Fa'idojin tsaftace muhalli a Musulunci


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BARIN YANAR GIZO CIKIN 'DAKI NA GADAR DA TALAUCI

Duk wani abinda kaga an kawo shi mai muhimmanci a matsayin wani ilimi da ake koyar da al'umma ya samo asali ne daga littafan muslimci.

Ko cikin makarantu na primary ana koyar da wani darasi mai suna ilimin kiwon lafiya (health education), sai dai a tsammanin wasu wani ilimi ne wanda Bature yazo dashi, alhali ba haka bane, ilimi ne wanda ya samo shi cikin littafan muslimci wanda akayi watsi da koyarwarsa, shine shi (Bature) ya tattaro mana na ana ganinsa a matsayin mafifi a tsabta wanda ke koyar dashi.

Ga wasu riwayoyi nan wadanda za mu kawo daga cikin littafan muslimci ko zai amfanar da mai buqata.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

(1)- الأمالي للصدوق فِي مَنَاهِي النَّبِيِّ ص أَنَّهُ قَالَ: لَا تُبَيِّتُوا الْقُمَامَةَ فِي بُيُوتِكُمْ وَ أَخْرِجُوهَا 

نَهَاراً فَإِنَّهَا مَقْعَدُ الشَّيْطَانِ‏."

Ya zo cikin Amali na Sudduq game da abubuwan da Annabi (S.A.W.W) yayi hani a kansu, lalle shi yace:

" KADA KUBAR SHARA (dust) CIKIN GIDAJANKU, KU FITAR DASHI (waje) DA RANA, DOMIN SHI MAZAUNIN SHAIDAN NE."

أمالي الصدوق: 254، و القمامة: الكناسة.

(2)- قرب الإسناد عَنِ الْيَقْطِينِيِّ عَنِ الْقَدَّاحِ عَنِ الصَّادِقِ ع عَنْ أَبِيهِ عَنْ أَمِيرِ الْمُؤْمِنِينَ ع قَالَ: نَظِّفُوا بُيُوتَكُمْ مِنْ حَوْكِ الْعَنْكَبُوتِ فَإِنَّ تَرْكَهُ فِي الْبَيْتِ يُورِثُ الْفَقْرَ.

Haka kuma ya zo cikin daga Yaqdeeniyyi, daga Qaddahi, daga Sadiq (A.S), daga babansa daga amirul-muminina (Ali (A.S) yace:

" KU TSABTACE GIDAJENKU DAGA YANAR GIZO-GIZO, DOMIN BARINSA CIKIN GIDA (daki) YANA GADAR DA TALAUCI."

قرب الإسناد: 35.

(3)- مكارم الأخلاق: عَنْ سَمَاعَةَ بْنِ مِهْرَانَ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ أَوْ أَبِي الْحَسَنِ ع‏ أَنَّهُ سُئِلَ مِنْ إِغْلَاقِ 

الْأَبْوَابِ وَ إِكْفَاءِ الْإِنَاءِ وَ إِطْفَاءِ السِّرَاجِ قَالَ أَغْلِقْ بَابَكَ فَإِنَّ الشَّيْطَانَ لَا يَفْتَحُ بَاباً وَ أَطْفِئْ سِرَاجَكَ مِنَ الْفُوَيْسِقَةِ وَ هِيَ الْفَأْرَةُ لَا تَحْرِقْ بَيْتَكَ وَ أَكْفِئْ إِنَاءَكَ فَإِنَّ الشَّيْطَانَ لَا يَرْفَعُ إِنَاءً مُكْفَأً.

Sannan kuma ya zo cikin Mukarimul-Akhlaaq: Daga Samaa'ata Bn Mihraana, daga Abu Abdullah ko Abu Hassan (A.S) cewa an tambaye shi game da rufe qofa da lullube (rufe) qwarya (kwanukan abinci) da kuma kashe fitila, yace;

" KA RUFE QOFARKA, DOMIN SHAIDAN BA YA BUDE QOFA, KUMA KA KASHE FITILARKA DAGA BERAYE, DOMIN SHI BERA BA ZAI HUHHUDA MAKA GIDA BA, KUMA KA LULLUBE QWARYARKA (kwanon abinci), DOMIN SHAIDAN BA YA 'DAUKAR QWARYAR DAKE LULLUBE."

مكارم الأخلاق: 147 و 146.

Wannan shine koyarwar muslimci wanda akayi watsi dashi, kuma ana ganin illar yin hakan. Yawanci mutane na cikin talauci ba tare da sanin dalilin hakan ba, wataqila kuwa hakan na faruwa ne sakamakon kaucewa wannan koyarwar. Allah ya amfanar damu daga wannan koyarwar.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda

      (08137925034)

30th December, 2021/ 25th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post