Ciyar da iyali yafi girman lada fiye da ciyar da dukiya a hanyar Allah


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

QUNTATAWA IYALI NA KAWO TAWAYAR DUKIYA

Allah (Ta) ya kawaitar damu wajen ciyar da dukiya domin daukaka addininSa, har ma yace:

" MISALIN WADANDA KE CIYAR DA DUKIYARSU A HANYAR ALLAH KAMAR QWAYA (seed) CE (wacce aka shuka) TA TSIRAR DA ZANGARNIYA BAKWAI, KUMA CIKIN KOWACCE ZANGARNIYAR AKWAI QWAYA 100, KUMA ALLAH NA NINNINKAWA GA WANDA YASO......"

Wannan na nuna mana ne girman ladan ciyar da dukiya a hanyar Allah, amma duk da wannan girman da yake dashi bai kai girman ladan ciyar da iyali ba.

Dalili kuwa shine, shi ciyar dukiya ya hanyar taimakon addini abu ne wanda ake yinsa don neman lada amma ba wanda za a azabtar dakai don ka qi yinsa ba. Idan kaqi yi wani zai yi kuma shi zai samun ladan ba kai ba.

Shi kuwa ciyar da iyali wani haqqi ne da Allah ya dora maka na iyalin da ke qarqashinka, saboda haka idan kaqi ciyar dasu ba ka sauke wannan haqqi ba, kuma Allah zai azantar da kai ta dalilin rashin ciyar dasu.

Wannan dalili yasa a lokacin da Imam Ali da iyalansa (A.S) su kayi azumin nakance (NAZAR) har aka sami nau'in mabuqata uku suka zo bara gidansa bai kwashe dukkan abincin gidan ya bayar ba saboda sanin wannan haqqi na iyalinsa dake kansa. Sai dai ya shawarci iyalan nasa ta hanyar kwadaitarwa kuma suka haqura da yunwar duniya don samun qoshin lahira. Suka debi dukkan abincin nasu suka bayar dashi ga :-

- Miskini,

- Maraya da kuma

- Ribataccen yaqi.

Yazo cikin riwayoyi kamar haka ;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

الأمالي للشيخ الطوسي جَمَاعَةٌ عَنْ أَبِي الْمُفَضَّلِ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ الْعَلَوِيِّ عَنْ حَمْزَةَ بْنِ أَحْمَدَ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ عُمَرَ بْنِ عَلِيٍّ عَنْ عَمِّهِ عِيسَى بْنِ عَبْدِ اللَّهِ عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ ع قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ ص فَقَالَ يَا رَسُولَ اللَّهِ عِنْدِي دِينَارٌ فَمَا تَأْمُرُنِي بِهِ قَالَ أَنْفِقْهُ عَلَى أُمِّكَ قَالَ عِنْدِي آخَرُ فَمَا تَأْمُرُنِي بِهِ قَالَ أَنْفِقْهُ عَلَى أَبِيكَ قَالَ عِنْدِي آخَرُ فَمَا تَأْمُرُنِي بِهِ قَالَ أَنْفِقْهُ عَلَى أَخِيكَ- قَالَ عِنْدِي آخَرُ فَمَا تَأْمُرُنِي بِهِ وَ لَا وَ اللَّهِ مَا عِنْدِي غَيْرُهُ قَالَ أَنْفِقْهُ فِي 

سَبِيلِ اللَّهِ وَ هُوَ أَدْنَاهَا أَجْراً.

Ya zo cikin Amali na Sheikh 'Dusi , jama'a (da dama suk riwato) daga baban Mufaddhal, daga Ja'afar Bn Muhammad, daga Ja'afar Bn Abdullahi l-Alawiy, daga Hamzata Bn Ahmad Bn Abdullahi Bn Muhammad Bn Umar Bn Aliyu , daga baffansa Isah Bn Abdullahi , daga babansa daga kakansa daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A.S) yace: Wani mutum ya zo waje Annabi (S.A.W.W) sai yace: 

" Yaa Ma'aikin Allah ! Akwai Zinari a wajena, wanne umarni kake min a kansa? " Yace:

" KA CIYAR DASHI GA MAHAIFIYARKA." Yace:

" Akwai wani na dabam tare dani, wanne umarni kake yimin a kansa? " Yace:

" KA CIYAR DASHI GA MAHAIFINKA ." Yace:

" Akwai wani kawai, wanne umarni kake yimin game dashi ?" Yace:

" KA CIYAR DASHI GA 'DAN'UWANKA." Yace:

" (Har yanzu) akwai wani (Dinarin) tare dani, wanne umarni kake yimin game dashi? Wallahi bani da wani koma bayansa." Yace:

" KA CIYAR DASHI A HANYAR ALLAH, DOMIN SHINE MAFI QARANCIN LADA."

أمالي الطوسيّ ج 1 ص 391.

Wannan na nuna mana ne cewa in dai girman lada kake so ba neman suna ba, to, ciyar da wadannan shi yafi fiye da yin wani aiki na taimakon addini matuqar wadannan na da buqata.

Sai dai hakan ba yana cewa kada ka taimaki addinin Allah bane bisa dogaro da cewa kai mai iyali ne, domin masu taimakon addinin ba suna yi ne don rashin iyali ba. Idan kaqi yi wasu za suyi, kuma kai kayi hasara ba wani ba.

" IDAN KUKA JUYA BAYA (kuka ce ba za ku taimaki addini ba) ALLAH ZAI CANZA WASU MUTANE BA KU BA, KUMA BA ZA SU KASANCE MISALINKU BA."

Wato sai ya tayar da wasu mutanen a idonku masu ciyar da dukiyarsu a hanyar Allah ba marowata irinku ba.

الخصال ابْنُ الْمُتَوَكِّلِ عَنْ مُحَمَّدٍ الْعَطَّارِ عَنْ جَعْفَرٍ الْفَزَارِيِّ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ سَهْلٍ عَنْ سَعِيدِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ مَسْعَدَةَ عَنْ مُوسَى بْنِ جَعْفَرٍ ع قَالَ: إِنَّ عِيَالَ الرَّجُلِ أُسَرَاؤُهُ فَمَنْ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِ نِعْمَةً فَلْيُوَسِّعْ عَلَى أُسَرَائِهِ فَإِنْ لَمْ يَفْعَلْ أَوْشَكَ أَنْ تَزُولَ النِّعْمَةُ.

Ya zo cikin Kisaal na Ibn Mutawakkal daga Muhammad Addaariy, daga Ja'afar Al-Fazaariy, daga Ja'afar Bn Sahal, daga Sa'eed Bn Muhammad, daga Mas'adata, daga Musa Bn Ja'afar (A.S) yace:

" LALLE SU IYALIN MUTUM RIBATATTUNSA NE, DUK WANDA ALLAH YA NI'IMTA SHI DA WATA YI NI'IMA TO, YA YALWATAWA RIBATATTUNSA. IDAN KUWA BAI AIKATA BA, TO, NI'IMAR TAYI KUSA TA GUSHE."

أمالي الصدوق ص 577.

Kalmar ribatattu yana nufin wadanda aka kamo su wajen yaqi aka raba su da duk wani dangi nasu. Kunga akwai buqatar a kyautata musu domin basu da wani mai yi musu hakan in ba ku ba.

RASHIN CIYAR DA IYALI BA QARAMIN SHARRI BANE GA MUTUM

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da Ado Isah Guda.

       (08126385470)

10th December, 2021/ 6th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post