِباً[7].
Ya zo cikin Al-Gawwaalil-Lil-Aaliy, an riwaito cikin littafin Takleef na Ibn Abiy Azaaqir, kuma ya riwaito daga masani (A.S) yace:
" DUK WANDA YA BAYAR DA SHAIDA AKAN MUMINI DA ABINDA ZAI KUBUTAR DASHI KO KUMA YA KUBUTAR DA DUKIYARSA KO MUTUNCINSA, TO, ALLAH ZAI AMBACE SHI (mai bayar da shaidar) MAQARYACI KO DA KUWA SHI MAI GASKIYA NE. KUMA WANDA YA YIWA MUMINI SHAIDA DA ABINDA ZAI RAYAR DA DUKIYARSA DA SHI KO KUMA YA TAIMAKE SHI AKAN MAQIYINSA KO KUMA YA TSARE MASA JININSA, TO, ALLAH ZAI AMBACE MAI GASKIYA KO DA KUWA YA KASANCE MAQARYACI NE."
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج101، ص: 310
Ma'anar wannan hadisi shine, duk wanda ya tsayawa azzalumai a matsayin shaidansu kan wani mumini, to, sunan wannan shaida maqaryaci ko da kuwa an san shi da gaskiya, domin mumini ba zai aikata abinda Allah ba ya so ba. Haka kuma duk wanda ya tsaya a matsayin shaida ga wani mumini, to, sunan wannan shaidai shine mai gaskiya ko da kuwa an san shi da qarya a baya, domin Allah ne yayi aiki da shi wajen bawa mumini kariya.
Babban misali shine; Wadanda suka tsaya a matsayin shaidun Sayyid Zakzaky (H) da wadanda suka tsaya a matsayin shaidun hukumar zalunci ta Buhari. Ko kuma wadanda suka tsayawa Sheikh Abdul-Jabbar da wadanda suka tsayawa gwamnatin zalunci ta Kano masu hadin qwiwa da malaman Majah.
ثواب الأعمال ابْنُ الْمُتَوَكِّلِ عَنِ الْحِمْيَرِيِّ عَنِ ابْنِ أَبِي الْخَطَّابِ عَنِ ابْنِ مَحْبُوبٍ عَنْ أَبِي أَيُّوبَ عَنْ سَمَاعَةَ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: شُهُودُ الزُّورِ يُجْلَدُونَ جَلْداً
لَيْسَ لَهُ وَقْتٌ وَ ذَلِكَ إِلَى الْإِمَامِ وَ يُطَافُ بِهِمْ حَتَّى يُعْرَفُوا فَلَا يَعُودُوا قَالَ فَقُلْتُ لَهُ فَإِنْ تَابُوا وَ أَصْلَحُوا تُقْبَلُ شَهَادَتُهُمْ بَعْدَهُ قَالَ إِذَا تَابُوا تَابَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ وَ قُبِلَتْ شَهَادَتُهُمْ بَعْدُ.
Ya zo cikin Sawabul-A'amaal na Ibn Mutawakkal, daga Himyariyyi, daga Ibn Abiy Khaddabi, daga Ibn Mahbuub, daga Abu Ayuba, daga Samaa'ata, daga Abu Abdullah (A.S) yace:
" MASU BAYAR DA SHAIDAR ZURR (shaidar qarya) ANA YI MUSU BULALA, BULALAR DA BATA DA IYAKA, KUMA HAKAN NA KAN LIMAMI NE. KUMA ZA A KEWAYA DASU (cikin jama'a) HAR SAI (kowa) YA SANSU (maqaryata ne), BA ZA SU QARA DAWOWA (amatsayin shaidu ga wani) BA. Yace; sai nace masa: " Idan sun tuba kuma suka kyautata za a karbi shaidarsu bayansa (bayar shaidar da suka bayar ta qarya) ?" Yace:
" IDAN SUN TUBA ALLAH ZAI KARBI TUBARSU, KUMA ZA A KARBI SHAIDARSU DAGA BAYA."
ثواب الأعمال و عقابها ص 203.
NB:- Maganar cewa za ayi bulala marar adadi ga masu bayar da shaidar zurr (qarya) kuma limami ne zai yi, ba ana nufin limamin masallaci bane, a'a limamin dake jagorantar muslimci da musulmai a aiki ba a suna ba, wato wanda ke jagorantar al'umma wanda ke aiki da littafin Allah ba kwansitushan ba. Sannan kuma zabi ne ga shi limamin wajen yin bulalar, wato ba wai yayi ko ya bari ba, a'a, adadin bulalar da zai yi ta danganta ne da matsayin shaidar da aka bayar. Idan an bada shaidar qarya wacce za ta taimaka a kashe mumini ko halakar masa da dukiyarsa za ta bambanta da shaidar da aka bayar wacce fada kawai ko zagi za a yiwa wanda aka bada shaidar a kansa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
18th December, 2021/ 13th Jimada-Ulah, 1443.