Ko da an kashe Sheikh Abduljabbar iliminsa ba zai dai walwala cikin duniyar Muslumci ba, da kisa na hana wanzuwar abu sa addinin nan bai zo garemu ba



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DA KISA WANI ABU NE DA YANZU BABU LABARIN AHLUL-BAIT (A.S)

Babban burin maqiya Allah maqiya Manzonsa (S.A.W.W) shine su shafe hasken dukkan wani mai da'awa irin ta Manzon Allah (S.A.W.W), da kuma tabbatar da aqidar kafiran farko ta fifita Gumaka akan wanda ke da ikon kashewa da rayawa.

Sune a kullum suke nuna cewa Annabi (S.A.W.W) kamar kowa yake, saboda haka yakan iya yin daidai kuma yakan iya aikata kuskure har ayi masa gyara.

Sun kashe Imam Hussaini (A.S) ne don su shafe hasken muslimci wanda Iyalan Annabi (A.S) suka zama sune masu haskaka shi, amma Allah bai yarje musu ba, sai ga shi yanzu dasu ake tinqahu. Su kuwa masu wannan aiki sun zama abin qyama kuma zuriya mafi muni da sharri.

Sunyi nufin kashe Sayyid Zakzaky (H) wanda ke da'awar a dawo kan littafin Allah ta hanyar riqo da wasiyyan Manzon Allah (S.A.W.W), sai dai Allah ya nuna gazawarsu.

Yanzu kuma sun juyo kan wanda ke qoqarin ruguza ginin qarya wanda ana gina shi don shafe ilimin haqiqa wanda yazo daga fiyayyen halitta.

An dade ana yiwa mutane tatsuniyar qarya da cewa ita ce fa addini, kuma mutane sun tafi akan haka sakamakon rashin karatunsu. Sai kuma ga shi Allah ya tayar masoyin Manzonsa (S.A.W.W) masoyin iyalan gidan Manzonsa (A.S) , wato Amirul-Wa'izeena Sheikh Abdul-Jabbar Bn Sheikh Nasiru Al-Kabariy.

Roqonmu a kullum shine Allah ya kare wannan bawan Allah daga makircin azzalumai 'yan maja qawayen azzalumai bayin Yahudawa.

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 

Daga wakilamu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

14th December, 2021/ 9th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post