@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SANIN ABUBUWA SHIDA KANSA MUTUM YA TSORACI WUTA IN JI IMAM ALI (A.S)
Sanin Allah a farko shine ginshiqin komai na addinin mutum, domin ta wannan hanya ce za kasan abubuwan da Yake so da wadanda ba ya so. Shi yasa yayin da Allah ya turo Manzonsa (S.A.W.W) sai ya zama farkon umarnin da akayi masa ya isarwa al'umma shine sanin Allah a matsayin abin bauta wanda ya kamata a tsarkake.
Hukuncin bai fara saukowa kan al'umma ba har sai bayan da aka dasa musu tauhudi cikin zukatansu, domin shine matakin farko kafin sanin hukunci.
Yazo daga Imam Ali (A.S) yadda yake nuna cewa matuqar mutum ya tattara abubuwa shida tare dashi, to, haqiqa ba zai taba barin neman Aljannah ba kuma ba zai taba barin jin tsoron wuta ba. Ka ruwayar nan kaman haka:
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
قال علي رضي الله عنه: من جمع ست خصال، لم يدع للجنة مطلبًا، ولا عن النار مهربًا: من عرف الله فأطاعه وعرف الشيطان فعصاه وعرف الحق فاتبعه وعرف الباطل فاتقاه وعرف الدنيا فرفضها وعرف الآخرة فطلبها.
Imam Ali (A.S) yace:
" DUK WANDA YA TATTARA ABUBUWA SHIDA (6) BA ZAI TABA BARIN NEMAN ALJANNAH BA, KUMA BA ZAI TABA BARIN JIN TSORON WUTA BA.
(1)- WANDA YASAN ALLAH KUMA YAYI MASA BIYAYYA.
(2)- KUMA YASAN SHADAN YA SABA MASA.
(3)- KUMA YASAN GASKIYA YA BI TA.
(4)- KUMA YASAN QARYA YA NISANCE TA.
(5)- KUMA YASAN DUNIYA YA YAYI WATSI DA ITA.
(6)- KUMA YASAN LAHIRA YA NEME TA.
(MAWA'IZUS-SAHABAH)
Sanin Allah dayi masa biyayya na qara qaunar lahira da nemanta, domin an san alqawarinSa da ya yiwa bayinsa masu yi masa biyayya, haka kuma wanda yasan Shaidan ya saba masa, to, ba zai taba yarda da tarkons ba don ya san zai kai shi wuta.
Sanin gaskiya da binta siffa ce ta masu tsoron shiga wuta da fatan shiga aljannah, kamar yadda aka san nisantar qarya neman kusanci ne ga aljannah kuma tsoro ne ga wuta.
A kullum duniya kiran mutum take tana nuna masa adonta don ta rudar dashi, wanda ya amsa mata kuwa wuta za ta kai shi, ita kuwa lahira a kullum kiran mutum take yi ta hanyar nuna masa ni'imomin da aka tanadar cikinta ga wanda yabi Allah, sabo haka amsa kiranta neman aljannah ne.
Yaa Allah ya mallakar mana sanin wadannan abubuwa shida (6) ta hanyar tattara su wajen aiki.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
24th December, 2021/ 19th Jimada-Ulah, 1443.