@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MUMINE KADAI KE KARANTATA A KULLUM CIKIN SALLOLINSA
Suratul-Ikhlaas wacce aka fi saninta da (Qulhuwal-Lahu) sura ce mai girman falala daga cikin surorin Al-Qur'ani mai tsarki. Babu wata surah wacce za ka karantata cikin sallarka mafi girma fiye da ita bayan Fatihatul-Kitaab. Idan kuwa karantawa ne haka ba a cikin sallah ba, to, ta fi komai cikin Qur'ani.
An samo riwayoyi masu yawa da suka yi magana kan falalarta, amma dai za mu taqaita kan uku daga cikinsu don gudun tsawaitawa. Ga su kamar haka insha Allahu;
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
َ(1)- عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص أَ يَعْجِزُ أَحَدُكُمْ أَنْ يَقْرَأَ كُلَّ لَيْلَةٍ ثُلُثَ الْقُرْآنِ قَالُوا وَ مَنْ يُطِيقُ ذَلِكَ قَالَ قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ ثُلُثُ الْقُرْآنِ."
An karbo daga Abdullahi Bn Mas'ud yace: Manzon Allah (S.A.W.W) yace:
" YANZU 'DAYANKU ZAI GAZA KARANTA 'DAYA BISA UKU NA QUR'ANI A KOWANNE DARE ?" Suka ce: " Wanene kuwa zai iya haka." Yace:
" QULHUWALLAHU AHD 'DAYA CIKIN KASHIN UKU NE NA QUR'ANI."
معاني الأخبار ص 191
Ma'ana duk wanda ya karanta Qulhuwal-Lahu uku tamkar ya karanta kashi daya ne daga cikin kashi uku na Qur'ani. In da kuwa zai karantata sau uku, to, yana daidai da ya karanta Qur'ani ne gaba dayansa.
(2)- ثواب الأعمال بِالْإِسْنَادِ عَنِ ابْنِ الْبَطَائِنِيِّ عَنْ سَيْفِ بْنِ
عَمِيرَةَ عَنْ مَنْصُورِ بْنِ حَازِمٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: مَنْ مَضَى بِهِ يَوْمٌ وَاحِدٌ فَصَلَّى فِيهِ خَمْسَ صَلَوَاتٍ وَ لَمْ يَقْرَأْ فِيهَا بِقُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ قِيلَ لَهُ يَا عَبْدَ اللَّهِ لَسْتَ مِنَ الْمُصَلِّينَ."
Ya zo cikin Thawabul-A'amaal da isnadinsa daga Ibn Badaa'iniyyi, daga Saifi Bn Ameerata, daga Mansur Bn Haazim, daga Abu Abdullah (A.S) yace:
" DUK WANDA WATA RANA TA KUBUCE MASA WACCE YA SALLACI SALLOLI BIYAR AMMA BAI KARANTA QULHUWALLAHU AHD A CIKINTA BA, KUCE MASA YAA KAI BAWAN ALLAH BAKA KASANCE CIKIN MASALLATA BA."
ثواب الأعمال ص 115.
Kun san kuwa Allah ya bamu labarin abinda 'yan wutar saqar za suce yayin da aka tambaye su cewa menene ya shigar daku cikin Saqar ? Za suce: " BAMU KASANCE CIKIN MASALLATA BA."
Kenan makomars wanda ba ya karanta Qulhuwal-Lahu cikin sallarsa a qarshe za ta kasance shiga wuta ne
(3)- التوحيد أَحْمَدُ بْنُ الْحُسَيْنِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ سُلَيْمَانَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ الرَّقَاشِيِّ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ سُلَيْمَانَ عَنْ يَزِيدَ الرِّشْكِ عَنْ مُطَرِّفِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ عَنْ عِمْرَانَ بْنِ حُصَيْنٍ أَنَّ النَّبِيَّ ص بَعَثَ سَرِيَّةً وَ اسْتَعْمَلَ عَلَيْهَا عَلِيّاً ع- فَلَمَّا رَجَعُوا سَأَلَهُمْ فَقَالُوا كُلُّ خَيْرٍ غَيْرَ أَنَّهُ قَرَأَ بِنَا فِي كُلِّ الصَّلَاةِ بِقُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ فَقَالَ يَا عَلِيُّ لِمَ فَعَلْتَ هَذَا فَقَالَ لِحُبِّي لِقُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ فَقَالَ النَّبِيُّ ص مَا أَحْبَبْتَهَا حَتَّى أَحَبَّكَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ.
Ya zo cikin Tauheed na Ahmad Bn Hussaini daga Muhammad Bn Sulaiman , daga Muhammad Bn Yahya, daga Muhammad Bn Abdullahi Ar-Raqaashiyyi, daga Ja'afar Bn Sulaiman , daga Yazeedar-Rishki, daga Mudarrifi Bn Abdullahi, daga Imraana Bn Hussain, cewa Annabi (S.A.W.W) ya aika wata tawaga ta mayaqa (SARIYYAH) sai ya shugabantar da Aliyu a kanta. Yayin da suka dawo sai ya tambaye su (game da sha'anin wannan tafiya tasu). Sai suka ce:
" Komai lafiya, sai dai kawai shi ya kasance yana karanta mana Qulhuwal-Lahu ce cikin kowacce sallah. Sai yace:
" YAA ALIYU ! DON MENENE KA AIKATA HAKA ?" Yace: " Saboda soyayyata ga Qulhuwal-Lahu Ahd. " Sai Annabi (S.A.W.W) yace:
" BA KA SOTA BA HAR SAIDA ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA SO KA."
التوحيد: 54.
Wannan shine kadan daga falalar karanta suratul-Ikhlaas, ya bamu ikon dabbaquwa kan karantata.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
28th December, 2021/ 23rd Jimada-Ulah, 1443.
crown casino reviews 2021 - Casinoofib fun88 soikeotot fun88 soikeotot 1XBET 1XBET 코인카지노 코인카지노 757Free Pragmatic Play Slot Joker Online - VieCasino.com
ReplyDelete